Forums » Rabon gabo

Shin kyautar da mutum bai amsa ba har ya mutu zai shiga gado?

  • 76 posts
  November 4, 2019 7:41 PM GMT

  Tambaya

  Assalamu alaikum

  Dan Allah ga wata tambaya ta gaggawa. Wata baiwar Allah ta sayi kaya da niyyar baiwa 'yar uwarta, amma kafin ta bata sai 'yar uwar ta rasu. Shin wannan sayayya ta shiga cikin kayan gado?

  Na gode.

  • 76 posts
  November 4, 2019 7:42 PM GMT

  Amsa

  To dan'uwa ba zai shiga rabon magada ba, saboda kyauta ba ta tabbata sai an amsa. Wannan ya sa lokacin da sayyadina Abubakar ya yiwa 'yarsa Aisha kyauta ba ta amsa ba, har mutuwa ta zo masa ya soke kyautar, ya mayar da ita dukiyar magada. Kamar yadda Malik ya rawaito a Muwada'i a hadisi mai lamba ta: 717.

  Wannan ita ce maganar mafi yawancin malamai.

  Don neman Karin bayani duba: Al'umm na Shafi'I 4\64, da Bada'iussana'i'i 6\8.

  Allah ne mafi sani.

  Amsawa

  Dr Jamilu Yusuf Zarewa

  13\4\2015