Forums » Aure

Mene ne hukuncin neman auren mace ta na cikin idda?

  • Moderator
  • 81 posts
  November 8, 2019 5:03 PM GMT

  Tambaya

  Assalamu Alaikum

  Malam tambaya ne na ke so a taimaka a amsa mun akan sha'anin aure. Malam mace ce tana zaune da mijinta sai ya kasance zamansun babu dadi, kullum a cikin matsaloli iri-iri har ya kai ga ta koma gidan iyayenta. Iyayenta sun matsa mata sai da ta tilasta mijinta ya saketa, saboda suna da wani manufa akan idan ya saketa tsohon saurayinta sai ya aureta.

  Bayan ta matsawa mijinta akan lalle ya saketa sai mijin nata ya amince akan zai kawo mata takardan sakin. Mallam a ranar da suka yi zai kawo mata takardan sakin, kawai sai ta samu tsohon saurayinta akan ta na so da zaran ta gama idda sai ya aureta.

  Mallam mene ne hukuncin wannan auren idan ta gama idda ya aureta?

  Na taba ji an ce duk wanda ya nemi mace tana idda babu aure a tsakanin su har abada. Mallam don Allah ka taimaka mana da karin bayani.

  • Moderator
  • 81 posts
  November 8, 2019 5:03 PM GMT

  Amsa

  Wa'alaikum assalam

  Idan mutum ya nemi mace tana idda ya aikata haramun, kamar yadda aya ta: (235) a suratul Bakara ta tabbatar da hakan, sai dai in an yi auran bayan ta gama idda, auran ya inganta, amma an aikata zunubin nema.

  Malikiyya suna haramta mace ga mutum har abada in ya aure ta cikin idda, ba in ya neme ta ba.

  Allah ne mafi sani.

  Amsawa

  Dr Jamilu Yusuf Zarewa

  12/8/1437

  19/5/2016