Forums » Sallah

Ina cikin sallah sai na tuna akwai najasa a hulata

  • Moderator
  • 81 posts
  November 8, 2019 5:16 PM GMT

  Tambaya

  Asalamu Alaikum Mallam

  Mutum ne yana tsakiyar sallah, ya kai raka'a ta biyu sai ya tuna kamar akwai najasa a hularsa, amma bai tabbatar ba sai ya cire hular, ya cigaba da Allah, toh ya ya sallar sa take?

  • Moderator
  • 81 posts
  November 8, 2019 5:17 PM GMT

  Amsa

  Wa'alaikumus salaam

  Wanda ya tuna da najasa a hularsa, zai iya hanzari ya cire ta ya yar, in har ya yi haka sallarsa ta yi, saboda abin da aka rawaito cewa: Annabi ? wani lokaci yana sallah, sai ya cire takalminsa, daga baya sai yake bawa sahabbansa labari cewa: Jibrilu ne ya ce ma?a akwai najasa a jiki. Hadisin sai ya nuna ingancin sallar wanda ya y? haka, tun da ba'a rawaito Annabi, Sallallahu alaihi wa sallama, ya sako sallarsa daga farko ba.

  Allah ne mafi sani.

  Amsawa

  Dr Jamilu Yusuf Zarewa

  28/3/2016