Forums » Sallah

Na bi sallah daga lasifika. Ya ya sallah ta?

  • Moderator
  • 81 posts
  November 9, 2019 3:43 PM GMT

  Tambaya

  Assalamu alaikum

  Malam, gidanmu yana kusa da masallaci, muna jiwo kiran sallah da ikama ta lasipika. Ko ya halatta in bi sallar jam'i daga laspika?

  • Moderator
  • 81 posts
  November 9, 2019 3:44 PM GMT

  Amsa

  Wa alaikum assalam

  To 'yar'uwa wannan mas'alar ta kasu kashi biyu:

  1. Idan ya zama dakinki yana like da masallacin, to tabbas wannan ya halatta, saboda nana A'isha ta bi sallar kisfewa rana daga dakinta, a zamanin Annabi s.a.w. kamar yadda Bukhari ya rawaito hakan a hadisi mai lamba ta : 184, sannan Abdurrazak ya rawaito cewa : takan bi ragowar salloli daga dakinta" kamar yadda ya zo a littafinsa na Musannaf a hadisi mai lamba ta : 4883, saboda dakinta a jikin masallacin yake.
  2. Idan ya zama dakin ba ya hade da masallacin, to zance mafi inganci shi ne : bai halatta ki bi ba, saboda a zamanin Annabi s.a.w. sahabbai suna haduwa ne a wuri daya idan za su yi sallar jam'i, ba sa rarrabuwa, wannan sai yake nuna cewa, hakan shi ne siffar sallar jama'i, sannan jera sawu a sallah, wani yana bin wani, dole ne.

  Don neman karin bayani duba : Fiqhunnawazil na Khalid Al-mushaikih shafi na : 50

  Allah ne masani.

  Amsawa

  Dr Jamilu Yusuf Zarewa

  13/11/2014