Forums » Rabon gabo

Shin dan zina zai iya gadon mahaifiyarsa?

  • Moderator
  • 81 posts
  November 19, 2019 11:22 PM GMT

  Tambaya

  Assalamu Alaikum

  Malam, don Allah ina da tambaya. Malam, mace ce ta yi ciki ba tare da aure ba, ta haihu kuma tana da kudi, sai Allah ya yi mata rasuwa. Shin malam, yaron zai iya cin gadonta?

  • Moderator
  • 81 posts
  November 19, 2019 11:22 PM GMT

  Amsa

  Wa'alaikum Assalam

  Idan mace ta yi cikin shege kuma ta haifi da, daga baya ta mutu dan zinar da ta haifa zai gaje ta, saboda Allah madaukakin sarki a cikin suratun Nisa'i aya ta: 10 ya yi wasiyya a bawa 'ya'yaye  gado. Dan zina kuma yana cikin jerin 'ya'yayen mahaifiyarsa, wannan yasa zai gaje ta.

  Dan zina ba ya gadon mahaifinsa a wajan mafi yawancin malamai, ko da kuwa ya yarda dansa ne.

  Allah ne mafi sani.

  Amsawa

  Dr Jamilu Yusuf Zarewa

  23/5/2016