Amsa
Wa'alaikum Assalam
Idan mace ta yi cikin shege kuma ta haifi da, daga baya ta mutu dan zinar da ta haifa zai gaje ta, saboda Allah madaukakin sarki a cikin suratun Nisa'i aya ta: 10 ya yi wasiyya a bawa 'ya'yaye gado. Dan zina kuma yana cikin jerin 'ya'yayen mahaifiyarsa, wannan yasa zai gaje ta.
Dan zina ba ya gadon mahaifinsa a wajan mafi yawancin malamai, ko da kuwa ya yarda dansa ne.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
23/5/2016