Forums » Sallah

Shin yin nafila bayan sallar asubahi ya inganta?

  • Moderator
  • 81 posts
  December 2, 2019 8:34 PM GMT

  Tambaya

  Assalamun alaikum

  Barka da wannan lokaci, barka da tashi. Malam dan Allah tambaya ce dani, malam dan Allah, ana yin nafilla bayan sallah asubahi, ya in ganta daga manzon Allah.

  Nagode

  • Moderator
  • 81 posts
  December 2, 2019 8:35 PM GMT

  Amsa

  Wa'alaikum assalam

  To dan 'uwa Annabi ? ya haramta yin sallah bayan sallar asuba har sai rana ta fito, amma wanda raka'atanil Fajr ta wuce shi kafin asuba, zai iya ramawa, bayan sallar asuba, saboda Annabi ? ya ga wani yana ramawa bai yi masa inkari ba, hakan sai ya nuna halaccinsa.

  Kamar yadda ya inganta a wajan Abu-dawud a hadisi mai lamba ta: 1267

  Allah ne mafi sani.                                                                                                       

  Amsawa

  Dr Jamilu Yusuf Zarewa

  28\12\2015

 • September 8, 2020 4:43 PM BST

  Aslm malam inatambaya mutum zai iya bin Mai Sallah nafila Sallah Farillah?