Amsa
Wa'alaikum assalam
To dan 'uwa Annabi ? ya haramta yin sallah bayan sallar asuba har sai rana ta fito, amma wanda raka'atanil Fajr ta wuce shi kafin asuba, zai iya ramawa, bayan sallar asuba, saboda Annabi ? ya ga wani yana ramawa bai yi masa inkari ba, hakan sai ya nuna halaccinsa.
Kamar yadda ya inganta a wajan Abu-dawud a hadisi mai lamba ta: 1267
Allah ne mafi sani.
Amsawa
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
28\12\2015