Amsa
To dan'uwa, hukuncin wannan albashi zai fara ne daga lokacin da ya shiga mulkinsa, don haka mutukar ba su shekara ba, to babu zakka a ciki, domin ba kawai samun nisabI ne ya ke wajabta zakka ba, dole sai an samu zagayowar shekara daga lokacin da kudin su ka shiga mulkinsa, don haka duk albashin da ya kai zakka, kuma aka ajjiye shi ya shekara to ya wajaba a fitar masa da zakka, amma mutukar shekara ba ta zagayo masa ba, to zakka ba ta wajaba ba akan wanda ya mallake shi.
Sai dai yana daga cikin dabarun da sharia ta haramta, mutum ya yi abin da zai sarayar masa da wajibi da gangan, don haka mutukar ya sayi filayan ne da nufin kaucewa fitar da zakka, to tabbas ya sabawa Allah.
Allah ne mafi sani
Amsawa
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
14/5/2014