Forums » Sallah

? Ya manta da kabbarar harama, yaya sallarsa?

  • Moderator
  • 81 posts
  December 2, 2019 9:06 PM GMT

  Tambaya

  Assalamu alaikum

  Malam ya kokari ya aiki. Dan Allah malam wata tambaya ce nake da ita. Me ye matsayin wanda har ya kusa gama sallah sai ya tuna ya manta bai yi kabbarar harama ba, koma dai farkon sallah ne ya zai yi? Allah bada ikon amsawa, ya saka da mafificin Alkhairin sa. Amin

  • Moderator
  • 81 posts
  December 2, 2019 9:06 PM GMT

  Amsa

  To dan'uwa malamai suna cewa: wanda ya bar kabbarar harama da mantuwa ko da gangan, sallarsa ta baci.

  Don haka ya wajaba ya sake sallarsa daga farko, saboda sallah ba ta kulluwa ba tare da kabbarar harama ba.

  Don neman Karin bayani duba: Al-mugni na Ibnu Khudaamah 1\640.

  Allah ne mafi sani.

  Amsawa

  Dr Jamilu Yusuf Zarewa

  22\11\2015