Forums » Aure

Zan iya auran 'yar kanwar matata?

  • Moderator
  • 81 posts
  December 2, 2019 9:18 PM GMT

  Tambaya

  Assalamu alaikum Malam, Ya halatta mutum ya auri yar qanwar matarsa?

  • Moderator
  • 81 posts
  December 2, 2019 9:19 PM GMT

  Amsa

  Wa'alaikum assalam

  Ya halatta ya aure ta, bayan ya saki matarsa, amma bai halatta ya hada su ba saboda innarta ce, Annabi ? yana cewa: "Ba'a a hada mace da goggonta, ba'a hada mace da innarta a auratayya, saboda in kuka yi haka, za ku lallata zumunci ku" kamar ayadda ibnu Hibban ya rawaito.

  Allah ne mafi sani.

  Amsawa

  Dr Jamilu Yusuf Zarewa

  20\5\2016