Forums » Aure

Hukuncin wanda ya fifita matarsa akan mahaifiyarsa

  • Moderator
  • 81 posts
  December 2, 2019 9:33 PM GMT

  Tambaya

  Assalamu alaikum

  Dr. tambayata ita ce mene ne ingancin hadithin da yake nuni da la'antar duk wanda ya fifita matarshi akan mahaifiyarshi?

  • Moderator
  • 81 posts
  December 2, 2019 9:33 PM GMT

  Amsa

  Wa'alaikumus salam

  Ban taba karanta hadisin ba, kuma na neme shi ban samu ba.

  Saidai nassoshi ingantattu sun tabbatar da cewa: mace ta fi girman hakkin Ciyarwa da kuma sutura fiye da mahaifiya,  saboda ita mahaifiya ciyar da ita yana wajaba ne idan ba ta da hali, ko mijinta ya mutu ko ba shi da Hali, mace kuwa ya wajaba a ciyar da ita ko tana da kudi.

  Ya wajaba mutum ya fifita mahaifiyarsa akan matarsa ta wajan biyayya da girmamawa, amma ban da bangaren ciyarwa, saboda mace ta fi girman hakki a nan .

  Bai wajaba duk abin da ka siyowa matarka ba, ka siyowa mahaifiyarka, saboda bambancin da muka fada a sama.

  Allah ne mafi sani.

  Amsawa

  Dr Jamilu Yusuf Zarewa

  30/11/2019