Forums » Sauran hukunce-hukunce

Yaya kaffarar direban da ya zama sababin mutuwar mutane da yawa?

  • 76 posts
  December 13, 2019 2:10 PM GMT

  Tambaya

  Assalamu Alaikum Sheikh

  Mutum ne suka yi accident a cikin mota sai aka kai su asibiti bayan wasu kwanaki wasu daga wadanda suka yi accident din suka mutu. Shin Malam mene matsayin direban motan, zai yi azumi ne? Kuma idan zai yi guda nawa zai yi saboda ba mutun dayane ya mutuba?

  Ina fata Sheikh zai amsa don ma amfanin ragowar musulmai masu damuwa irin wannan.

  Nagode Allah ya kara ilimi da imani.

  • 76 posts
  December 13, 2019 2:11 PM GMT

  Amsa

  Wa'alaykumussalam

  To dan'uwa kisan kuskure yana wajabta abubuwa guda biyu:

  1. Diyya wace dangin wanda ya yi kisan za su bayar ga dangin wanda aka kashe da kuskure, sai dai in sun yafe.

  2. Kaffara, wacce zai 'yanta kuyanga, in bai samu ba sai ya yi azumi 60, kamar yadda aya ta 92 a Suratunnisa'i take nuni zuwa ga hakan.

  Idan sama da mutum daya suka mutu a mota, ya wajaba ga direban motar ya yiwa kowa kaffara kuma danginsa su biya diyya, mutukar shi ne sababi a hadarin, kamar ya zamana ya wuce danja ko kuma ya yi gudun da ya zarta ka'ida, ko burkinsa ya lalace amma ya ki gyarawa, ko wani abu makamancin haka wanda yake nuna sakacin direban, ko wuce ka'idarsa.

  Idan hadari ya faru wasu suka ji ciwo saboda sakacin direba ko wuce ka'idarsa, sai suka mutu daga baya, danginsa za su biya diyyarsu kuma zai yiwa kowa kaffara, ko da kuwa bayan shekaru biyar ne da faruwar hadarin, saboda duk dalilin da yake kaiwa zuwa abu, to yana daidai da abun.

  Don neman Karin bayani a duba: Al'inaya 1\116, Madalibu Uli-Annuhaa 6\147 da kuma Fataawa Allajnah Adda'imah 23\352.

  Allah ne mafi sani

  Amsawa

  Dr Jamilu Yusuf Zarewa

  29/12/2015


  This post was edited by Bakandamiya at December 13, 2019 2:12 PM GMT
  • 1 posts
  January 21, 2020 2:05 PM GMT
  ????