Forums » Sallah

Duk sallar da ta fi mutane da yawa ta fi lada!

  • Moderator
  • 81 posts
  December 26, 2019 6:09 PM GMT

  Tambaya

  Assalamu alaikum

  Allah ya kara ma Dr. Ikhlasi. Dan Allah Dr. akwai bambancin lada ne a sallar jam'i mai mutane da yawa da kuma yan kadan?

  Domin muna da masallatai biyu a anguwar mu, to da yawa an fi raja'a a daya, idan na yi ma mutane magana sai suce ai an fi cika a wancan ne shiyasa basa zuwa wannan.

  • Moderator
  • 81 posts
  December 26, 2019 6:09 PM GMT

  Amsa

  Wa alaikum assalam

  Wannan magana haka take, Annabi (SAW)  yana cewa: "Sallar mutane biyu tafi sallar mutum daya, sallar mutum uku tafi sallar mutum biyu lada, duk sallar da tafi mutane da yawa tafi yawan lada" kamar yadda Bukhari da Muslim suka rawaito.

  Hadisin da ya gabata yana nuna babu laifi idan mutum ya tsallake Masallacin da yake da karancin jama'a ya tafi wanda ya fi yawan mutane saboda neman karin lada.

  Allah ne mafi sani.

  Amsawa

  Dr Jamilu Yusuf Zarewa

  21/12/2019