Forums » Sauran hukunce-hukunce

Zan iya huda hanci saboda kwalliya ga mijina?

  • Moderator
  • 81 posts
  January 31, 2020 6:18 AM GMT

  Tambaya

  Assalamu Alaikum

  Malam don Allah wata ce mijinta ya ce hujin hanci na burge shi. So, tana so ta huda sai aka ce mata babu kyau a Musulunci. Shin Malam ya abun yake? Haramun ne, ko kuwa tana iya hudawa ta sa dankunne ta yi kwalliya da shi?

  • Moderator
  • 81 posts
  January 31, 2020 6:19 AM GMT

  Amsa

  Wa'alaikumus Salaam

  An tambayi Sheikh Ibnu Uthaimin akan wannan matsalar ta huda hanci sai yake cewa: Huda hanci zai iya zama canza halittar Allah, amma idan garin da matar da ta huda hancin take ana y?n ado a hanci, ta yadda hakan ya zama al'ada, to babu laifi a yi hakan.

  Duba: Majmu'u Fatawaa Ibnu Uthaimin 11/137.

  Haka nan an tambayi Sheikh Abdul Muhsin Al'abbad akan haka a darasinsa da yake gabatarwa a Haram, sai ya ce babu laifi akan haka.

  Bisa abin da ya gabata ya halatta matar BAHAUSHE ta huda hancinta saboda ta sanya abin kwalliya tun da al'adarsu ce, saboda ya tabbata sahaban Annabi S.A.W. mata suna huda kunnansu suna sanya 'yan kunnaye kamar yadda hadisin Bukhari mai lamba 98 yake nuni zuwa hakan.

  Allah ne mafi sani.

  Amsawa

  Dr Jamilu Yusuf Zarewa

  4/1/2016