Amsa:
Wa alaikum assalam
Za ta yi gini ne akan tabbas wajan ramako, misali idan k?na zaton ashirin suka rage miki ko kuma ashirin da biyar, to sai ki rama ashirin da biyar (25), saboda in kin yi haka za ki fita daga kokwanto, kuma zai zama tabbas kin rama abin da ake binki.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
18/04/2016