Forums » Aure

Wace mata ce a ke kira kwarkwara

  • 1 posts
  May 2, 2020 11:24 PM BST
  • 4 posts
  August 4, 2020 1:37 PM BST

  A iya karamin sani na, kwarkwara mata ce da ba matan aure ba ga basarake amma ta na karkashin ikonsa a gidansa kuma yana mu'amalar auratayya da ita harma su haifi 'ya'ya. Anfi samun kwarkwara a zamanin da to amma har a yanzu ance akwai su a gidajen sarakunanmu na gargajiya. Hukunci su kuma a musulunci sai mu jira malamai su yi mana bayanin yadda abin ya ke.


  This post was edited by Rahmatu Lawan at August 4, 2020 1:56 PM BST
  • 4 posts
  August 4, 2020 1:51 PM BST

  Daga Premium Times Hausa:

  Mas’alar bauta, bayi da kwarkwara mas’ala ce da makiya musulunci suke aibata musulmi da ita. Lalle harkar bayi tsohuwar harkace da musulunci ya gada kuma bauta ta wanzu a cikin al’ummomin duniya rankatakaf, ashe kenan ba gajiyawar musulunci ba ne.

  Da musulunci ya zo, sai ya shinfida kyawawan tsari a cikin harkan bayi da bauta, kuma ya takaita hanyoyin samun bayi zuwa kwaya daya tak, wato hanyar JIHADI, sannan kuma ya yawaita hanyoyin ‘yanci. Musulunci ya kwadaitar da ‘yanta bayi kuma ya sashi a matsayin daya daga cikin manyan ibadu, ‘yanta bawa kaffarar kisa ne, kaffarar karya azumin Ramadana ne, kaffarar Zihari ne, kaffarar rantsuwa ne, kuma musulunci ya samo ma bayi ‘yancin mutuntaka.

  Kuma musulunci ya hukunta cewa duk wata kwarkwarar da ta haihu da ubangidanta, toh ‘yantacciyace, kuma ‘ya’yanta ma ‘yantattu ne.

  Babu wani lokaci da musulunci ya haramta bauta, bayi, kwarkwara ko sa daka. Halal ne a musulunce da nassoshin Al-Kur’ani da Sunnan ma’aiki SAW. Wata kila sabo da rubdugun da makiya musulunci ke yi wa musulmai da musulunci, mai tambaya ke zaton musulunci ya haramta wannan mas’ala ta bauta, bayi da kwarkwara, ko kuma yake tunanin ai ya kamata musulunci ya haramta.

  Hakika musulunci ya dakushe harkar bauta da bayi harma da kwarkwara, amma babu inda musulunci ya hana,

  Latsa nan ka karanta sauran


  This post was edited by Rahmatu Lawan at August 4, 2020 1:57 PM BST