Tambaya
Assalamu alaikum Malam
Tambaya ce dani. Mijina ne ya sake ni sau biyu, sai ya sha abin maye yace na zo na same shi, ni kuma ban zo ba saboda bana son abin da yake sha na maye, shine yace idan ban zo ba a bakin aure na. Shin yaya auren mu?
Allah ya saka da alheri.
Amsa
Wa alaikum assalam,
Malamai sun yi sabani game da aukuwar sakin wanda yake cikin maye:
Sannan an rawaito daga sayyadina Usman da Ibnu Abbas cewa: sakin mashayin giya ba ya aukuwa, kuma ba a san wanda ya saba musu ba a cikin Sahabbai.
Wannan ita ce maganar Imamu Ahmad da Zahiriyya da Ibnu Taimiyya.
Babban Muftin Saudiyya na waccan lokacin Sheik Abdulaziz bn Bazz da wasu Malaman suna rinjayar da magana ta biyu saboda mashayin giya bai san abin da yake fada ba. Hakan sai ya sa ya yi kama da mahaukaci wanda Alkalami ya saraya daga kan shi. Kai har sallah ma an hana mashayin giya ya yi saboda ba ya cikin hayyacinsa, kamar yadda aya ta (43) a Suratu Annisa'í ta tabbatar da hakan
Don neman karin bayani a duba: Al-Mugni 7/289 dá kuma Sharhul Munti'i 10/233.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
9/08/2017