Forums » Aure

Wanda ya saki matarsa a cikin maye, ba ta saku ba

  • Moderator
  • 81 posts
  August 25, 2020 5:50 PM BST

  Tambaya

  Assalamu alaikum Malam

  Tambaya ce dani. Mijina ne ya sake ni sau biyu, sai ya sha abin maye yace na zo na same shi, ni kuma ban zo ba saboda bana son abin da yake sha na maye, shine yace idan ban zo ba a bakin aure na. Shin yaya auren mu?

  Allah ya saka da alheri.


  This post was edited by Bakandamiya at August 25, 2020 6:24 PM BST
  • Moderator
  • 81 posts
  August 25, 2020 5:51 PM BST

  Amsa

  Wa alaikum assalam,

  Malamai sun yi sabani game da aukuwar sakin wanda yake cikin maye:

  1. Mafi yawan malamai sun tafi akan cewa idan ya saki matarsa, tabbas sakin ya auku, saboda shan giya sabon Allah ne, kuma shi ya jawowa kansa, don haka ba za a yi masa uzuri ba, wannan ita ce maganar Abu-hanifa da Malik da Shafii a daya daga cikin zantukansa.
  2. Sakinsa bai auku ba saboda lokacin da Ma’iz ya zo ya tabbatarwa Annabi S.A.W. ya yi zina sai da ya tambaye shi ko ka sha giya ne,  kamar yadda Baihaki ya rawaito a Sunanul-kubrah,  hakan saí ya nuna mashayin giya ba a amsar maganarsa.

  Sannan an rawaito daga sayyadina Usman da Ibnu Abbas cewa: sakin mashayin giya ba ya aukuwa, kuma ba a san wanda ya saba musu ba a cikin Sahabbai.

  Wannan ita ce maganar Imamu Ahmad da Zahiriyya da Ibnu Taimiyya.

  Babban Muftin Saudiyya na waccan lokacin Sheik Abdulaziz bn Bazz da wasu Malaman suna rinjayar da magana ta biyu  saboda mashayin giya bai san abin da yake fada ba. Hakan sai ya sa ya yi kama da mahaukaci wanda Alkalami ya saraya daga kan shi. Kai har sallah ma an hana mashayin giya ya yi saboda ba ya cikin hayyacinsa, kamar yadda aya ta (43) a Suratu Annisa'í  ta tabbatar  da hakan

  Don neman karin bayani a duba: Al-Mugni 7/289 dá kuma Sharhul Munti'i 10/233.

  Allah ne mafi sani.

  Amsawa

  Dr Jamilu Yusuf Zarewa

  9/08/2017


  This post was edited by Bakandamiya at August 25, 2020 6:24 PM BST