Forums » Aure

Mene ne hukuncin wacce ta haihu kafin ta cika wata 7 da aure?

  • Moderator
  • 81 posts
  September 22, 2020 9:42 PM BST

  Assalamu Alaikum. Malam yarinya ne aka aurar da ita ba ta yi wata bakwai ba ta haihu cikakkiyar yarinya yar wata tara (9). To malam me ye hukuncin auren kuma ya hallaccin jaririyar a Musulunci?

 • September 22, 2020 9:53 PM BST

  Wa’alaikum salam,

  In har an San tana da ciki aka yi auran wannan hukuncinsa a fili yake, kuma auran bai inganta ba a zance mafi inganci. Amma in haihuwa ta yi kafin ta cika wata bakwai, kuma ba a santa da ciki ba to dansa ne, saboda ayar suratu Lukman da ta suratul Ahkafi sun nuna cewa ana iya haife ciki a watanni shida.

  Auran da aka yi da cikin shege ba tare da an sani ba ya inganta, saidai ba za a danganta cikin zuwa mijin ba, tunda ba shi ya yi ba. In har ya san tana da ciki bayan sun yi aure, bai halatta ya take ta ba har sai ta haihu saboda fadin Annabi s.a.w. “Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar Lahira to kar ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa,” kamar yadda Abu-dawud ya rawaito.

  In ta haihu za su iya cigaba da mu’amalarsu ta aure, musamman in bai sani ba sai da aka daura.

  Allah ne mafi sani.

  Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

  07/08/2017