Forums » Rayuwar Aure

Shin me ke kawo yawan mutuwar aure a kasar Hausa a yau?

  • Moderator
  • 81 posts
  November 19, 2018 7:32 PM GMT
  Kun san yanzu za a iya cewa babu abinda yakai aure saurin lalacewa a kasar Hausa. A fahimtarku, wai shin wasu dalilai ne ke kawo yawan rugujewar auren?

  Ku fadi ra'ayinku da kawo hujjoji kwarara.
  • Moderator
  • 4 posts
  November 21, 2018 7:38 PM GMT
  Ina ganin babban abinda ke kawo mutuwan aure musamman a kasar Hausa shine jahilci. Wannan jahilcin kuwa daga wajen mazan har matan. Za ka ga a tsakani ana ta tabka shirme babu sanin hakkin juna sam saboda wannan jahilcin. Kowa kawai abinda ya masa dai dai yake aikatawa.

  To a irin haka in ba a yi dace ba sai kaga aure ya mutu. Inko auren bai mutu ba, akasari ana cutar da daya ne yana/tana hakuri.
  This post was edited by Rahmatu Lawan at November 21, 2018 7:38 PM GMT
  • 1 posts
  September 27, 2019 9:42 PM BST
  Abubuwan da ke kawo mutuwar aure a Kasar Hausa sun hada da:
  Rashin sanin miye aure shi kansa.
  Auren Sha'awa.
  Karya a wurin neman aure.
  Boye gaskiyar waye kai yayin neman aure.
  Bayyana sirrin juna ga iyaye, abokai.
  Rashin hakuri (gajen hakuri).
  Rashin ilmi.