*πΈπ¦ZAMAN AMANA WRITERS*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)π€π€
*DOMIN SAMUN DUKKANIN LITATTAFANMU A FACEBOOK DA BAKANDAMIYA TSOFAFFI HARMA DA SABABBIN DON YI MANA LIKE DA COMMENT, GROUP 'DINMU NA FACEBOOK BIYU NE, DUK WANDA KA SHIGA ZAKA SAMU LITATTAFANMU A CIKI.*
ππππ
https://www.facebook.com/gidanzamanlpydaamana/
Alhaji da D.P.O wad'anda suke bakin k'ofa a tsaye ne suka k'araso ciki, cikin sauri Intisar ta matso kusa da Shamsu ta b'oye a bayanshi tana yi tana d'an lek'o da kanta kamar wata tsohuwar munafuka.
Shamsu cikin tsananin b'acin rai ya kalli Goga ya ce, "Yanzu Mubarak duk yardar da mukai da kai abinda zaka saka mana da shi kenan ko."
Goga ya kalli Shamsu ya ce, "Wallahi ba ni na fad'a musu inda kuke ba, taya kake tunanin......................" Want irin tsawa Alhaji ya daka musu ya ce, "Ku yi min shiru munafukan banza kawai, ya juyo da kallonshi kan Shamsu ya cigaba da magana ya ce, me kake tunani da? a tunaninka ba za'a iya kamaka ba ko me? to bari ka ji, ko k'asar nan ka bari wallahi ina iya zak'uloka in wulak'anta rayuwarka. dubi gidan da ka kawo min 'ya ka ajiye, dan tsabar iskanci kana mai gadi ka tsaya a matsayinka mana, a'a kai dole sai ka kai kanka inda Allah bai kaika ba. Daga yau zaka kiyaye k'ok'arin sake aikata makamancin haka a gaba, zan tafi da 'yata gida yau, kai kuma zaka je ka cigaba da kwanan cell, daga cikin cell kuma sai a zarce k'auye a je a cigaba da gararambar da aka saba a cikinta ba aikin yi."
Hannu Shamsu ya dunk'ule a fusace, sai Intisar ta rik'eshi tare da girgiza mishi kai alamar kada yai komai.
Shamsu ya ce, "Ko a garin da kake zaune sai naso ka kamani zaka kamani, a yanzu ma da nake gabanka sai naso ka kamani zaka kamani, kuma 'yarka shaida ce kud'inku sam baya gabana dan ban tab'a cin k'wandalarta ba, kuma ka sani muddin akwai so da k'aunata a cikin zuciyar Intisar to wallahi ba zaka tab'a iya rabamu ba, kuma mu zuba aga wanda zai yi nasara, tasirin so a zuciya ya wuce yanda ku iyaye kuke kallonshi, da kunsan ya akeji da kun rik'a tausayawa kuna bawa yaranku zab'insu, amma tunda ka dage, nima na dage, in har baka bani Intisar ba to wallahi ba zan tab'a barin cikin rayuwarta ba, alk'awarinmu ne wannan ko kashemu za'ai ba zamu tab'a rabuwa ba, dan haka ka rubuta ka ajiye a ranka wallahi ba zan rabu da 'yarka ba."
Mahaifin Intisar ya tako har zuwa gaban Shamsu ya wankeshi da mari, cikin sauri Intisar ta dafe kumatunta tana sosawa yanda kasan ita aka mara, da sauri ta tsaya a gaban Shamsu ta kareshi dan kar Alhaji ya k'ara marinshi. Cikin kuka ta ce, "Daddy shi ka mara amma ni naji zafin a raina, dan Allah ka yi hak'uri ka k'yalemu, shi nake so, ba zan iya rayuwa babu shi ba, Dad wai duk ina tarin k'aunar da kake yi min ne."
Alhaji ya kalli Intisar ya ce, "Nima tambayar da nake yiwa kaina kenan ina neman amsarta, ina soyayyar da na nunawa 'yata ta tafi? ina wadda itama take nunamin? da har na kasa samun alfarmarta a matsayina na mahaifi. Wallahi dole ku rabu, domin kuwa aikin gama ya riga da ya gama, an riga an d'aura miki aure da Nidal, banda ma Allah ya taimakeni mijin naki yai tafiya da yanzu ya san halin da ake ciki."
Cikin kad'uwa Intisar da Shamsu suka d'ago kai suna kallonshi, Intisar ta hau yiwa mahaifinta magiya akan ya barta tai rayuwa da wanda take so, a maimakon ma ya saurareta sai ya kama hannunta ya rik'e gam, sannan ya kalli D.P.O ya ce, "Yallab'ai ga Shamsu nan ku kuka san yanda zaku yi da shi." Yana gama fad'in haka ya fara jan Intisar yana k'ok'arin fita da ita daga gidan, kuka take tana kiran sunan Shamsu a bakinta.
Suna zuwa daf da bakin k'ofa ta fizge hannunta ta ruga da gudu wajen Shamsu, Alhaji ya sake tahowa ya jawo hannunta zai sake janta ta k'ara fizgewa, sannan ta kalleshi ta ce, "Ni wallahi Dad ba inda zan bika, ni Shamsu kad'ai nake muradi."
Alhaji ya ja ya tsaya yana kallonta ya ce, "Kika ce ba zaki bini ba?" Intisar ta ce, "Eh, ni ba zan bika ba, bana son wanda kuka auramin Shamsu nake so, kuma ni da shi kad'ai nake son in cigaba da zama a rayuwa, duk cikin daular da zaka kaini in ba da shi ba to ba zan tab'a jin dad'in rayuwata ba, idan ka rabani da shi mutuwa zan yi."
Alhaji ya tsaya shiru yana kallonta cikin tsananin mamaki, ya ce, "To yanzu sai ki zab'a a cikinmu ko ni ko shi."
Cikin sauri Shamsu ya kalleta ya ce, "Kar kice komai Intisar, ki bi mahaifinki kinji."
Intisar ta kalli Shamsu ta ce, "Ka k'yaleni, na lura Dad baya k'aunar farin cikina ne, juyowa ta yi ta kalli mahaifinta ta cigaba da magana ta ce na zab'i zama da Shamsu fiye da kai Dad, kai fa uba ne, ya kamata ka tuna hakan, ka rik'e girma da matsayinka na uba ka barmu mu yi rayuwarmu."
Ba Alhaji kad'ai ba hatta jami'an wajen manyansu da k'ananan sai da suka girgiza da maganar Intisar.
Hawaye ne suka fara wankewa Alhaji fuska, cikin rawar murya ya fara magana ya ce, "Nagode Intisar, ban tab'a tunanin akwai ranar da zata iya zuwa ki so wani fiye da iyayen da suka zama silar zuwanki duniya ba, har sanadinshi kina yi min gargad'i akan in daina damunku in barku ku yi rayuwa." Kuka ya fashe da shi, a cikin kukan ne ya cigaba da cewa wata k'ila ma kallon mahaukaci kike min Intisar saboda na damu da ke. In haifeki in k'aunaceki fiye da kowa, in baki kyakkyawar rayuwa, ko kallon banza bana bari ai miki saboda bana k'aunar b'acin ranki, tun kina k'aramarki nine nake yi miki komai da kaina har kika girma, makarantu kuwa na sauya miki su ya fi a irga, dan ban yarda a dokarmin ke ba. bayan kin taso kin gama sec. school d'inki na turaki waje domin yabawa da k'wak'walwarki ba dan wai ki je ki lalace ki zo ki fi k'arfina ba. kin sha yi min laifi amma bana iya yi miki fad'a saboda bana so naga ranki ya b'aci, zaki yi laifi kuma kiyi fushi in rarrasheki amma a yau wanda ya nuna miki so da tattali shi kike yiwa gargad'i da jan kunne akan ya k'yaleki kiyi rayuwarki. A yanda kike a yanda na sanki ban tab'a tunanin zaki iya kula koda k'aramin ma'aikaci ne ba balle mai gadi, shiyasa ban tab'a kawowa soyayya kuke ba. bayan kun gudu na haukace da nemanki, kullum tunanina ya kike, a wane hali kike ciki, ina ya kaiki, wane irin abinci yake baki kike ci, ki kalleni duk nabi na rame, kwanaki sai da aka aunani aka ce jinina ya hau, ba dan komai ba sai dan tunaninki, ko abinci bana iya ci saboda ban san a wane hali ke kike ciki ba, amma a yau soyayyata ita ta zama abun takura saboda masoyinki ko? Ban tab'a tunanin akwai wanda zai zo a duniya ki soshi sama da iyayenki ba, ban tab'a tunanin duk k'aunar da na nuna miki zaki iya yin biris da ita ki zab'i wani a madadin zab'ina ba, a tunanina na cancanci kiymin ko wace irin sadaukarwa, kuma a tunanina na cancanci kowace irin alfarma a wajenki ko dan k'aunar da na nuna a gareki, a da tunanina yana bani shine ya hure miki kunne kuka gudu. Amma yanzu na gode miki da kika fahimtar da ni cewa da yardarki da amincewarki kika zab'i ku gudu domin cika muradinku, ya sake fashewa da kuka, sannan ya d'aga hannu sama ya ce Allah mun gode maka da ka kawomu wannan zamanin da ake maida iyaye su koma ba komai ba, ya sake kallon Intisar ya ce ban tab'a tunanin fuskantar haka daga wajen 'yar da na fifita sama da kowa ba, amma nagode, kuma ku yi hak'uri da shiga rayuwarku da nayi, ku je ku yi rayuwarku yanda kuke so, kuma daga yanzu nai muku alk'awarin ba zan sake shiga harkarku ba, rayuwarku ce, ku yi yanda kuka so da ita, kuma ba zan tab'a miki baki ba dan har yanzu ina k'aunarki 'yata, ina rok'on Allah ya shiryar da ke, Shamsu na gode, Allah ya ganar da ku da sauran masu irin tunani naku gaskiya."
Cikin kuka yake magana har ya k'arashe wannan bayanin nashi, jiki a sanyaye ya fara tafiya, sai da ya kai bakin k'ofa sannan ya tsaya, ba tare da ya juyo ba ya ce, "D.P.O ku k'yalesu ku taho mu tafi kawai."
Gaba d'ayansu suka fice suka bar gidan, Alhaji ya dad'e jingine a jikin motarshi yana kuka D.P.O yana rarrashinsa, sannan suka shiga mota suka ja suka tafi.
Sai dare suka isa gida wajen k'arfe takwas saura, kai tsaye Alhaji gida ya nufa, inda su kuma suka wuce station.
Alhaji yana tuk'i yana kuka, bai san me yasa maganganun Intisar suka fi yi mishi zafi a rai ba, domin su kawai yake tunowa suna sakashi kuka.
Haka ya k'araso gida dafe da k'irji, da k'yar ya samu yai hon, da sauri Bala ya bud'e mishi gate, sai dai ganin shiru bai zo ya wuce bane yasa ya taho wajen motar, yana zuwa ya tarar da shi yana dafe da dai-dai saitin zuciyarsa, cikin mawuyacin hali ya kalli Bala wanda yake ta salati ya ce, "Shiga da ni gida Bala."
Bala ya kamashi suka shiga ciki, Habu da ke zaune kan benci yana ganinsu shima ya taso, suka shiga da shi cikin gida.
Suna fita Shamsu ya fara kai kawo maganganun Alhaji suna yawo a k'wak'walwarshi Intisar sai aikin bashi hak'uri take, a yayin da shi kuma Goga yai matuk'ar jin tausayin mahaifin Intisar, sannan ya fara jin takaicin su Intisar d'in, tunowa da nashi iyayen yayi, sai ya fara kuka, takaici yake ji, wasu iyayen nasu suna raye amma suke wofintar da su, shi yana jin d'acin rasa nashi, yana ji a ranshi ina ma nashi ne suke raye yanzu, yanda ya samu aikin nan da sun ga gata. Can sai Shamsu ya samu waje ya zauna, inda suma su Intisar suka zazzauna. Goga ya share hawayen fuskarshi, sannan ya kallesu ya ce, "Wallahi sam ban san ya akai suka taho nan ba, kuma ban tab'a fad'a musu inda kuke ba, duk da irin wahalar da na sha a hannunsu kuwa."
Intisar ta ce, "Kar ka damu Mubarak, mun san ba zaka tab'a yi mana haka ba. kallon Shamsu tayi wanda fuskarshi ke d'auke da tsananin b'acin rai da damuwa, itama cikin damuwar ta ce, "Jarumina ka yi hak'uri da abinda ya faru dan Allah, kada ka sa komai a ranka, insha Allah komai zai yi dai-dai."
Shamsu ya kalleta yana mata yak'en da ya fi kuka ciwo, ya ce, "Kar ki damu, amma ki sani cewa na tsani wulak'anci da cin zarafi, dan haka dole a d'aga bikin nan, zan fita na nemo kud'i, yanzu da kaina nake so nai komai na bikinmu. Kuma zamu tashi mu sauya gida, koda ace bamu samu gida ba zamu kama d'aki a gidan haya amma banda wannan, nasan halin mahaifinki sarai ba zai tab'a k'yalemu ba."
Intisar ta ce, "Amma mun riga mun gama siyan komai fa, dan Allah ka yi hak'uri a cigaba da hidimar nan a lokacin da aka saka, in yaso ka cigaba da nemo na ciyar da mu."
Sai a lokacin Goga ya saka baki, ya tayata rok'onshi, Shamsu yana matukar jin nauyin Goga, ba dan komai ba sai dan irin halaccin da yai musu a rayuwa baya jin zai iya musa wata alfarma daga gareshi, hakan ne yasa ya sassauta fushinsa, tare da amincewa da cigaba da hidimar bikin da kuma karb'ar duk abinda aka siya da kud'in Intisar, amma ya dage akan lallai ba za'a d'aura aure gobe ba har sai ya samu abin yi.
Wannan dalilin ne yasa gari na wayewa Goga yai sallama da su ya tafi gida, yana tafe a hanya yana kukan rashin iyayensa.
Intisar kuwa tun jiya har zuwa yau aikin kuka take da kuma fushi da Shamsu a kan ya k'i yarda a d'aura aurensu yau har sai ya samu kud'i.
Kallon inda take yayi yaga ta had'a kai da gwiwa, tashi yayi daga inda yake zaune ya k'arasa har gabanta ya tsugunna, sannan ya ce, "Intisar, d'ago kanki ki kalleni akwai maganar da nake so mu yi."
A hankali ta d'ago kai tana kallonshi da kumburarrun idanunta, domin duk tsananin fushin da take yi da shi bata iya yi mishi musu Shamsu ya ce, "Ki fahimceni dan Allah, kin san ina k'aunarki, amma bana son abinda zai jawo a rik'a yi min gori kullum, ki kwantar da hankalinki ba gamu a tare ba, ai ba abinda zai rabamu da ke sai mutuwa, nidai nafi so komai na cigaba da yi da kaina ne, ki bani nan da wata d'aya tak, in har ban samu abin yi ba to nai miki alk'warin za'a cigaba da yin hidima da kud'in hannunki har zuwa na samu aiki kinji."
Intisar ta gyad'a kai alamar eh, sai ya ce, "Yauwa ko ke fa, to d'an yi min murmushi mana," Murmushin tai mishi daga nan kuma ya lallab'ata ta ci abinci sannan suka cigaba da harkokinsu kamar kullum.
Shamsu ya tafi wajen mai wannan gidan da suke ciki ya rok'eshi akan ya cire iya kud'in kwanakin da suka yi ya bashi ragowar zasu tashi, ba musu ya basu, saboda ko ba komai an gyara mishi gidanshi yai rass da shi kamar sabon gini, yasan ba zai sha wahalar samun wasu ba.
Can cikin Paiko suka koma, duk da yanayin unguwar kamar sabuwar unguwa ce, kuma tayi nisa sosai da cikin gari, a k'alla kafin ka fito cikin gari sai ka kashe d'ari biyar. A haka suka cigaba da rayuwa a wannan unguwar, sai dai saboda yanayin wajen yasa komai ya sauya musu, hatta kayan abinci sai an tafi cikin gari ake samowa, hakan ne yasa rayuwa ta fara musu tsada, kullum sai Shamsu ya fita nema amma har yanzu bai samu aiki ba. Wannan dalilin ne yasa 'yan ragowar kud'in da suke hannun Intisar suka k'are nan da nan, kuma da ta tafi da niyyar sake d'ebo wasu ta A.T.M sai ta tarar da an gark'ame account d'inta, bata da damar shigarwa ko fitarwa, a haka ta dawo gida cikin tsananin tashin hankali.
Ta dawo ba dad'ewa Shamsu shima ya shigo cikin gidan, sannu da zuwa tai mishi ya amsa, sannan ta tashi ta kawo mishi ruwa ya karb'a ya sha, ya kalleta ya ce, "Ba wani abun tab'awa a gidan ne?" Intisar ta ce, "Kasan kayan abinci duk sun k'are, kuma kud'in hannuna ya k'are gabad'aya, sannan naje cirowa an rufe account d'ina, gaskiyarka ne Dad ba zai tab'a k'yalemu ba, gwara ma da muka sauya wajen zama."
Shamsu yai wata uban hamma, sannan ya kalleta kallo mai cike da tausayawa ya ce, "Ni ina ganin zan siyar da wayar hannuna sai in siya mana abinda zamu ci kafin Allah ya warware mana komai."
Intisar ta ce, "A'a, ba zaka saida taka ba, ka siyar da tawa, kuma in ka amince ni ya kamata na je na nemo aiki saboda takarduna sun yi kyau kaga sai mu samu abinda zamu rik'a rufawa juna asiri kafin komai ya warware."
Shamsu ya ce, "Shikenan sai mu rik'a fita tare duk wanda ya samo aikin shikenan," da wannan shawarar suka kwanta a ranar ba tare da sun ci komai ba, haka sukai ta juyi saboda yunwa, da k'yar suka samu suka yi bacci musamman ma Intisar.
Washe gari a wahalce Shamsu ya fita da sassafe ko Intisar bata tashi daga bacci ba ya je ya siyar da wayarshi ya zo ya tule musu kayan abinci. sai da ya gama jerawa sannan ya tasheta ta d'an dafa musu wani abun.
Kafin wata d'aya abincin nan shima ya k'are, gashi har lokacin basu samu abin yi ba, gabad'aya sun rame, gashi abinda zasu kai baki ma yana musu wahala, Intisar kuwa cimar da ko a mafarki bata tab'a kawowa zata ci ba sai gashi in ta samu da farin ciki zata karb'a tana murna.
Duk kamanninsu ya sauya, dukkansu sun saba da sai dai a basu gashi yanzu rayuwa ta sauya musu, sai sun nemo sannan zasu zo su sarrafa su ci. Amma abun mamakin duk da wannan rayuwar da suke ciki bai sa ko kad'an Intisar ta karaya ba, saima k'ara jin farin ciki da natsuwa da take saboda ganinta tare da masoyinta.
Shamsu kuwa abun ya fara damunshi, yana tunani akan lallai ba makawa hakkin iyayensu ne ya fara tambayarsu, shi yama fi jin tausayin Intisar, yanda yaga ta zab'eshi fiye da iyayenta, kai fiye da kowa ma, kuma har zuwa yanzu babu nadamar hakan a tattare da ita. Kullum burinta su yi aure, gashi har wata d'ayan da yai mata alk'awari ya shud'e har an kusa fita na biyu ma a shiga na uku ba labari, itama kuma yanzu ba bayani,wannan dalilin ne yasa Shamsu ya amince mata da neman aikin nata, duk garin Allah in ya waye tare zasu fito su tafi neman aiki.
Yau ta kasance Juma'a babbar rana, suma su Intisar sai ta zame musu Babbar ranar da basa tab'a iya mantawa da ita a rayuwarsu, musamman ma ita. Kamar kullum yauma da garin kwaki da suga suka karya, bayan sun gama sai suka shirya suka fita, a k'ofar gida suka yi sallama kowa ya kama hanyar inda zai tafi neman aikin. Wata Unguwa Intisar ta shiga, wadda a cikin unguwar kuma akwai wasu tak'adiran yara marasa ji, d'an mai unguwar ne ogansu, sam basa ji sun gagari kowa hatta iyayensu, sun sha yiwa yaran unguwa fyad'e, k'aramin abu ne a wajensu su yiwa mace fyad'e a gaban iyayensu, matar aure kuma a gaban mijinta. Suna hango Intisar suka hau binta da kallo, can sai Ogan nasu mai suna Inda Hadi ya ce, "Ke zo nan," Intisar ko kallon inda suke bata yi ba, tasowa yayi da sauri ya sha gabanta, sannan ya kalleta yana nunata da yatsa ya ce, "Ke dan uwarki hala ke bak'uwa ce a garin nan da har zan kiraki ki wuce?" Bata ce mishi komai ba, sai ta matsa gefe zata wuce ya sake shan gabanta, ta d'aga hannu ta daddage ta kotsa mishi mari, tana marinshi ya dafe kunci, yaranshi suka taso mata ya dakatar da su da hannu, sannan ya kalleta ya ce, "Kin ci sa'a ina sonki, amma duk da haka sai kin biya marin nan da kika yi wallahi, jeki abinki." Tsaki ta ja, sannan ta wuce abinta ta cigaba da tafiya. Wajen zamansa ya koma, ya kalli d'aya daga cikin yaransa ya ce, "Ubalele maza tashi ka bi yarinyar can ka rakata," Ubalele ya ce, "An gama Oga," ya tashi ya bita a baya kamar yanda mai gidanshi ya ce. Shi kuwa Inda Hadi bin Intisar yake da kallo yana lasar leb'e sai kace tsohon kwarton kare, ya ce, "Gaskiya za'ai matuk'ar hutawa tare da yarinyar nan, ko 'yar gidan uban waye anjima sai na haura katanga da daddare."
A k'a'idarsu idan Inda Hadi ya ce a raka yarinya to lallai gidansu yake bukatar a gano mishi, idan kuwa ya ce sai ya haura katanga to yana nufin sai ya kwanta da mace ko wacece kuwa, kuma indai ba wani iko na Allah ba to abu biyun nan zasu hanashi aiwatarwa. In ba mutuwa yayi ba ko ya kwanta matsanancin rashin lafiya to sai ya aikata.
Shamsu kuwa yana fita ya shiga nan ya shiga can yana neman abun yi amma shiru ba labari, da k'yar ya samu wani mutumi ya kwatanta mishi wani bawan Allah da yake baiwa matasa napep suna kawo mishi balance, yana zuwa kuwa cikin sa'a ya amince zai bashi keke napep d'insa ya rik'a tuk'awa yana kawo mishi balance yana biyanshi.
sai da aka kafa shaidu sannan ya saka hannu a takarda aka biyoshi har gida suka ga gidanshi tukunna. Sannan aka karb'i lambar wayarshi ya bashi makulli ya ja ya tafi.
A hanya ne ya had'u da Intisar zata koma gida, kwana ya yo, a gabanta ya faka sannan ya lek'o da kanshi yana kallonta yana mata murmushi, ya ce, "Tafiya ne 'yan mata?" jin muryar Jaruminta ya sata juyowa da sauri tana kallonshi, cikin farin ciki da mamaki ta shiga ta zauna sannan ta kalleshi ta ce, "Ga dukkan alamu safiyar yau da sa'a ta zo mana, "Shamsu ya ce, "Wallahi kuwa Jaruma, kamar da wasa Allah ya taimakeni na je gidan wani mutumi da aka kwatantamin yana bada napep da mashina a rik'a kawo mishi balance, ina zuwa na tarar ya kori d'aya daga cikin ma'aikatansa saboda yana mishi wasa da kud'i, shine fa aka bani, sai dai ki tayani da addu'a naji ana fad'in rashin mutuncinsa akan kud'i Allah yasa mu rabu lafiya."
Intisar tai murmushi, sannan ta ce, "Ba zaka dad'e ba ma zaka mayar mishi da abunshi, domin kuwa nima yau na samu aiki." Nan sukai ta taya junansu murna har suka k'arasa gida. Sai dai abinda basu sani ba shine, Ubalele ya biyosu a baya a kan mashin har sai da yaga gidan da suka shiga sannan ya juya ya tafi.
Shamsu kuwa yana ajiyeta yai mata sallama ya fito neman na abinci, sai da ya cika napep da mutane sannan ya mik'i hanyar zuwa cikin gari, domin duk fasinjojin na can ne. Bayan ya saukesu ya juyo zai koma gida ya ci abinci yai wanka sai ya sake fita . Yana cikin tafiya sai ya ji fitsari ya matseshi, faka Napep d'in yayi, ya fito cikin sauri ya je gefe ya fara, yana cikin yi ne sai ga wasu sun zo suna k'ok'arin jan mashin d'in su yi gaba da shi, yana waigowa ya hangosu, da gudu ya k'araso wajen suka rufeshi da duka, har da buga kanshi a jikin k'arfen napep d'in, nan ya fad'i a sume inda su kuma suka ja napep d'in sukai gaba abinsu suka barshi nan kwance.
Shi kuwa Ubalele yana komawa wajen Inda Hadi ya sanar da shi unguwar da suke, Inda Hadi ya ce, "To me zamu jira, mu fasa kawai," tashi suka yi suka shiga motar Inda suka d'auki hanya sai k'ofar gidan su Shamsu.
Shamsu kuwa bai dad'e a sume ba Allah ya taimaka ya farfad'o sakamakon wata sassanyar iska da ta buso, a hankali ya bud'e idanu tare da mik'ewa zaune yana dafe da kanshi.
Hawaye ya fara yi yana salati, a haka ya tashi da k'yar ya fara tafiya, yana tafe yana ganin jiri, sai da yai tafiya ba 'yar kad'an ba sannan ya k'araso gida.
Tun daga nesa yake kallon motar da ke fake a k'ofar gidan gabanshi na fad'uwa, yana mamakin wane bak'o suka yi haka masu mota, amma har ya k'araso bai samu amsa ba, kai tsaye ya shige ciki inda ya jiyo sautin ihun Intisar a cikin d'aki tana kururuwar neman taimako.
Da gudu ya shigo yana k'ok'arin shiga ciki yaran Inda Hadi suka rik'eshi, wani irin kukan kura yayi ya watsar da su sannan ya shige cikin d'akin da gudu, d'ago Inda Hadi yayi wanda ya dad'e yana keta mata haddi, kallonta yayi tare da runtse idanu hawaye suka fara ambaliya a fuskarshi, duka ya fara kai mishi, amma su Ubalele na shigowa sai suka rirrik'eshi, sanadin damuwoyi da b'acin rai ga kuma ciwon da ya ji yasa suka samu galaba wajen rirrik'eshi tamau, nan suka k'ara yi mishi duka, kuma a gabanshi Inda Hadi ya k'ara yiwa Intisar fyad'e, yana kuka itama tana yi, bayan ya gama abinda ya kawoshi ya tashi ya maida kayanshi, sannan ya kalli Shamsu ya ce, "Wannan Beb d'in bata dace da miji irinka ba, dan haka ka gaggauta sakinta yau, gobe da daddare zan zo in d'auki kayata, ya juya ya kalli Intisar ya ce, "Baby sai na dawo ko." Daga nan ya fita, sai a lokacin suma yaranshi suka saki Shamsu suka fice daga d'akin
Kuka Shamsu yake sosai kamar ranshi zai fita, itama Intisar haka. Da rarrafe ya k'arasa wajenta, yana kallonta sau d'aya yai saurin kauda idanu, zani ya jawo da k'yar ya rufe mata jiki da shi, sannan ya had'a kai da gwiwa yana kuka kamar k'aramin yaro. Intisar ma kukan take sai dai nashi yafi k'ara, ita saboda tsananin kukan da tasha yau har ya sa muryarta ma ta dishe.
Kanshi yake k'ara bugawa a jikin bango, yana sake fashewa da kuka, yana fad'in "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!"
_Ya Allah ka gafarta mana zunubanmu, ka bamu ikon gamawa da duniya lafiya, ka bamu ikon kyautatawa iyayenmu da yi musu biyayya har k'arshen rayuwarmu._
*πΈπ¦ZAMAN AMANA WRITERS*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)π€π€
*DOMIN SAMUN DUKKANIN LITATTAFANMU A FACEBOOK DA BAKANDAMIYA TSOFAFFI HARMA DA SABABBIN DON YI MANA LIKE DA COMMENT, GROUP 'DINMU NA FACEBOOK BIYU NE, DUK WANDA KA SHIGA ZAKA SAMU LITATTAFANMU A CIKI.*
ππππ
https://www.facebook.com/gidanzamanlpydaamana/
NIMCYLUV
*ALLAH YA WADATAKI DA LAFIYARSA, ALLAH YA DUBEKI YA YAYE MIKI DUKKANIN ABINDA YAKE DAMUNKI, ALLAH YA TASHI KAFA'DUNKI YASA KAFFARA CE.*ππππππππππ
MUHAMMAD KAREEM (MK)
*GAISUWAR BAN GIRMA DA JINJINAR K'ASAITA, ALLAH YA BIYAKA DA KYAKKYAWAN TUKUICI NA LADA AKAN K'OK'ARIN DA KAKE KANMU NA POSTING, DA KAI DA DUK MASU YI DA WANDA NA SANI DA MA WANDA BAN SANI BA ALLAH YAI MUKU TUKUICI DA GIDAN ALJANNARSA.ππππππππππ*
πNUSYπ SANADIN K'IYAYYA FANS
*INA ALFAHARI DA KE, INA ALFAHARI DA SAMUN MASOYIYA TA HAK'IK'A IRINKI, ALLAH YA BAR K'AUNA.*
*HAFEEZ 'DINA MASOYIN GASKE INA ROK'ON MAHALICCINA YA 'DORARMIN DA LAFIYARKA, WANNAN KARON CIWO YASA BAN SHA DARIYAR COMMENT 'DINKA BA, ALLAH YA BAKA LAFIYA.*
*BA WANDA YA KAI MAI YIN SOYAYYA JURE BAK'AR WUYA, TAMKAR HATSARI TAKE IN AKA FA'DA DOLE A TAUSAYA.*
SHAFI NA ASHIRIN DA 'DAYA
Da d'akunan Intisar ta fara Shamsu yana tayata, bayan ta gyara ko'ina shi kuma ya share. Bayan sun kammala da d'aki suka fito tsakar gida, shi ya share tsakar gidan ita kuma ta wanke ban d'akin. Bayan sun gama sai ta d'ora musu abincin rana, da yake a gas ne tana kusa da shi, shi kuma Shamsu yana tayata da k'ananan abubuwa irin su b'are magi, yanka albasa da makamantansu.
Jelop d'in taliya ta dafa, bayan ta kammala sai ta zuba a d'aya daga cikin kulolin da suka siyo jiya, yanzu a k'oshe suke shiyasa suka ajiye zuwa anjima idan rana ta yi.
Hira kawai Intisar ke janshi da shi saboda ita sam ta tsani wannan fitar tashi ta neman aikin da yake magana akai, ba dan komai ba sai don kishinsa da take ji a ranta. Shi kuma ya riga da ya fahimci manufarta sarai, shiyasa ya katseta daga labarin da take ta bashi na makarantarsu da baya ma fahimtar komai a ciki. Kallonta yayi ya ce, "Tunda mun gama aikin to ki barni na tafi, ko kuma ki tashi mu tafi taren." Intisar ta b'ata rai, sannan ta ce, "Ni wallahi fitarka wajen ne gabad'aya bana so, kawai ka zauna tunda inada ragowar kud'i a hannuna idan sun k'are ma nemi wasu."
Shamsu ya kalleta ya ce, "Ai ba na kashewa zan fita nema ba, na aurenki zan fita nemowa." Cikin sauri ta ce, "Eh naji har na sadakin ma duk zan ware maka a ciki."
Cikin sauri Shamsu ya tashi yana fad'in, "Bari dai ki gani," Yana tashi ya fito da gudu, itama da gudun ta tashi ta biyoshi, sai dai koda ta fito bata ganshi ba. K'ofar gidan ta lek'a hagu da damansa amma babu shi ba alamarshi. Cikin gida ta dawo tana share hawayen da ke wanke mata fuska.
Jiyo sautin kukanta da yayi ne yasa ya fito daga mab'oyarsa, ta bayanta ya b'ullo yana murmushi, magana yayi a hankali ya ce, "Ranki ya dad'e kukan me kike kuma bayan gani a gefenki?" A d'an razane ta juyo tana kallonshi.
Kunne ya kama tare da d'an b'ata rai irin na kalar neman afuwa, duka zata kai mishi cikin fushi sai ya kauce yana dariya, ruwa ta d'auko cike da bokiti ta watsa mishi, nan da nan ya hau makyarkyatar sanyi har hak'oranshi suna k'ara, ita kuwa sai dariya take mishi tana tsalle tana fad'in, "Yeeeee na rama, na rama."
Cikin fushi shima ya cika bokiti da ruwa ya bita tana guduwa da haka har ya samu itama ya shek'a mata a jiki, haka sukai ta yi duk suka bi suka jik'a gidan, basu ankara ba sai gani suka yi sun k'arar da ruwan bokitin gabad'aya.
Kowanne bedroom d'insa ya nufa dan su canza kaya, gashi ita kuma Intisar bata taho da komai ba banda kayan jikinta, hakan ne yasa ta fito daga cikin bedroom da wad'annan jik'ak'k'un kayan ba tare da ta cire a. Shi kuwa Shamsu har ya canza kayan jikinshi ya fito falo ya zauna yana jiranta, yana ganin ta sake fitowa da jik'ak'k'un kaya ya kalleta ya ce, "Ya haka naga har yanzu baki canza wannan jik'ak'k'un kayan ba, ko so kike sai mura ta kamamin ke?"
Intisar ta kalleshi ta ce, "Ka manta ban taho da kaya ba?" Sai a lokacin Shamsu ya tuna, cikin sauri ya tashi ya shiga cikin d'akinshi ya d'auko wata tsummar jallabiyarsa ya zo ya bata ya ce, "Gashi ki saka ki shanya naki idan sun bushe mu je kasuwa mu siyo kaya," Intisar ta karb'a tare da komawa cikin d'aki ta saka, bayan ta saka sai ta fito, tareta yayi, ya karb'i kayan hannunta ya fita ya shanya sannan ya dawo ya zauna nesa da ita ya kalleta ya ce, "Amma nai mamaki da kika iya saka jallabiyyar nan ba tare da k'yama ba, hankalinki a kwance."
Intisar tai dariya, sannan ta kalleshi ta ce, "wani abun idan ka fad'a mamaki kake bani wallahi, ita k'auna ta asali ba ruwanta da k'yank'yami, baka iya k'yank'yamin abinda kake muradi, wadda take soyayya da mahaukaci fa sai tace me? kuma duk abinda ya bata sai ta sa a bakinta, balle ni da na saka tufafin da ya zama mallakinka taya zan ji k'yank'yamin duk wani abinda ya fito daga wajen abin sona? Gaskiya wannan abin da ka fad'a tamkar zunubi ne. Ni wallahi yanzu haka ma tsantsar farin ciki nake ji na saka kayan mijina, kuma daga yau ma ta zama tawa."
Shamsu yai murmushi, sannan ya kalleta ya ce, "Gaskiya na zama mai sa'a tunda gani yau zaune tare da autar mata, kin san me ke bani mamaki a yanzu game da ke?" Intisar ta ce, "A'a sai ka fad'a."
Shamsu ya ce, "Naga farin ciki a tare da ke, sam bakya cikin damuwa duk da halin da muke ciki kuwa," Intisar ta ce, "Ban gane ba?" Shamsu ya ce, "Ina nufin bana ganin alamun kina tunowa da gida."
Intisar ta ce, "Ban manta da su ba, amma a yanzu farin cikin kasancewa tare da kai yasa ko tunawa da su ma bana yi, kuma koda hakan ba dai-dai bane to ni hakan shine sanadin cigaban farin cikina da kuma numfashina, ba abinda so baya sanyawa Jarumina, a yanzu jina nake koda mutuwa zakayi sai dai mu mutu tare amma ban iya janyewa daga gareka, saboda na fahimci cewa farin cikina yana tattare da kasancewa tare da kai ne."
Shamsu yai murmushin da ke bayyanar da jin dad'insa, kallonta yake yana k'ara jin tsananin k'aunarta a cikin ranshi, ya ce, "Akan kula dake zan iya bada rayuwata, tabbas na yarda had'uwarmu had'in Allah ne," Hira suka ci gaba da yi cikin farin ciki da annashuwa. A cikin hirar ne Intisar ta kalli Shamsu ta ce, "Ka kira Mubarak kuwa ka ji ya isa lafiya? Ni kasan tawa wayar tun jiya ta d'auke ba caji, kuma dukkanmu ba wanda ya taho da caza, kuma naga gidan ma kamar ba wuta." Shamsu ya ce, "Eh gaskiya ya kamata ace mun kirashi mun ji ya ya isa gida daga nan mu sake yi mishi godiya," wayar ya d'auka ya lalibo lambar ya kira, sai dai wata baturiya ce ke fad'a mishi cewa katin cikin wayar ya shek'e. Dole suka hak'ura da niyyar idan sun fita sai su siya katin ita kuma Intisar ta daga nan sai bada cajin wayar ta-ta wajen masu caji.
Bayan kayan sun bushe ta saka suka tashi suka fita tare da jawo gidan suka tafi kasuwar da aka nuna musu jiya, wajen caji suka hango, Shamsu ya ce, "Ina wayarki mu bada caji, idan zamu koma gida sai mu amsa in kuma bata cika ba ni sai na sake dawowa na karb'ar miki." Intisar ta bud'e jakarta domin ta d'auko ta bashi, amma koda ta duba ba waya ba alamunta ta mantota a gida. Ta kalli Shamsu ta ce "Na manta da wayar a gida." Shamsu ya ce, "Shikenan idan mun koma gida sai in kawo tunda naga wajen."
Da haka har tsawon sati uzurirrika sukaita shan gabansu har maganar kiran Goga domin su yi mishi ban gajiya ta shiririce.
Alhaji yana zuwa station d'in yai fakin d'in motarsa, cikin sauri ya fito daga cikin motar ya shiga station d'in, kai tsaye Office d'in D.P.O ya zarce, bud'e k'ofar yayi ya shiga d'auke da sallama.
D.P.O yana ganinshi ya mik'e suka gaisa cikin mutunta juna, bayan sun gaisa sannan suka zauna lokaci guda. Nan D.P.O ya sake yi mishi bayanin duk yanda suka yi da Goga, sannan ya k'ara da cewa, "Har dabara nai mishi irin na aikinmu na ce mishi mun riga da mun d'auki lambar motar wanda ya d'aukesu kuma lambar ba ta kowa ta nuna ba sai tashi, amma saboda taurin kai irin nashi ya kafe, amma duk da haka bari na sa a sake fito da shi, tunda na saka a ladaftar da shi k'ila yanzu tunda ya ci wuya ya fad'i abinda ya sani game da su."
Wayarshi ya d'aga ya kira ya bayar da umurnin a kawo mishi Goga Office d'inshi yanzu. Wasu 'yan sanda ne suka shigo da Shamsu an yi mishi jina-jina, wannan dukan da akai mishi koda ace kisan kai yayi sai haka.
D.P.O ya sake kallon Goga ya ce, "Malam Mubarak yanzu ka shirya zaka fad'a mana inda ka kaisu ka b'oye ko kuwa sai mun cigaba da dukanka?" Goga ya kalleshi, a wahalce ya fara magana ya ce, "Yallab'ai idan zan baku shawara ku ji to gwara ku tattauna abinda kuka ga ya dace ku yanke zaku yi a kaina, amma wallahi billahil azeem kaji na rantse koda kasheni zaku yi ba zan sanar da ku komai ba, bazan tab'a fad'a muku inda suke ba, dan haka ku yanke hukuncinku kawai a kaina."
Cikin fushi Alhaji ya wanke Goga da mari, sannan ya shak'o wuyanshi yana fad'in, "Dan ubanka sai kun fitomin da 'yata, na sani sarai kasan inda take."
D.P.O ne ya taso da sauri ya b'amb'are hannun Alhaji a wuyan Goga, ya kalleshi ya ce, "Haba Alhaji, ka yi hak'uri mana ka kwantar da hankalinka, binciken nan fa yanzu aka fara, kuma nasan dole sai ya fad'i gaskiyane ma da bakinshi." Alhaji ya koma kan kujera ya zauna yana huci.
Shima D.P.O wajen zamansa ya koma ya zauna, sannan ya kira jami'an da suka kawoshi ya ce su maida shi su cigaba da tuhumarsa har sai ya shirya fad'in gaskiya.
Bayan sun fita dashi D.P.O ya sake ba Alhaji baki akan ya kwantar da hankalinshi, yai mishi alk'awarin zasu cigaba da yin k'ok'ari akan case d'in har sai sun ga an gansu, daga nan Alhaji yai mishi sallama ya fito ya shiga mota ya tafi gida ranshi a b'ace.
Haka akaita ladaftar da Goga akan sai ya fad'i inda su Shamsu suke amma sam yak'i cewa komai a kansu, an yi dukan an yi barazanar duk a banza ya gwammace da ya karya alk'awarin da ya d'aukar musu gwara a kasheshi.
_Samun irin su Goga a wannan lokacin abu ne mai matuk'ar wahala, domin kuwa yanzu rayuwa ta zama abinda ta zama, jira kawai mutum yake ya ji sirrinka ko kuma ka bashi amana ya samu na watsawa a duniya, to wannan babbar cin amana ne kuma shi kad'ai ya isa hana mutum gamawa da duniya lafiya muddin bai tuba ba._
Ganin har tsawon sati amma ya k'i fad'a musu gaskiya yasa D.P.O ya sake neman Alhaji domin sake wata shawarar daban.
Bayan Alhaji ya k'araso D.P.O ya kalli Alhaji ya ce, "Abinda yasa na nemi ganinka Alhaji saboda har yanzu yaron nan ya k'i karb'ar laifinsa, kaga kenan bamu da hujjar cigaba da rik'eshi tunda har yanzu bamu da k'wak'k'warar sheda a hannu, zamu sallameshi ya tafi, amma inada wata dabara wadda zai sa su zo hannunmu cikin sauk'i."
Alhaji ya ce, "Ina jinka wannan wace dabara ce?" D.P.O ya ce, "Zamu rik'a bibiyar dukkanin kiran wayarsa domin na tabbatar dole zasu kirashi, sannan zamu baza jami'anmu a k'ofar gidanshi da kayan gida, kuma a sirrance su rik'a binshi a baya duk inda ya shiga har mu fahimci inda suke, amma kar ka ce zaka koreshi a wajen aiki, ka barshi ya cigaba da zuwa aikinshi."
Alhaji yai murmushi, sannan ya ce, lallai wannan shawara ce mai kyau, dama ita aka bi tun farko, shikenan zai cigaba da zuwa aikinshi kamar da."
A gaban Alhajin aka fito da Goga D.P.O ya ce an gano bashi da laifi, aka bashi takarda ya cike sannan aka ce yai tafiyarshi an sallameshi.
*BAYAN WATA 'DAYA*
Alhamdulillah da taimakon kud'ad'en hannun Intisar Shamsu ya gyara musu gida akai fenti sannan ya had'a mata lefe, kuma ta bashi na sadaki, mad'aurin aure kawai ya rage su nema, shima ba tare da sun sha wahala ba da taimakon wannan me gidan da suke ciki ne ya had'asu da wani limami wanda ya amince shi zai daura musu auren, amma ya ce a bari sai ranar Juma'a wato jibi kenan za'a d'aura aurensu a masallaci bayan an idar da sallah.
Hum bayyana farin cikin wad'annan masoya ma ai b'ata baki ne, domin ko yaya zaka kwatantashi ma ya wuce haka saboda tsananin yawansa.
Yau Alhamis, dawowarsu gida kenan, sun je wajen telan da suka kaiwa d'inki sun karb'o kayansu, k'iri-k'iri da karambani da kuma k'arfin hali sun fara zama 'yan gari.
Bayan sun zazzauna suka fito da kayan suna dubawa, cikin farin ciki Intisar wadda sam bakinta ya kasa rufuwa ta kalleshi ta ce, "Sai gani nake kamar zan fika had'uwa fa, gaskiya telan nan ya tsantsaramin d'inkina yanda nake so."
Shamsu ya ce, "Ai sai ranar za'a tantance wanda ya fi wani had'uwa."
Intisar tai dariya, can sai ta ruga da gudu ciki da kayan a hannunta tana fad'in, "Ina zuwa, bari na je na gwada."
Shamsu ya bita da kallo yana mamakin irin wannan zumud'in nata, gaskiya duk da yana tsananin k'aunar Intisar amma ya fahimci k'aunar da take mishi ya zarce wanda yake mata sosai.
Tunowa yayi da Goga akan sun mishi alk'awarin sanar da shi idan bikin ya matso. Cikin sauri Shamsu ya lalibo lambarshi a cikin wayarshi da ke hannunshi ya kira.
A dai-dai lokacin da ya kirane 'yan sandan da keta faman dakon kiran nasu ne suka ji shigowar kiran wata lamba a wayar Goga, cikin sauri suka shirya jin abinda zasu tattauna.
Goga yana kwance a d'akinshi, dawowarshi kenan daga wajen aiki yana cikin hutawa har bacci ya fara d'aukarshi sai ya ji wayarshi tana k'ara alamar ana kiranshi.
Yana dubawa yaga Shamsu ne, cikin sauri ya d'aga, bayan sun gaisa Shamsu ya ce, "Inata neman lambar Hajiya ai bana samu, kai kuma banda taka shiyasa ban kira ba." Shamsu ya ce, " Allah sarki wallahi ba caji ne shiyasa ma bamu kiraka ba, ka yi hak'uri dan Allah, gobe ne d'aurin aurenmu idan Allah ya kaimu, ina fatan zaka samu damar halarta?" Goga ya ce, "Insha Allah zan zo, amma sai anjima zan taho, dan ban san da tafiyar ba, dole yanzu sai na tanadarwa yaran komai kafin na taho." Shamsu ya ce, "Ba matsala, Allah ya kawoka lafiya." Daga nan suka yi sallama ya ajiye wayar.
Cikin sauri suka nad'i abinda suka saurara suka kaiwa D.P.O, bayan ya gama saurara sai ya lalibo lambar Alhaji ya sanar da shi komai, sannan ya ce, "Gobe in Allah ya kaimu zan tura yaranmu su bishi a baya har zuwa inda su Shamsu suke d'in." Alhaji ya ce, "Alhamdulillah, amma D.P.O ni nafi gane aikinka akan na wasu yaranka gaskiya." D.P.O ya ce, "Eh ai da ni za'a je, zasu dai rigani yin gaba ne saboda sune suke k'ofar gidansa, to dan kar mu rasashi dole su zasu yi gaba sai na bisu a baya, in yaso sai su rik'a sanar da mu inda suke."
Alhaji ya ce, "Shikenan D.P.O, amma da ni za'a yi tafiyar," D.P.O ya ce, "Ba matsala, Allah dai ya kaimu goben kawai."
Shi kuwa Goga suna gama waya ya tashi ya fito daga cikin gidan ya shiga mota sai kasuwa, duk abinda ya dace ya siyowa k'annenshi ya sai musu, daga nan ya siyowa amarya da ango tsaraba.
Bayan ya k'araso gida ya shiga da kayan da ya siyowa k'annen nashi, bayan ya ajiye ya kalli babbar k'anwarshi ya ce, "Safiyya ga abubuwan da suka k'are nan na siyo, kuma ga wannan kud'in ki ajiye a hannunki koda zaku buk'aci wani abu, ni wata tafiya ta taso min yanzu, zan halarci bikin wani abokina kuma kwana zan yi, anjima kad'an zan tafi."
Safiyya ta ce, "To yaya, Allah ya tsare ya dawo mana da kai gida lafiya," Shamsu ya ce, "Ameen ya rabbi k'anwata."
K'arfe d'aya da minti ashirin ya d'auki hanya, bayan ya yi sallah ya fito yaiwa k'annenshi sallama sannan ya shiga mota ya jata ya tafi.
Suma 'yan sandan nan a dai-dai wannan lokacin ne suka fito daga mab'oyarsu suka shiga mota suka bi bayanshi.
Sai wajen k'arfe hud'u ya isa k'ofar gidan, yana zuwa ya faka motar, yana fitowa daga cikin motar su Intisar suka fito tare da yi mishi lale marhabin, kayan hannunshi suka karb'a suka shiga dashi yana biye da su a baya.
Cikin d'akin Shamsu ta je ta ajiye kayan Goga, tana ajiyewa ta fito ta d'auko abinci da ruwa ta ajiye gabanshi, tana ajiyewa ta samu waje ta zauna suka gaisa.
Bayan sun gama gaisawa ya zuba ruwa a kofi ya sha, daga nan ya bud'e abincin ya fara ci yana basu labarin abinda ya faru da shi bayan komawarshi gida.
Su kuwa 'yan sandan nan da suka biyo Goga suna karyo kwanar unguwar da suka ga ya shiga cikinta ne suka hango motarshi, a can gaban tashi suka faka tasu, sannan suka kewaye k'ofar gidan kamar yanda aka umurcesu, amma basu shiga ba suna jiran k'arasowar su D.P.O d'in.
Wajen k'arfe hud'e da rabi su Alhaji suka k'araso, suna fitowa kai tsaye suka tunkari gidan gadan-gadan.
Su Intisar kuwa, bayan Goga ya gama basu labarin wahalar da ya sha a hannun 'yan sanda sun yi matuk'ar tausaya mishi, kuma sun k'ara jinjina amanarshi.
Godiya suka yi mishi tare da k'ara bashi hak'uri akan kasadar da ya d'auka na rayuwa a kansu, daga nan kuma suka duk'ufa hirar biki. Goga ya kallesu ya ce, "Wallahi ba k'aramin dacewa kuka yi da juna ba." Cikin tsananin farin ciki da jin dad'in abinda ya ce ne yasa Intisar ta bud'e baki zata yi magana. Doko k'ofar gidan da aka yi ne ya sa dukkaninsu suka yi shiru suna kallon k'ofa domin ganin masu k'arfin halin shigo musu cikin gida haka.
Ganin wad'anda suka shigo ne ya sakasu zaro idanu dukkansu tare da mik'ewa tsaye a lokaci d'aya.
Cikin sauri 'yan sanda suka zagayesu tare da saita kowannensu da bindiga.
*πΈπ¦ZAMAN AMANA WRITERS*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)π€π€
*DOMIN SAMUN DUKKANIN LITATTAFANMU A FACEBOOK DA BAKANDAMIYA TSOFAFFI HARMA DA SABABBIN DON YI MANA LIKE DA COMMENT, GROUP 'DINMU NA FACEBOOK BIYU NE, DUK WANDA KA SHIGA ZAKA SAMU LITATTAFANMU A CIKI.*
ππππ
https://www.facebook.com/gidanzamanlpydaamana/
LITATTAFAN MARUBUCIYAR:
1 *RAYUWATA TAKI CE*
2 *KA CUTAR DA NI!*
3 *NA'KASASHSHE MA MUTUM NE*
4 *LAIFIN WAYE?*
5 *LAIFIN WAYE SABON SALO*
6 *SO MAHA'DIN RAYUWA*
7 *ZUCIYAR MUGU!*
8 *ME KE FARUWA?*
9 *LABARIN FATIMA*
10 *NA BAKI RAYUWATA*
11 *AURE*
12 *A SANADIN 'KAUNA*
13 *TASKU!!*
14 *RAYUWAR RAYAM*
AND NOW...................... BA ZASU GA DAI-DAI BA
A~A~S
*INA ALFAHARI DA KE, KUMA INA K'AUNARKI.*
HADY LOVE
*JINJINA TA MUSAMMAN A GAREKI, ALLAH YA BIYAKI AKAN K'OK'ARINKI, INA ALFAHARI DA KE.*
HAUWA LAWAL
*KINA CIKIN JERIN HAK'IK'ANIN MASOYAN DA BASU TAB'A GOGEWA A ZUCIYATA, INA K'AUNARKI RABIN RAI.*
SHAFI NA ASHIRIN
Tun daga nesa Goga ya fara hango Jami'ai rututu a k'ofar gidansu, gabanshi ne ke fad'uwa, yana tunanin abinda ya kawosu k'ofar gidanshi, babu irin tunanin da bai zo zuciyarshi ba, dan har tunani yayi ko dai an gano cewa shi ya taimakesu ne, amma lokaci guda ya kauda wannan tunanin saboda shi a ganinshi ba wanda ya hangosu. Duk da haka bai fasa tunkarar k'ofar gidan ba domin yana so ya ji k'arin bayani a wajensu na dalilin zuwan nasu, amma duk da haka gabanshi bai dena fad'i ba.
A haka ya k'araso k'ofar gidan, tun kafin ya samu damar faka motar suka zagaye motar tashi, bayan yai fakin sai d'aya daga cikin jami'an ya bud'e k'ofa ya ce ya fito.
Ba musu ya fito, sannan ya kallesu ya ce, "Yallab'ai lafiya na ganku a nan?" Babbansu ne ya kalleshi ya ce, "Gayyatarka ofishinmu muka zo yi domin ka je ka amsa mana wasu tambayoyi." Goga ya ce, "Amma Yallab'ai a kan me zaku tafi da ni bayan na san ban yi komai ba?" Kallonshi ya yi ya ce, "Sai mun je can zaka ji koma menene," Goga ya ce, "Amma Yallab'ai......................" Dakatar da shi d'an sandan nan ya yi, ta hanyar d'aga mishi hannu. Ya kalleshi ya ce, "Bama son jin komai a yanzu, duk abinda kake son fad'a ka adanashi a ranka sai mun je can, dan haka wuce mu tafi."
Ko gida basu barshi ya shiga ba suka tasa k'eyarshi suka tura a motarsu suka ja suka tafi da shi.
Kai tsaye station suka wuce da Goga, Office d'in D.P.O aka wuce da shi. Bayan D.P.O ya gama wayar da suka shiga suka tarar dashi yana yi, sai ya kalli jami'an da suka kamo Gogan ya basu izinin tafiya. Bayan sun fita sai ya jawo wani littafi wanda daga gani kasan kundi ne na ajiye bayanan masu laifi. Bayan ya d'an yi rubutu a ciki sai ya d'ago ya kalli Goga ya ce, "Menene sunanka?" Goga wanda ke zaune gaban D.P.O ya d'ago ya kalleshi cikin damuwa ya ce, "Sunana Mubarak."
D.P.O ya ce, "Malam Mubarak ko kasan Alhaji Tajuddeen?" Goga ya ce, "Eh na sanshi," D.P.O ya ce, "Menene alak'arka da shi?" Goga ya ce, "Ina aiki a kamfaninshi ne." D.P.O ya ce, "A bayanan da suka gabata ya nuna cewa a kwanakin baya can ka yi garkuwa da 'yar Alhajin da kuma mai gadinsa, daga baya da aka kamaku sai ka sanar da dalilinka na yin garkuwa da su, wanda dalilin ya kasance akan sauya ra'ayi da ya yi na k'in d'aukarka aiki ne sanadin damunshi da kayi akan ya baka bashi kafin ka fara aiki, silar haka ya jawo ka rasa mahaifinka, sakamakon wannan rashin ne itama mahaifiyarka zuciyarta tai mummunan bugawa ta mutu. Wannan dalilin ne ya jawo ka yi fushi har ka yi garkuwa da su, kuma a yanda ka sanar ka so ka kashe Alhaji ne idan ya kawo kud'in nan, amma sanadin taimakon da 'yarsa tai maka ne na sawa mahaifinta ya d'aukeka aiki da kuma hak'urin da ta baka yasa ka jinkirta da d'aukar fansarka. To amma meyasa kuma ka sauya ra'ayinka na yafe musu ka sake sacesu a karo na biyu?"
Cikin kad'uwa Goga ya d'ago ya kalleshi ya ce, "Wallahi Allah ban sacesu ba yallab'ai, banma san inda suke ba."
D.P.O yai murmushi, sannan ya kalli Goga ya ce, "In baka sacesu ba to lallai ka taimakesu sun gudu, dan haka karka wahalar da mu ka sa mu wahalar da jikinka, ka fad'a mana gaskiya kawai, ina ka kaisu?" Gaban Goga ne yai wani irin fad'uwa, tabbas sun ganshi kenan tunda har suka gane cewa shine ya d'aukesu a motarshi, ba mamaki ma sun d'auki lambar motarshi. Yana cikin wannan tunanin ne ya ji D.P.O yana cewa "Kada ka tsaya b'atamin lokaci kaji, mun riga da mun gano kaine ka d'aukesu a motarka, mun ga shedar tayar mota a k'ofar gidan su Shamsu, sannan lokacin da jami'anmu suka bi bayan motarku sun d'auki lambar motar da suke ciki wanda yai dai-dai da irin lambar motarka. Dan haka kawai ka fad'amin gaskiya kaji ko."
Shamsu ya fara hawaye, ya ce, "Wallahi yallab'ai ban sacesu ba, ni ba sana'ata bace dama yanayin rayuwane yasa nai hakan a baya, amma na dad'e da dainawa. Su Intisar kuma ban san inda suke ba, kuma koda na sani wallahi ba zan fad'a muku ba." D.P.O ya kalleshi a fusace ya ce, "Ok haka ka ce ko? Tunda haka ka zab'a shikenan."
Sunan Jami'ai biyu ya kira suka amsa, sai gasu sun shigo da sauri suka k'ame tare da sarawa, D.P.O ya kallesu ya ce, "Ku kaishi cell, sannan ku tabbata kun tuhumeshi da kyau ya fad'i gaskiyar inda ya je ya b'oyesu." Amsa mishi suka yi tare da tasa k'eyar Goga suka fice daga Office d'in.
B'angaren Alhaji kuwa banda tsananin b'acin rai ba abinda yake sawa a ranshi, a duk inda ya zauna aikin kenan. Yau ma haka yana zaune a kan dining suna karyawa, banda jujjuya cokali ba abinda yake. Can kuma sai su Hajiya suka ji a fusace yana magana shi kad'ai ya ce, "Inaaaaa ba zai tab'a yiwuwa ba, ba zan bar 'yata tai rayuwar talauci ba."
Hajiya ta kalleshi ta ce, "Dan Allah Alhaji ka sassautawa zuciyarka wannan damuwar," Alhaji ya kalleta kallo wanda ke bayyanar da tsananin takaici, sannan ya ja tsaki, ya ce, "Dubeki dan Allah, 'yarki ta kwana a waje tare da wani k'aton gardi amma ke ko a jikinki, to bari kiji, ni nawa hankalin ba zai tab'a kwanciya ba har sai naga an kama wannan tsinannen yaron da ya hurewa 'yata kunne har yasa ta bijirewa maganata ta bishi, dan nasan irin k'aunar da na nunawa 'yata ba zata zab'i ta watsamin k'asa a ido haka kawai ba sai da taimakon wannan d'an iskan yaron, kuma wallahi ba zan barshi ba."
Yana gama fad'in haka ya tashi ya shiga cikin d'akinsa, yana shiga ya d'auki wayarshi da ke kan gado ya lalibo lambar D.P.O wanda kwamishina ya dank'a ragamar case d'in a hannunshi. Tana fara ringing ya d'aga, bayan sun gaisa Alhaji ya ce, "Ba dai wani labari har yanzu ko D.P.O?"
D.P.O ya ce, "Yanzu nake shirin kiranka nima Alhaji, har yanzu bamu samu labarin inda suke ba, amma tunda Mubarak d'in da ya d'aukesu a motarshi yana hannunmu a halin yanzu to na tabbatar zamu samu bayanan inda suke a wajenshi."
Cikin farin ciki Alhaji ya ce, "Ok kun kama Gogan ko? Alhamdulillah, gani nan zuwa station d'in sai mu k'arasa tattaunawar a nan, daga nan in ga idanun Mubarak d'in shima d'an iskan."
Nan suka yi sallama da D.P.O akan zai taho station d'in yanzu domin ya k'arasa jin bayanai.
Su Intisar kuwa suna shiga cikin gida suka samu waje suka zauna fuskarsu tana fuskantar juna, Intisar ta kalli Shamsu tana murmushi ta ce, "A iya tunanina da nazarina na gano cewa babu abinda ya kai kasancewa da masoyi a waje guda wanzar da farin ciki."
Shamsu ya kalleta shima yana murmushi ya ce, "Nayi alk'awari ba zan tab'a bari a rabani da ke ba, bazan tab'a bari ki kub'ucemin ba, kuma ba zan tab'a rabuwa da ke ba, kuma zan cigaba da sonki har k'arshen rayuwa." Cikin farin ciki Intisar ta ce, "Da gaske ka yi alk'awari ba zaka barni ba?" Shamsu ya ce, "Eh, nai miki alk'awari zan tsaya a gefenki duk tsananin da zamu kasance a ciki to tare zamu fuskanta."
Intisar ta ce, "Nagode wa Allah da ya mallakamin kai, ji nake a raina tunda na sameka na gama samun dukkanin nasara ta rayuwa."
Shamsu ya mik'e ya ce, "Idan na biye ta taki ba zaki tab'a barina na fita ba." Intisar ta ce, "Wai nufinka fita zaka yi ka barni ni kad'ai a cikin gidan?" Shamsu ya ce, "Eh mana, fita zanyi in je neman na aurenki mana, dan so nake a 'yan watanni igiya ta aure ta k'ullu a tsakaninmu."
Intisar tai murmushi, sannan ta ce, "In kai haka da ko ka kyauta. Shamsu ya kalleta yana dariya ya ce, "Iyye, ko kunyata ma bakya ji kike fad'in haka a gabana?" Intisar tai dariya, sannan ta ce, "Menene abun jin kunya dan nayi farin ciki abinda nake muradi zai zama mallakina ni kad'ai?" Shamsu ya ce, "Kinga kada ki tsareni da surutu, bari in tafi da sanyin safiya ake kama fara."
Mik'ewa tsaye tayi cikin sauri ta sha gabanshi tana fad'in, "Wallahi ba zaka barni ni kad'ai ba haka kawai salon ka d'aurawa zuciyata jinyar da bata shirya mata ba." Shamsu ya ce, "Wace irin jinya kuma ana zaune k'alau?" A shagwab'e ta ce, "Ta tunaninka mana."
Shamsu yai murmushi, jinta yake sosai a ranshi, kallonta yake yana murmushin shagwab'ar da take yi, wadda take matuk'ar burgeshi. Ya ce, "Yanzu me kike so a yi?"
Intisar ta ce, "So nake ka zauna in gama gyara ko'ina sai mu tafi neman aikin tare." Shamsu ya zaro idanu yana mata kallon kin tab'u ya ce, "Neman aikin ne zan tafi tare da ke?" Intisar ta sake shagwab'ewa ta ce, "Eh mana, wallahi in ba dani zaka tafi ba sai dai a hak'ura dan ni ban yarda ka fita kai kad'ai ba muddin ba tare da ni ba, haka kawai salon wasu matan su kallemin kai, daga nan a fara k'ok'arin kawo maka hari."
Shamsu yai dariya, sannan ya ce, "Intisar sarkin rigima, shikenan yanda kika ce haka za'a yi, irinku ne idan kukaiwa mazajenku shagwaba to dolensu ko basu yi niyyar yi muku abinda kuka buk'ata sanadinta sai sunyi." Intisar tai murmushi sannan ta ce, "Alhamdulillah, na ji dad'i, ko ba komai na gane d'aya daga cikin abinda zaisa in rik'a cutarka da shi." Dariya suka sa gabad'ayansu.
_Da babu gwara ba dad'i aka ce, a yi hak'uri da wannan, kuma a cigaba da yi min addu'a dan Allah_πππππ
*πΈπ¦ZAMAN AMANA WRITERS*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)π€π€
*DOMIN SAMUN DUKKANIN LITATTAFANMU A FACEBOOK DA BAKANDAMIYA TSOFAFFI HARMA DA SABABBIN DON YI MANA LIKE DA COMMENT, GROUP 'DINMU NA FACEBOOK BIYU NE, DUK WANDA KA SHIGA ZAKA SAMU LITATTAFANMU A CIKI.*
ππππ
https://www.facebook.com/gidanzamanlpydaamana/
Zamewa ta yi a bakin k'ofar d'akin nata, ta cigaba da rera wani sabon kukan. Can sai ta zabura ta mik'e ta nufi wayarta da ke kan gado tana maimaita sunan Shamsu a bakinta.
Wayar ta d'auka cikin sauri ta lalibo lambarshi ta kira, tana fara yin ringing sau d'aya sai ta ji ya d'aga, yana d'agawa ya ce, "Kinga abinda nake gudun faruwarsa tun farko ko, burin yawancin iyayenda yaransu suka taso cikin dukiya shine su aurar da su ga mai dukiya koda bata kai tasu ba, amma basa fatan bawa yaransu talaka a cewarsu kuma a ganinsu wahala kawai 'yarsu zata sha, shiyasa suke gudun irinmu." Intisar bata ce komai ba sai kuka da ta fara yi mishi yana rarrashinta. A cikin kukan nata ne ta ce, "Kana ina ne yanzu haka Jarumina?" Shamsu ya ce, "Gani a k'ofar gidanku, amma yanzun nan nake shirin barin wajen kar mahaifinki ya fito ya ganni ya sake yi min wani abun."
Intisar ta ce, "Dan Allah kar ka tafi ka barni." Shamsu ya ce, "Ki yi hak'uri Intisar, dole ce tasa zan yi nesa da ke a yau, amma ki saka a ranki cewa duk inda na tafi muna tare, insha Allah ba zan tab'a barinki ba." Intisar ta ce, "To yanzu ina zaka tafi?" Shamsu ya ce, "Kin manta nima muna da gida ne?" Intisar ta ce, "Ka yi hak'uri ka daina jin haushina, ka san ina k'aunarka, kuma ba ni nai maka haka ba, mahaifina ne." Shamsu ya ce, "Shikenan, bari na tafi, zamu yi waya anjima, ki kula da kanki," Cikin kuka Intisar ta ce, "Kaima ka kulamin da kanka."
Suna gama waya Intisar ta jefa wayar a kan gado, tare da kwantawa ta sake fashewa da wani sabon kukan. Shima Shamsu mik'ewa ya yi, yana rungume da jakar kayanshi a hannu, a haka ya fara tafiya, yana yi yana waigen gidan, har ya daina hangoshi sakamakon wata kwana da ya sha. Yana zuwa bakin ti-ti ya tsaya yana jiran napep domin ta kaishi tasha ya hau ya tafi gida.
Tuno farin cikin da suka kasance a ciki d'azu yake a zuciyarshi, tunani yake a cikin ranshi, yanzu shikenan duk k'aunar da suke yiwa juna da kuma shak'uwar da suka yi duk ta tashi a banza kenan? Tambayar da ya kasa samun amsarta kenan, amma zuciyarshi ta k'i daina bijiro mishi da ita har yanzu. Hawaye ne ya fara wanke mishi fuska, kuma bai damu da ya share ba dan kar mutane su gani, ko ba komai sa fahimci cewa lallai yana cikin matsananciyar damuwa su tausaya mishi.
Wata mota ce mai kyan gaske tai fakin a gabanshi, sam shi Shamsu bai ganta ba, domin shi kawai sunan yana bakin ti-ti ne, amma hankalinshi da tunaninshi baya wajan.
Wanda ke cikin motar ne ya fito tare da k'arasowa inda Shamsu ya ke tsaye.
Yana k'arasawa wajenshi ya fara doka mishi sallama har wajen sau uku amma sam bai ji ba, hannu ya sa ya dafa shi, Shamsu yai firgigit kamar wanda ya farka daga gigitaccen bacci.
Abun mamaki Goga ya gani tsaye a gabanshi, ya yi shar da shi, duk ya canza ya zama tamkar ba shi ba. Cikin sauri Shamsu ya share hawayen fuskarshi, sannan ya bashi hannu suka gaisa, bayan sun gaisa sai Goga ya kalli Shamsu ya ce, "Shamsu lafiya na ganka a nan kuma cikin irin wannan yanayin na damuwa haka?" Shamsu ya kalleshi ya ce, "Ba komai Mubarak, ka tafi abunka kawai ka k'yaleni dan Allah."
Ba yanda bai yi da Shamsu akan ya fad'a mishi damuwarshi ba amma ya k'i, juyawa yayi da niyyar ya tafi tunda ya k'i saurarenshi, sai dai har ya kai bakin motarshi sai ya sake juyowa yana kallonshi, zuciyarshi na raya mishi cewa bai kamata ya tafi ya barshi a cikin irin wannan halin ba. Wayarshi ya ciro a cikin aljihu ya lalibo lambar Intisar ya kirata.
Intisar wadda ke kwance a kan gado tana sharara kuka ta ji wayarta tana k'ara, cikin sauri ta duba, tana dubawa taga Goga ne ke kira, sai dai sam bata damu da ta d'aga ba, tunda ta lura da cewa ba wanda take tsammanin kiransa ba ne, kuma a halin da take ciki a yanzu kiranshi ne kad'ai zaisa ta d'aga waya har ta ji farin ciki.
Sai da ya kirata wajen sau biyar, a na shida ne Intisar ta ja tsaki tare da sa hannunta ta jawo wayar, d'agawa ta yi sannan ta kara a kunne ta ce, "Hello," Goga ya gaisheta ta amsa mishi a tak'aice, sannan ya ce, "Hajiya na kiraki ne akan wata magana, amma na ji muryarki wata iri kamar baki da lafiya ko?"
Intisar ta ce, "Eh bana jin dad'i ne, kuma bana son yawan magana, dan Allah ka k'yalleni sai anjima." Goga ya ce, "Akwai dalilin da yasa na kiraki Hajiya, Shamsu na gani tsaye a bakin ti-ti rik'e da jaka yana cikin damuwa, kuma yana zubar da hawaye, na tambayeshi dalilin damuwar ya ce ba komai in tafi in k'yaleshi kamar dai yanda kema kika fad'amin yanzu. Har na juya zan tafin sai naga bai kamata na barshi cikin irin wannan halin ba shine na yanke shawarar kiranki domin in sanar da ke halin da yake ciki."
Jin wanda aka ambata ne yasa Intisar tashi zaune cikin sauri, ta ce, "Dole mu fad'a maka magana wadda take kamanceceniya da juna Mubarak, saboda damuwarmu iri d'aya ce, yanzu yana ina ne? Kana tare da shi?" Goga ya ce, "Eh gashi can a kusa da ni," Intisar ta ce, "To bashi wayar, ko da yake k'yaleshi kar ka bashi, amma dan Allah Mubarak ka taimakeni kar ka tafi ka barshi cikin wannan halin, ka d'aukeshi ka kaishi gidanku ya zauna na d'an wasu lokuta kafin komai ya daidaita, zan sanar da kai komai daga baya."
Goga ya ce, "Ba damuwa Hajiya, zan iya yi miki fiye da haka saboda kin cancanta." Intisar ta ce, "To nagode sosai, yi sauri ka koma wajenshi kafin ya tsaida abun hawa ya tafi." Nan suka yi sallama shi kuma Goga ya koma wajen Shamsu ya ci gaba da rok'onshi akan ya amince su je gidansu ya samu natsuwa kafin ya tafi k'auyen nasu. Da k'yar da sud'in goshi ya amince suka shiga mota Goga ya ja suka tafi.
Intisar kuwa ta d'an tsagaita da kukanta, saboda ko ba komai a yanzu ta san inda masoyinta yake, zata san yanda zata rik'a yi suna had'uwa har zuwa lokacin da zata samu ta shawo kan mahaifinta ya amince su yi aure.
Shamsu kuwa, bayan sun k'arasa k'ofar gidan su Goga suka fito daga motar, suka shiga cikin gidan d'auke da sallama goga na rik'e da jakar Shamsu a hannunshi.
Suna shiga k'annenshi suka yi musu sannu da zuwa daga nan suka gaishesu, kai tsaye d'akinshi ya wuce da Shamsu. 'Daki ne madaidaici, katifa ce a ciki sai akwati da kuma jakar kaya duk na Goga, sai kuma kayan kallo da ya siya kwanan nan shima ya sa a d'akinshi bayan ya sawa k'annenshi. 'Dakin a tsaftace yake, saboda kullum sai k'annenshi sun shiga sun gyara sun share mishi bayan fitarshi. Gefen katifar d'akin suka zauna, Goga ya kalli Shamsu ya ce, "Ka yi kwanciyarka a nan ka huta kafin in sa a gyara maka d'akin nan da ke kusa da ni." Shamsu ya ce, "To ba damuwa, na gode sosai." Goga ya ce, "Karka damu, Karka manta Hajiya Intisar ta tab'a fad'amin abinda ke tsakaninku, dan haka ta wuce haka a wajena, dan ba zan tab'a manta halarcinta gareni ba, bari in d'an fita in dawo, zan sa a kawo maka abinci yanzu," suna gama magana ya fito daga d'akin, bayan ya umurci babbar k'anwarshi da ta kaiwa bak'onshi abinci sai ya fice daga gidan.
Yana shiga cikin motarshi sai ga kiran Intisar, d'agawa ya yi tare da karawa a kunne. Intisar ta ce, "Ya ake ciki Mubarak ya yarda ya bika d'in kuwa?" Mubarak ya ce, "Eh Hajiya ya biyoni, yanzu haka ma yana cikin gidanmu."
Intisar ta ce, "To dan Allah ka bashi kyakkyawar kulawa, ka yi mishi duk abinda yake buk'ata, gobe in Allah ya kaimu zan zo gidan in ganshi, ko da yake goben in ka dawo daga wajen aiki sai ka biyo kawai ka d'aukeni mu je." Goga ya ce, "Baki da matsala Hajiya, gobe ma Asabar ce ai ba aiki." Intisar ta ce, "To shikenan sai na ganka gobe da safe in Allah ya kaimu." Goga ya ce, "Allah ya kaimu, ai Hajiya babu abinda ba zan iya yi miki ba a duniyar nan, saboda kema kin taimaki rayuwata." Intisar ta ce, "To nagode sosai Mubarak, sai na ganka goben."
Sallama suka yi ta ajiye wayar tana tunani a kan anya kuwa zata iya bari har gobe sannan ta je ta ga Shamsu, tana cikin wannan tunanin ne ta ji k'arar sak'o ya shigo cikin wayarta.
Tana dubawa ta ga sak'on daga wanda tai tsammani ne kuwa. Cikin sauri da zumud'i ta bud'e, tare da fara karantawa kamar haka:
_Kewa wata abu ce da ke bayyanar da damuwa, ita kuwa damuwa tana bayyanar da abinda zuciya ke ji ne, KINA RAINA._
Daga karanta sak'onshi da tayi sai ta ji tausayinshi ya kamata, nan da nan idanunta suka cika da k'wallah, amsa ta fara mayar mishi kamar haka:
_NIMA KANA RAINA. a halin da ake ciki yanzu da baka kusa da ni kewarka ce taketa ziyartata, ka kulamin da kanka._
Shamsu na ganin amsar sak'on Intisar ya ji tausayinsu ya kamashi, wasu zafafan hawaye ne suka wanke mishi fuska. Lambarta ya lalibo ya kira, yana kira ta d'aga, tana d'agawa ta fashe mishi da kuka, dama wannan dalilin ne yasa ya kasa kiranta, dan yasan a yanzu dukkaninsu zuciyarsu a raunane take, rarrashi kowannensu yake buk'ata. Kukanta k'ara dagula mishi zuciya yake, hakan ne yasa ya katse kiran ba tare da ya ce komai ba, cigaba ta yi da kukan, shima Shamsu daga can inda yake yanata tayata.
Yanke shawarar sake zuwa ta samu mahaifinta ta sake rok'onshi ta yi, da wannan shawarar ta tashi cikin sauri ta fita, a falo ta sameshi shi da Hajiya a tsaye suna jimami akan abinda ya faru. A gabanshi ta tsugunna har k'asa, abinda bata tab'a yi mishi ba kenan. Ta kalleshi ta ce, "Dan Allah Daddy ka taimaki rayuwata ka auramin wanda nake so, wallahi raba zuciyata da Shamsu tamkar raba jikina da ruhina ne, Daddy dan Allah, Shamsu shine tubalin da na gina rayuwata a jiki, wallahi yana matsawa bangon rugujewa zai yi."
Tana kammala maganarta Alhaji ya kalleta ya ce, "Ai kuwa sai da ginin ya rushe d'in dan ubanki dan kuwa aure tsakaninki da Nidal wallahi ba fashi. Tashi ki bani waje kafin na fara kai hannuna kan fuskarki."
Da gudu ta tashi ta shige d'akinta, kan gado ta fad'a tare da cigaba da rusa kuka mai matukar ban tausayi.
B'angaren su Alhaji kuwa shima d'akinshi ya wuce a fusace, Hajiya ta biyo bayanshi tana bashi baki.
Yana shiga ya cire babbar rigarshi (malum-malum), ya zauna kan gado, ya tashi, ya fara kai kawo ya sake zama, ya sake tashi, haka yaita yi har matarshi ta shigo ta sameshi.
Zama yayi a bakin gado, sannan ya lalibo lambar wayar Alhaji Ridwan ya cigaba da kira, tun baya d'agawa har Allah ya bashi sa'a ya d'aga, hak'uri yake ta bashi yana fad'a mishi cewa sam bai tab'a kawowa soyayya ce a tsakaninsu ba, amma yanzu ya shawo kan lamarin, kuma idan ya amince shi a gobe ma su zo a d'aura aure ya shirya.
Alhaji Ridwan ya ce, "Kawai a bar wannan maganar Alhaji Tajuddeen, tunda har ta furta ga wanda take so, to koda ace an aura mata shi ba zata yi masa biyayya ba," Nidal da ke gefe yana jin abinda mahaifinsa ke cewa sai yai saurin yi mishi alama akan ya amince, ba dan komai ya ce haka ba sai domin ya koya musu hankali tare da rama abinda aka yi mishi.
_Nidai Bk ba abinda nake tunani da ya wuce wannan rayuwar da muke cikinta a yanzu, wadda sam babu yafiya a cikinta sai tarin cin alwashin d'aukar fansa._
Mahaifin Nidal ya dakatar da maganar da yake tare da kallon yaronshi ya ce, "Au to ka amince kana sonta dai har yanzu a hakan?" Nidal ya ce, "Eh Dad." Mahaifin Nidal ya ce, "To banda ta cewa kuma yanzu, tunda yaro ya amince yana k'aunar 'yarka har yanzu duk da abinda tai mishi ai shikenan."
Sai da Alhaji ya samu mahaifin Nidal ya amince sannan hankalinshi ya d'an kwanta, sai da suka tsayar da magana akan goben zasu zo a d'aura aure daga baya ta tare sannan suka yi sallama.
Bayan sun gama waya Hajiya ta kalleshi ta ce, "Alhaji dan Allah kada ka yanke hukunci cikin fushi, ka........................." Cikin tsawa ya dakatar da ita, ya ce, "Wallahi ki yi min shiru kafin na sauke fushina a kanki." Hajiya ta ce, "Allah ya baka hak'uri," tana gama fad'in haka ta tashi ta fito daga d'akin.
A haka Intisar ta yini ba tare da ta ci komai ba, duk abinda aka kai mata a yanda aka kaishi a haka za'a fito da shi.
Shima Shamsu haka ya wuni ba tare da ko ruwa ya sake kaiwa bakinshi ba, a haka suka kwana cike da damuwa, suma Hajiya da Alhaji haka suka kwana da damuwa a ransu, kowa ka gani zuciyarshi ba dad'i.
Washe gari Alhaji ya shirya zai fita ya gargad'i Hajiya akan zai tafi gidan yayarsa ya dawo, kafin bak'insu su k'araso, dan haka kada ta kuskura ta bar Intisar ta fita.
Bayan Alhaji ya tafi gidan yayarshi ba dad'ewa sai gasu sun dawo tare da ita yayar tashi. Suna dawowa ba dad'ewa kuma sai ga ango da waliyyansa, can jimawa kad'an sai ga malam liman ya k'araso wanda dama shi Alhaji ya shirya zai d'aurawa yaransa aure.
Duk wainar da ake toyawa sam Intisar bata sani ba, tunda ba fitowa take ba.
Ba tare da b'ata lokaci ba Aka fara gabatar da d'aurin aure, a dai-dai wannan lokacin ne Goga ya k'araso gidan sakamakon Shamsu da ya dameshi akan ya zo ya dubo mishi halin da Intisar ke ciki, da kuma alk'awarin da yaiwa ita kanta Intisar d'in na zuwa ya d'auketa ya kaita wajenshi.
Sai dai yana shigowa cikin gidan yai matuk'ar shan mamaki da kunnenshi ya jiyo mishi wai d'aurin auren Intisar za'a yi a dai-dai wannan lokacin.
Wayarshi ya ciro ya kira Intisar d'in, tana ganin kiranshi ta d'aga ta kara a kunne cikin sauri, ta ce, "Hello, Mubarak ka k'araso ne?" Goga ya ce, "Eh na k'araso Hajiya, amma dama yau ne d'aurin aurenki ashe amma shine sam bamu da labari?"
Cikin tsananin kad'uwa da matsanancin fad'uwar gaba ta mik'e a razane tare da fad'in "Mene! d'aurin auren wa ake! ban son shirme Mubarak." Goga ya ce, "Wallahi d'aurin aurenki za'a yi yanzu haka a harabar gidanku."
Intisar ta kurma ihu, sannan ta ce, "Na shiga uku! Cikin kuka ta ce, "Ba zan tab'a bari hakan ta faru ba, ba zan iya rayuwa da wani ba bayan Shamsu wallahi, dan Allah Mubarak ka taimakeni dan girman Allah."
Goga ya ce, "Ki fad'i koma menene Hajiya zan yi miki shi muddin bai fi k'arfina ba." Intisar ta ce, "Inason had'uwa da Shamsu yanzu," Goga ya ce, "To yanzu ya za'ai ki fito ba tare da kowa ya ganki ba?" Intisar ta ce, Ka yi sauri ka fita ka dawo da motarka ta bayan gidanmu yanzu, ni kuma zan san yanda zan yi na fito ta bayan gidan mu tafi."
Goga ya ce, "To shikenan ina jiranki," suna gama wayar cikin sauri Goga ya fito daga cikin gidan ya shiga motarshi ya ja ya kaita dai-dai inda Intisar d'in ta ce.
Intisar kuwa kayanta ta fara had'awa cikin sauri, ganin zasu b'ata mata lokaci ne har a gano shirinta yasa ta fasa d'ibar kayan, wayarta da jaka da takalmi ta d'auka, sai ta yafa mayafinta ta bud'e k'ofarta ta fita, cikin sa'a har ta fita bata had'u da kowa ba.
Tana fitowa Goga ya bud'e mata murfin mota ta shige da sauri ya bawa motar wuta suka bar unguwar.
Sai da suka yi nisa sannan ta samu damar saka takalmin da ta rik'o a hannu sai kallon Goga take tana cewa, "Maza k'ara gudun motar mu yi mu b'ace kar su gane bana nan a kamomu."
Bayan an d'aura aure, wasu daga cikin 'yan uwan ango suka ce a kira musu amarya su ganta, Alhaji da kanshi ya tashi ya shiga ciki, kai tsaye ya tafi d'akinta da niyyar ya rarrasota ta fito su gaisa, dan shi duk tunaninshi da an d'aura zai iya rarrashinta ta hak'ura da zab'inshi.
Yana shiga cikin d'akin ya tarar da d'akin a hargitse, sip d'inta a bud'e, ga jakarta itama a bud'e, sannan ga kayanta duk a barbatse a kan gado, kuma ba kowa a ciki, gabanshi ne ya fad'i, ya fara tunanin kar fa ya zo yarinyar nan guduwa ta yi. Nan ya lek'a bayi ba kowa cikin tashin hankali ya fito ya nufi d'akin Hajiya ya tambayeta ina Intisar nan ma bata nan, dan ta tabbatar mishi da cewa tana d'akinta bata fito ba har yanzu. 'Dakin Hindu ma haka bata ciki, a tak'aice sai da aka duba ko'ina na cikin gidan amma bata nan, d'akinta ya sake komawa ya duba k'ofar bayan gida ta cikin d'akinta ya ga k'ofar a bud'e, dawowa ya yi cikin d'akin nata yana kai kawo tare da tunanin mafita. Ya tunkari k'ofa zai fita kenan ya hango wata farar takarda, k'arasowa ya yi ya d'auka. Bud'ewa yayi ya fara karantawa kamar haka:
_Dad tunda ka k'i jin rok'ona a gareka shikenan, ni na zab'i in bar maka gidan._
Zufa ce ta fara keto mishi, yana tunanin yanzu abinda yarinyar nan zata yi mishi kenan, a fili ya fara magana cikin fushi ya ce, "Zaki sha mamakina Baby, wallahi muddin ba zaki bi zab'ina ba, to kema naki burin ba zai cika ba." Wayarshi ya lalibo ya kira abokinshi kwamishina ya sanar da shi cewa mai gadinshi ya gudun mishi da yarinya, nan kwamishina yace ya turo mishi da hotunansu tare da yi mishi alk'awarin cewa zai baza yara a ko'ina su kamosu.
Intisar kuwa basu dad'e ba suka isa k'ofar gidan su Goga, Shamsu yana kwance ya ji zuciyarshi tai wani irin bugu da k'arfi, ba shiri ya tashi zaune. A dai-dai wannan lokacin ne Intisar ta bud'e k'ofar mota ta shige cikin gidan a guje tana k'wala mishi kira, kamar a mafarki ya jiyo sautin muryarta.
Cikin sauri shima ya taso ya fito, a hanya sukai karo, tsayawa suka yi cak suna kallon juna, suna murmushi da farin cikin sake ganin junansu.
Can sai intisar ta fara kuka me had'e da dariya, a haka ta duk'e a gabanshi, shima duk'awan ya yi tare da mik'a mata hankici domin ta share hawayen fuskarta.
Intisar ta d'ago ta kalleshi ta ce, "Ka tashi mu gudu yanzu mu bar garin nan Jarumi." Shamsu ya zaro idanu, tare da fad'in, "Guduwa kuma, me yasa zamu gudu Intisar?" Intisar ta ce, "Shamsu mahaifina yana k'ok'arin d'auramin aure da wani a yau ba da kai ba, ni kuma ba zan iya juriyar rasaka ba gaskiya."
Shamsu ya zauna dirshan a k'asa saboda jin da yayi kamar jiri na shirin kwasheshi ya fad'i, hawaye ne ya fara wanke mishi fuska shima, ya kalleta ya ce, "Nima ba zan iya rayuwa da wata in ba ke ba, saboda ban tab'a sanin menene so ba sai a kanki, ban tab'a jina a matsayin dai-dai da kowa ba sai ta dalilinki, dan haka tunda rasa junanmu zai zama da cutuwa har mu iya rasa rayuwa to na amince da k'udurinki, tashi mu tafi.
Cikin sauri suka juya zasu fita daga gidan sun ma manta da wani wai shi Goga, Gogan ne ya ce," Hajiya, ku tsaya in kaiku tasha mana sai ku samu ku hau mota a can."
*πΈπ¦ZAMAN AMANA WRITERS*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)π€π€
*DOMIN SAMUN DUKKANIN LITATTAFANMU A FACEBOOK DA BAKANDAMIYA TSOFAFFI HARMA DA SABABBIN DON YI MANA LIKE DA COMMENT, GROUP 'DINMU NA FACEBOOK BIYU NE, DUK WANDA KA SHIGA ZAKA SAMU LITATTAFANMU A CIKI.*
ππππ
https://www.facebook.com/gidanzamanlpydaamana/
'Dakinshi ya shige yana huci, Intisar ta dad'e tsaye anan jikinta a sanyaye tana tunanin mafita, can sai ta yanke shawarar binshi domin tai mishi bayani. Tana zuwa ta tarar da shi zaune ya had'a kai da gwiwa, wanda ta san ga dukkan alamu kuka yake.
Kusa da shi ta je ta zauna, sannan ta sa hannu ta dafashi, cikin sauri ya d'ago da idanunshi wanda suka koma jajaye tare da ture hannunta, ya ce, "Me ya kawoki d'akina? Kuma ba na ce kar ki sake tab'ani ba?"
Intisar ta kalleshi ta ce, "A k'alla dai koda ba zaka yarda da ni ba ai ka saurareni ko Jarumina, kaine sanadin farin cikina, kai ka zamo min fitila. Kaifa shaida ne ka zama rayuwata, samunka shine cigaban da baya tab'a k'arewa. Kishi ya rufe maka idanu ka kasa fahimtar hak'ik'anin soyayyar da nake maka Jarumina, idan kana da hujjar cewa shimfid'ar fuska tana d'aya daga cikin alamu na bayyanar da so, meyasa ka kasa duba idanuna wad'anda sune hak'ik'anin abinda zasu bayyana maka waje da zuciyata ta karkata? Me yasa kake tunanin zan iya baiwa wani gurbi a cikin zuciyar da ta cika taf ta ko'ina da k'aunarka? A ina kake tunanin zan sashi tunda babu waje a cikinta?"
Shamsu yai mata wani kallo me d'auke da kin rainamin hankali ma, sannan ya ce, "Duk wannan dariyar da kulawar ta musamman da kika bashi shima ba so bane ko? Tunda nake da ke ban tab'a ganin irin dariyar da kikaita yiwa wancan k'aton gardin ba sai yau na gani ta sanadinshi, sannan ki zo ki rainamin hankali da batutuwanki, ki tashi kawai ki tafi ba zan tab'a yarda da maganganunki ba."
Intisar cikin damuwa ta kalleshi ta ce, "Dan Allah ka yarda da ni, a cikin raina muradinka ne kawai ya kewayeta, wannan da ka gani shine wanda Dad ke cewa zai had'ani da shi, kuma ni banma yi niyyar sauraronshi ba duk da Daddy ya ce kar na wulak'antashi. Abinda yasa kaga na zage munata hira muna dariya dan in rama abinda kaimin ne fa d'azu ba wai dan so ba, amma duk da ina dariyar wallahi hankalina baya gareshi, wasu abubuwan da yake cewa ma bana fahimta saboda dariyar kawai nake, fara'ata kawai yake gani amma zuciyata da natsuwata suna gareka. Nifa na riga na saka k'aunarka a raina, kuma komai wahala ban tab'a barinka."
Shamsu dai be ce mata komai ba dan har yanzu haushinta yake ji, Intisar kuwa hakan da ya yi ne yasa ta tabbatar da har yanzu be yarda da maganganunta bane, magana ta cigaba da yi kamar zata yi kuka, ta ce, "Yanzu me kake so na ce kuma, me kake so na yi don ka tabbatar da cewa kai kad'ai ne a cikin raina?" Shamsu ya juyo ya kalleta ya ce, "In kina so in yarda da ke to koda ya zo kada ki kuskura in sake ganin kin saurareshi, idan hakan ta sake faruwa kuwa to zan cigaba da kallonki a mayaudariya, kuma zan hak'ura da ke."
Intisar ta ce, "Ba ma zata kaimu ga haka ba, na yarda, ba zan sake sauraronshi ba, da inada lambarshi ma da na kirashi na ce kar ya sake zuwa inda nake." Shamsu ya ce, "A'a, barshi ya cigaba da zuwa, ko ba komai ya fuskanci irin matsayin da nake da shi a gidan nan, baki ga wata irin harara da kallon wulak'ancin da yaita watsomin ba, ni ban san me yasa kowane d'an kan uba da ya samu 'yar d'aukaka sai ya rik'a jin kanshi na hayak'i, yana ganin kamar ya mallaki duniya ne a tafin hannunshi, a rik'a kallon mutane wanda basu kaishi matsayi da d'aukaka ba a banzaye, ya manta cewa da samun da rashin da d'aukakar kanta duk a hannun ubangiji suke, ko wane irin lokaci yana iya sauya mutum." Intisar ta ce, "Yi hak'uri Jarumina, kada ka yi jam'i, wasu ne suke haka, amma akwai na kirki." Shamsu ya ce, "Amma su wa suka fi yawa?" Ta ce, masu wulak'ancin sun fi yawa gaskiya." Shamsu ya ce, "To kin gani, haka giyar kud'i take, tana da saka mutane girman kai da d'agawa, shi yasa ALLAH (S.W.A) ya ce, dukiya da 'ya'ya fitna ce, sai wanda Allah ya tsallakar, wanda ya ji tsoronsa da su gwargwadon iko, yai mishi d'a'a da su, kuma ya aikata alkhairi da su." Intisar ta ce, "Ta yaya?" Shamsu ya ce, "Masu tsoron Allah ne a cikin al'umma suke kiyaye dokokin Allah, idan Iyaye suka bi dokokin Allah to lallai sun kasance masu tsoronshi, kuma suma yaransu zasu taso da kiyaye dokar Allah, shine d'a'ar. Aikata alkhairi kuma shine wanda zasu yi har yaransu su gani su koya suma su rik'a yi, to wad'annan ne zasu sa ko duniya mutum ya samu a zai manta da wanda yai sanadin samuwarsu ba, haka kuma zaisa mutum ko yaran gari guda ya haifa ba zai yi sakaci da tarbiyarsu ba." Intisar ta ce, "Hakane, tabbas na lura duk abinda Allah ya baka walau dukiyar ko kuma talaucin to duk jarabawa ce, kai komai ma na duniyar nan jarabawa ne shi, hatta soyayyar nan tamu jarabawa ce, Allah ya bamu ikon tsabtaceta."
Shamsu ya harareta ya ce, "Ai ni naga jarabawa kam yau," Intisar tai dariya, ya harareta ya ce, "Allah ki daina dariya, da abinda nai tunani shine ya faru, ma'ana da ace da gaske yaudarata kika yi to da na gama yawo, dan shigowata d'akin nan har na fara tunanin fara bada wasiyya ne." Intisar ta b'ata rai, sannan ta ce, "Wasiyya kuma?" Shamsu ya ce, "Eh mana, ai wallahi kinji na rantse idan ba keba a so, to sai dai kawai a sa cigiyata a mak'abarta, domin tun da dad'ewa k'aunarki ta soke min zuciya, kinga kuwa goge raunin suka abune mara yiwuwa."
Intisar ta sake b'ata rai, tare da yin rau-rau zata yi kuka, ta kalleshi ta ce, "To yanzu dan Allah menene na maganar mutuwa ko aure bamu yi ba, wa ma ya ce maka zamu rabu?" Shamsu yai murmushi, sannan ya ce, "Yi hak'uri na daina, amma kema muddin zaki rik'a yimin irin wannan wasan to wallahi wata rana zaki iya tsayar da numfashina."
Intisar ta ce, "Ina sane nai maka irinshi dan ka ji yanda zuciya ke kasancewa idan abinda kake so ya d'auko hanyar rabuwa da kai, dan ni d'azu nasha guduwa kayi." Nan suka ci gaba da hirarsu cikin farin ciki da annashuwa har lokacin sallar azahar ya yi suka tashi, ita ta wuce cikin gida, shi kuma ya tafi d'auro alwala.
Intisar ta rigashi idarwa, tana yin addu'a ta fito domin komawa wajenshi sai ga Hajiya ta fito daga d'akinta, Hindu tana bayanta.
Hajiya ta kalleta ta ce, "Ina kuma zaki sake komawa? Ki zo ki zauna mu ci abinci tukunna. Intisar ta turo baki, sannan ta ce, "Bana jin yunwa na k'oshi." Tana gama fad'in haka sai ga sak'on Shamsu ya shigo, murmushi ta yi, dubawa tayi cikin sauri ta fara karantawa kamar haka:
_Kece komai kuma kece kowa sarauniyar mata, kece mallakin dukkanin zuciyata, rayuwata, da kuma kaina. Ki tabbata kin ci abinci kafin ki fito, nima ga nawa nan a gabana, amma wallahi in baki ci ba to nima haka zan zauna ban ci komai ba, kuma ko ruwa ban sha._
Tana gama karantawa sai ta maida mishi da amsa kamar haka:
_Ina muradinka masoyina, duk abinda ka ce haka za'a yi, ban tab'a sab'awa umurninka, in ka ga ban aikata ba to na mutu ne, amma kaima dan Allah ka ci yanzu, nima gani zanje na zauna na ci. Idan ma akwai wani abun da kake buk'ata bayan abincin to ka fad'amin, ni kuma a take zan kawo maka shi da kaina, ka kulamin da kanka._
Tana gama tura mishi ta taho wajen su Hajiya da saurinta, ta ce, "Mom mu je mu ci abincin," wucesu tayi ta rigasu isa wajen cin abinci ta zuba ta fara cin abinta, inda su kuma suka bita da idanu kawai, daga k'arshe suma suka k'arasa suka zazzauna suka fara cin nasu suma.
Bayan ta gama cin abincin sai ta tashi tare da kallon Hajiya ta ce, "Mummy, Sister Hindu, ni ina harabar gida," tana gama fad'in haka ta fice.
Tana fitowa ta hango Shamsu zaune yana jiran fitowarta. Ta tunkari wajenshi kenan ta hango Bala a wajen Habu, yana wanki suna hira, tsayawa tayi tana kallonsu tana tunani, wato gayun nan had'ewa Shamsu kai suka yi ko, wajensu ta nufa kai tsaye.
Tana zuwa tai sallama, suka amsa sannan suka gaisheta. Intisar ta kallesu ta ce, "Wai ku menene matsalarku ne? meyasa kowa kanshi ya fiye so ne? meyasa zaku had'ewa Shamsu kai ku daina zama inda yake? Ku da kunada tunani ai murna zaku yi abokinku ya kama zuciyata, kuma wallahi sanadin alak'arku da shi ne ma zaisa in cigaba da kyautata muku har ma in saka Daddyna shima ya kyautata muku. Amma wallahi cigaba da shareshi zaisa ku jawa kanku ku yi biyu babu, ba aikin kuma baku samu cigaban ba. Yanzu idan na koma ciki kai Bala ka zo ka karb'i dubu d'ayanka da ka tab'a ranta min, sannan akwai kud'in da na ware zan baku kai da Habun."
Sai a lokacin suka fara washe baki, cikin farin ciki suka yi mata godiya, tare da yi mata alk'awarin cewa ba zasu sake sauya mishi da komai ba. Intisar ta ce Idan ta tafi su je su shirya da abokinsu, suka amsa mata da to.
Wajen Shamsu ta nufa wanda yake zaune yana kallosu, tana k'arasawa ta zauna d'an nesa da shi, kallonta ya yi ya ce, "Me yasa kike son yin magana da fad'a ne? Ya kamata ki daina, duk wanda kike yiwa tsawa zaiga kamar saboda yana k'ark'ashinki ne yasa kike mishi haka, kuma magana me dad'i ma wallahi sadaka ce." Intisar ta ce, "Na daina insha Allah Jarumina." Shamsu ya kalleta ya ce, "Na gode nima da nake fad'a ake na'am da maganata Jarumata." Dukkansu suka yiwa juna murmushi.
Suna cikin hira ne aka fara k'wank'wasa gate, Shamsu ya tashi da sauri ya je ya bud'e, yana bud'ewa ya ga Goga ne shi da k'anninshi, shigowa suka yi dukkansu sannan Shamsu ya rufe k'ofar. Wajen Intisar suka k'arasa, Goga ya gaisheta, suma k'annenshi suka gaisheta, nan ya k'ara mata godiya ya ce dama abinda ya sake kawosu kenan su yi mata godiya.
Intisar ta ce mishi bakomai yiwa kai ne, Goga ya ce, "Ko zaki yi mana jagora in gaishe da Hajiya?" Kafin Intisar tai magana Shamsu yai saurin cewa, "Muje ni nai maka jagoran," Haka suka tafi Shamsu yana gaba su kuma suna bayanshi. Intisar ta bisu da kallo tana dariya da mamakin irin wannan kishin na Shamsu.
Basu dad'e ba a ciki suka fito suka yi musu sallama suka tafi.
Intisar ta kalli Shamsu ta ce, "Ka cika kishi." Shamsu ya ce, "To kin ga laifina? Ai kishi alama ne na gane k'aunar gaske."
Suna cikin magana sai ga Alhaji ya dawo. Cikin sauri yaje ya bud'e mishi gate, yana shigowa ya mayar ya rufe, ya dawo ya zauna nesa da Intisar d'in suka cigaba da hirarsu, dan tun yana d'ar-d'ar akan kar Alhaji yaita ganinsu tare yai mishi rashin mutunci har ya zo ya daina jin tsoron, tunda ya ga har yanzu Alhajin bai canza mishi da komai ba.
Alhaji yana gama fakin ya kashe motar ya fito. Kai tsaye wajensu ya nufo, yana k'arasowa wajensu ya ce, "Wato Baby Shamsu ya fara k'wacemin ke ko, wato yanzu har zan dawo ba zaki taso ki yi min oyoyo ba ko." Intisar ta ce, "Ba haka bane Daddy nah," nan suka yi mishi sannu da zuwa ya amsa cikin anashuwa sannan ya wuce cikin gida abunshi.
Yana shiga ciki ya tarar da Hajiya a Falo, zama yayi a kujera yana fad'in "Na gaji yau sosai." Hajiya ta ce, "Sannu da zuwa Alhaji, har ka dawo?" Alhaji ya ce, "Eh na dawo, na wuto mutuniyarki da abokin hirarta Shamsu suna ta hira, ban tab'a tunanin zasu shak'u haka ba balle har su zauna a inuwa d'aya." Hajiya ta ce, "Ai yanzu can ne wajen hirarta, kusan can take wuni yanzu."
Bayan Alhaji ya sake yin wanka ya ci abinci sai ya sake fita, a cewarshi dama wasu takardu ya dawo d'auka.
Yana tafiya ba dad'ewa sai suka k'ara jin wani hon d'in, cikin sauri Shamsu ya tashi ya je, yana lek'awa yaga ashe saurayin Intisar ne ya dawo, bud'e mishi k'ofar ya yi ya shigo.
Yana shigowa ya mayar ya rufe, sannan ya koma wajen Intisar ya zauna suka cigaba da hirarsu.
Shi kuwa saurayin Intisar me suna Nidal ya kame ne a mota shi a dole yana jiran tsammanin sake samun irin tarbar da ya samu jiya. Jin shirun yai yawa ne yasa ya fito daga cikin motan, abun mamaki, idanunshi ne suka hango mishi ita har yanzu wajen me gadi suna hira cikin nishad'i da kwanciyar hankali.
Cikin b'acin rai ya tunkari wajen, yana k'arasowa ya kalli Intisar yana nuna Shamsu da hannu ya ce, "Yanzu har kina da lokacin zama da wannan abun kina hira har da dariya? Kuma a kanshi har ki shanyani ina zaman jiranki tsawon lokaci, kada ki manta fa shi mai gadi ne." Ran Shamsu ne ya fara b'aci shima, ya kalli Nidal ya ce, "Ba zan baka amsa ba, ita da kanta zata sanar da kai ko ni wanene da kuma matsayina a wajenta."
Intisar ta kalli Nidal ta ce, "Nidal ko jiya albarkacinshi ka ci har ka ga hak'orana, in baka sani ba yanzu ka sani ni bani da sha'awar auren had'i, ga zab'ina nan zaune a gabana, dan haka ka je ka nemi sa'arka dan ni matar mai gadi nake." Nidal ya kalleta ya ce, "Ba laifinki bane, laifina ne da na zo inda kike har kike wulak'antani akan wannan matsiyacin, 'yar wahala kawai, duk ajinki da kyawunki, da iliminki amma ki k'are a soyayya da me gadi, 'yar wahala kawai." Mik'ewa Intisar tayi, ta d'aga hannu zata mareshi kenan sai Shamsu ya dakatar da ita, kallon Nidal Shamsu ya yi, ya ce, "Kada ka tab'a manta wannan a ranka, cewa matsiyaci kuma mai gadi ya kasaka, yai nasara a kanka, kuma ko ba komai yau ka k'ara d'aukar darasin cewa ba kowace buk'ata bace kud'i suke biya musamman ma a fagen so." Intisar ta ce, "Kana iya fice mana daga gida ko malam."
Cikin d'acin rai Nidal ya hau nunasu da yatsa yana huci, dan yama kasa cewa komai, daga k'arshe sai ya sauke hannun tare da tafiya wajen motarshi cikin sauri, Shamsu ya bud'e mishi gate, da gudu ya taho da motar kamar zai yo kan Shamsu d'in, yana fita Shamsu ya d'aga murya wajen fad'in, "Ka gaida gida."
Intisar ta k'araso wajen Shamsu tana fad'in, "Ba ruwana idan ya dawo ya baka kashi," Shamsu yai dariya, sannan ya ce, "Ai ke zaki shaida ko wanene masoyinki, ke bari fa kiji, kowa a fagen so sadauki ne kuma jarumi, sai dai in ba'a tab'o abin sonsa ba."
Intisar ta ce, "Har ka tunamin da wani wanda yaiwa 'yan fashi duka duk da yawansu kuwa saboda so da kishi, kuma abun ban dariya shine shi yake kai naushi kuma shine yake ihu da k'araji tamkar me ihun neman taimako. Shamsu yai dariya domin ya gane inda maganarta ta dosa, sannan ya ce, "Ai wallahi yanzu na riga da na fahimta yanzu na gane sai dake zan iya morar rayuwa." Intisar ta ce, "Kamar yanda nima yanzu a gareni ka zamo min kamar jini, kuma kai ka zamo min idanuwan ganina, dukkannin maza basu da k'warjini a wajena, kaine kad'ai ka samu karb'uwa, kuma wallahi duk wanda bai sonka to ni da shi bamuda sauran wata jituwa a rayuwa. Kai banma son had'a hanya da ni da shi, domin kuwa had'uwarmu da mak'iyinka Allah kad'ai ne masanin me zai faru a ranar. Ni fa a fagen sonka babu wanda zai iya sani in fad'i k'asa."
Shamsu yai musmurshin jin dad'i, sannan ya ce, "Na sadaukar da raina gareki, a kanki kad'ai zan iya rasa rayuwa."
Nidal ne zaune gaban mahaifinshi yana kora mishi bayanin duk abinda ya faru, in ran mahaifin Nidal yai dubu to ya b'aci. Wayarshi ya ciro a cikin aljihu ya lalibo lambar Alhaji ya kirashi, a dai-dai lokacin Alhaji yana hanyarshi ta dawowa gida bayan kammala gajeren meeting d'insu da ya koma wajen aikin suka tattauna.
Yana ganin kiran mahaifin Nidal ya d'aga tare da karawa a kunne da murmushi d'auke a kan fuskarshi. Alhaji yana yin sallama ya ji mahaifin Nidal ya ce, "Na ji abinda 'yarka taiwa d'ana Alhaji, kuma na gode, dan haka 'yarka koda ta goal ce to yarona ya hak'ura da ita, sai ka je ka aurawa mai gadin naka, wanda sanadinshi ne aka wulak'antamin d'a a kanshi." Kafin Alhaji ya tambayi ba'asi sai ya katse kiran.
Alhaji ya sake kiran lambar mahaifin Nidal d'in har wajen sau uku amma har ta katse ba'a d'agawa. Ajiye wayar ya yi cikin damuwa yana ta tunanin to menene ya faru haka a cikin ranshi, gudun motar ya k'ara, Allah-Allah yake kawai ya ganshi a gida domin ya ji abinda ke faruwa.
Yana k'arasowa yai hon Shamsu ya taso ya bud'e mishi gate tare da yi mishi sannu da zuwa amma sai be amsa mishi ba. Alhaji yana shiga yai fakin ya fito. Tsayawa ya yi daga bakin motar ya k'walawa Intisar kira, ya ce, "Ke Intisar, juyowa tayi, Alhaji ya ce zo ciki yanzu ina son magana da ke." Amsawa ta yi da, "To Daddy."
Yana gama fad'in haka ya shige ciki, yana shiga Hajiya ta fahimci yanayinshi akwai damuwa, ko zama bai yi ba, rai a b'ace ya fara faman kai kawo a falo. Wajenshi Hajiya ta k'araso tana tambayarshi lafiya, Alhaji ya kalleta ya ce, "Me Intisar taiwa yaron nan Nidal da yazo wajenta yau?" Hajiya ta ce, "Banda masaniyar komai Alhaji, banma san ya zo ba dan bai shigo nan ba."
Intisar kuwa Shamsu ta kalla ta ce, "Yi hak'uri bari in je, yanzu zan dawo." Shamsu ya ce, "To ba damuwa, ki zauna kawai ma yi waya." Intisar ta ce, 'A'a sai na dawo." Nan ta tashi ta tafi ta barshi yana tunanin yanayin da Alhaji ya dawo a ciki, wanda ko sannu da zuwanshi ma ya k'i amsa mishi yau.
Intisar na shiga falo mahaifinta ya tunkarota yana fad'in "Me kikaiwa Nidal d'an Alhaji Ridwan yau da yazo wajenki?" Intisar ta ce, "Dad ba abinda nai mishi, kawai gaskiya na fad'a mishi cewa bana muradinshi Shamsu nake muradi."
Hannu Alhaji ya sa ya d'auketa da mari, sannan ya nunata da yatsa ya ce, "Ke kin yi kad'an ki zama sanadin yankewar alak'armu da Alhaji Ridwan, kuma baki da miji sai Nidal, shi kuma Shamsu d'in tunda na gano daga wajenshi matsalar take yau ba sai gobe ba zan d'auki mataki a kanshi."
Yana gama fad'in haka ya fito waje Intisar ta biyoshi domin ganin me zai aikata. Yana zuwa wajen Shamsu ya ci kwalar rigar Shamsu ya watsa shi gefe Shamsu ya fad'i k'asa, sannan ya kalleshi tare da nunashi da yatsa ya ce, "Ka tattara komatsanka ka bar min gidana yanzu tunda ba gidan ubanka bane," Shamsu cikin jin zafin kalamanshi ya mik'e, sannan ya kalleshi ya ce, "Zan tafi, tunda kamar yanda ka ce tabbas ba gidan ubana bane, amma ka sani dan na bar gidanka ba wai yana nufin na bar zuciyar 'yarka bane, kuma dan na bar aikin gadi a k'ark'ashinka ba shi zaisa na rasa kowane irin aiki ba, dan haka zan tafi kamar yanda ka buk'ata." Yana gama fad'in haka ya shiga d'aki ya kwaso kayanshi ya fito.
Yana fitowa Intisar ta rik'e rigarshi tana kuka tana fad'in, dan Allah kada ka tafi ka barni Jarumina." Cikin k'arfin hali Shamsu ya ce, "Ya zama wajibi na tafi Intisar tunda har mahaifinki ya nemi hakan, amma ki sani cewa hakan ba yana nufin mun rabu ba kenan na tabbatar miki da hakan." Alhaji ya zo gaban Shamsu ya jawo rigarshi Intisar kuma ta jawo rigar Alhaji, sai ya zama shi yana jan Shamsu ya fitar da shi ita kuma tana jan rigar mahaifinta dan ta dakatar da shi. A haka sukaita jan juna har k'arfin Alhaji ya rinjayi na Intisar d'in har ya samu ya turashi waje ya maida k'ofa ya rufe, sannan ya ja hannun Intisar tana kuka tana turjiya har suka shiga cikin falo. Duk wannan abubuwan da ke faruwa a kan idanun su bala ya faru.
Suna shiga cikin falo ya jefata kan kujera, sannan ya nunata da yatsa ya ce, "Babu ke ba Shamsu daga yau," Intisar ta ce, "Ni kuma wallahi ba zan tab'a son wani bayan Shamsu ba, zuciyata shi kad'ai take muradi."
Hajiya ta fara yiwa Intisar magana cikin tsawa ta ce, "Ke Intisar kanki d'aya kuwa? Mahaifinki kike fad'awa irin wad'annan maganganun?"
Alhaji ya kalli Hajiya ya ce, "Rabu da ita, ya juyo ya kalli Intisar ya cigaba da cewa, tunda abun naki Iskanci ne, ni kuma zan tabbatar miki da cewa ni ubanki ne, kuma dole sai da amincewata ko wani nawa sannan zaki yi aure."
Wani ihu da kuka Intisar ta saki, sannan ta tashi da gudu ta shige cikin d'akinta ta kulle.
_Topha, ko yaya wannan badak'alar zata kaya? Mu had'u ni da ku a shafin gaba domin jin abubuwan da zasu wakana, Ina sonku masoyana_
*πΈπ¦ZAMAN AMANA WRITERS*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)π€π€
*DOMIN SAMUN DUKKANIN LITATTAFANMU A FACEBOOK DA BAKANDAMIYA TSOFAFFI HARMA DA SABABBIN DON YI MANA LIKE DA COMMENT, GROUP 'DINMU NA FACEBOOK BIYU NE, DUK WANDA KA SHIGA ZAKA SAMU LITATTAFANMU A CIKI.*
ππππ
https://www.facebook.com/gidanzamanlpydaamana/
Farin cikin da ke kan fuskar iyayenta da 'yar uwarta ne a hankali ya gushe gabad'aya, saboda ganin yanda ta tashi hankalinta lokaci d'aya daga jin zancen aure. Intisar ce ta cigaba da magana a hassale, ta ce, "Haba Dad! Duk k'aunar da kake min yau ina ta tafi? Ashe zaka iya yanke hukunci ba tare da ka tuntub'i ra'ayina ba?"
Alhaji ya tashi ya rik'o Intisar ya zaunar da ita sannan shima ya zauna. Kallonta ya yi, sannan ya ce, "Kwantar da hankalinki Baby, kamar yanda kika sani ne ba zan tab'a zab'ar miki abinda zai cutar da ke da kuma rayuwarki ba, hasalima sai da na zab'o miki wanda nake da tabbaci akan zai yi dai-dai da rayuwarki, kuma wanda ya dace da ke. Kamar yanda ba zan iya had'aki da wanda zai cutar min da ke ba, to haka ma ba zan tab'a aura miki wanda bakya so ba. Ganin bakya kula kowa yasa nai tunanin bakida wanda kike k'auna a cikin ranki, dan haka ki kwantar da hankalinki, ba zan tab'a hanaki zab'inki ba, amma dan Allah Baby koda ya zo kada ki k'i sauraronshi, duk yawan maneman 'ya mace cikinsu bata san waye zata aura ba sai wanda Allah ya zab'a mata, nafi so a hankali in ma rabuwar ne a rabu lafiya, koda ya zo goben kar ki wulak'antashi, in samu wannan alfarmar daga gareki kinji."
Intisar ta numfasa, sannan ta kalli mahaifinta ta ce, "Ba zan wulak'antashi ba kamar yanda ka nema daga gareni Dad, amma wallahi bana jin zuciyata zata yi muradin wani mahaluk'i a duniya bayan wanda ya mallaketa a yanzu kuma har yake da ikon sarrfata ta yanda ya so, ta kalli Alhaji ido cikin ido ta cigaba da cewa, Ba amfanin b'oye maka Dad, wallahi shi kad'ai zuciyata ke muradi." Tana gama fad'in haka ta tashi ta fita daga d'akin jikinta a sanyaye, kai tsaye wajen Shamsu ta nufa. Su kuwa su Alhaji dukkansu binta suka yi da idanu har ta fita daga cikin d'akin, sannan cikin sauri Alhaji ya juyo da sauri ya kalli Hajiya ya ce, "Hajiya wa take so ne, ba dai aljanin take nufi ba?" Hajiya ta kalleshi ta ce, "Nima binda nake tunani kenan Alhaji, amma banda abinka in ba shi ba tun dawowarta wa kaga tana saurara?"
Alhaji ya ce, "Muna murna ta warke ashe d'an iskan yana nan manne da ita." Hindu ta ce, "Daddy ance fa in ana maganarsu suna ji." Alhaji ya rufe baki da hannu yana zare idanu ya ce, "Hakane my luv, bari nai shiru, tashi ki je ki dubata kiga tana ina ne, kar ya zo mu muna nan tai wani wajen bamu sani ba tunda abun ya juyo," Hindu ta amsa mishi da "To," sannan ta tashi ta fita.
Intisar kuwa tana tunkaro inda Shamsu yake ya lura da ita jikinta a sanyaye yake, tana k'arasowa wajenshi ta zauna, yana kallonta ya fuskanci damuwa k'arara a kan fuskarta.
Shamsu ya kalleta ya ce, "Fad'amin?" Intisar ta kalleshi a sanyaye ta ce, "Me zan fad'a maka?" Shamsu ya ce, "Dalilan da yasa damuwa, k'unci, da kuma b'acin rai suka ziyartomin kan wannan kyakkyawar fuskar."
Jikinshi ta fad'a tana kuka, can sai kuma ta tuna da nasihar da yai mata akan rab'o jikinshi, hakan yasa tai saurin tashi, sannan ta ce mishi ya yi hak'uri.
Shamsu jin kukanta yake sosai a k'wak'walwarshi. Tasowa yayi ya tsugunna a gabanta, ya kalleta ya ce, "Intisar d'ago ki kalleni." 'Dagowa ta yi a hankali tana kallonshi kamar yanda ya ce, Shamsu ya ce, "Kinsan ya masoyi ke kasancewa idan ya ga damuwa har da kuka a wajen masoyinsa?" Intisar ta girgiza kai alamar a'a. Ya ce, "Kin tab'a ganin zuciyar masoya a yayin da suka kasance cikin damuwa, ko kuma d'aya daga cikinsu ya kasance a cikin irin halin da kike ciki a yanzu?" Nan ma ta girgiza kai ta ce a'a. Shamsu ya ce, "To da ace kina gani wallahi na tabbatar wannan kukan da ba zaki yi ba, saboda damuwar taki ce amma ni na fiki jin rad'ad'inta, hakan ne yasa gobara ta kunnu a cikin zuciyata wadda ke bakya iya ganinta ni kad'ai ke jin rad'ad'inta da zafin k'unarta a cikin zuciyata da jikina, kuma ba zan tab'a samun sassauci ba a cikinta har sai kin daina kuka kin sanar da ni damuwarki."
Jin abinda ya ce ne ya sa ta tsaida kukan, sannan cikin sauri ta sa hannayenta ta fara share hawaye. Shamsu yai murmushi, sannan ya ce, "Ko ke fa, ashe gimbiyar tawa tana son zaman lafiyar zuciyata," Murmushi ta d'an yi. Tashi ya yi daga gabanta ya samu waje ya zauna, Shamsu ya kalleta ya ce, "To yanzu sanar da ni abinda ya sameki?"
Intisar ta d'an b'ata rai, cikin damuwa tare da turo baki ta ce, "Ba Daddy bane ya sani kuka, magana fa yake akan abinda zai datse alak'ar da ke tsakaninmu, wai ya yi min miji fa yake cewa."
Cikin kad'uwa Shamsu ya mik'e tsaye da sauri yana kallonta, Gabanshi ne yai mugun fad'uwa sakamakon jin bak'on al'amarin da Intisar ke sanar da shi. Gaskiya hankalinshi yai matuka'ar tashi, duk da dama yasan wutsiyar rak'umi tai nesa da k'asa, dama yasan da wuya a mallaka mishi Intisar matsayin mata.
A sanyaye ya koma ya zauna yana jujjuya maganar Intisar a cikin zuciyarshi, natsuwarshi yake k'ok'arin tattarowa domin ya danne nashi damuwar, ko dan ya samu damar rarrashin Intisar d'in, dan yasan zata fishi shiga damuwa. Kallonta ya yi ya ce, "Ki kwantar da hankalinki Jarumata, ina da tabbaci akan irin k'aunar da Alhaji yake miki, wannan kad'ai ya isa zama hujja akan cewa ba zai tab'a yi miki auren dole ba, a yanda na lura ma ya fi k'aunarki fiye da Hindu, idan kuwa har haka ne, to ba zai tab'a baki wanda bakya so ba, dan haka ki saki ranki dan Allah, kin san fa lafiyarki lafiyata ce, haka ma damuwarki damuwata ce."
Intisar tai murmushi, sannan ta ce, "Gaskiya nayi sa'ar miji mai sauri wajen koremin dukkanin damuwa, gaskiya duk macen da ta rasa namiji irinka to tana ruwa tsamo-tsamo." Dariya kalmarta ta k'arshe ta bashi, sanadin haka ya sa ya dara itama tana tayashi. Shamsu ya kalleta ya ce, lokacin sallah ya yi, ya kamata ki tashi ki je kiyi nima na samu na yi." Intisar ta ce, "Ka bari kawai sai anjima sai mu had'a da Magriba." Shamsu ya b'ata rai, sannan ya ce, "Wato ashe da gaske ne sakacin da kike da sallah har ya kai haka ko, to ki sani itace abu na farko da ake fara duba inganci da kyawunta cikin ayyuka, bayan wannan ma yin sallah akan lokaci da yinta kamar yanda addininmu ya koyar da mu to yana saka farin ciki a zuciya, yana saka ni'ima tsabtatacciya cikin jiki da rayuwa, sannan yana saka haske da annuri a fuskar mutum, haka ma gab'ob'inka idan ka mutu su ke haska maka k'abarinka Intisar ibada itace rayuwarmu, domin albarkacinta ne muke raye a duniya, kuma yinta shi ke sawa Allah ya so mutum, idan kuma ya soka to alamu ne na ya yarda da kai da ayyukanka, idan kuma hakan ta kasance to sai kiga ya saka soyayyarka a cikin zuciyar mutane, kuma wannan soyayyar bata tab'a gushewa saboda komai dominsa kayi shiyasa shima ya zama silar karb'uwarka, kuma yake inganta soyayyarka a cikin zuciyar mutane, duk abinda kika ga an yishi ya gushe to dama ba domin mahalicci aka ginashi ba, dan haka falalar ibadu sunada yawa wallahi, ba lada kad'ai suke wanzarwa ba, har da ingantacciyar wayuwa, da kuma kyakkyawar mu'amala da mutane, dan haka tun wuri kiyi k'ok'ari ki ga kin daidaita tsakaninki da mahaliccinki, kuma kiyta istigfari, azumi da nafila saboda sakacin da kika yi a baya." Intisar ta ce, "insha Allah zan gyara daga yau bama sai gobe ba, nagode sosai da tunatarwarka Jarumina, a da idan aka yi min gyara haushi nake ji har nai sababi akai, amma sai a yanzu nake ganin amfanin tunatarwa a cikin rayuwa, tabbas kaine mutum na farko da ka samu kaina a wannan b'angaren, na k'ara tabbatarwa tabbas kasancewarmu da kai had'ine na ubangiji, nagode sosai da k'ok'arin inganta rayuwata da kuma lahirata da kake Jarumina."
Shamsu ya ce, "Ba komai, duk abinda nai a kanki sanadin k'auna ne, kije kiyi sallahr idan kin idar ki aikomin da wayata dan Allah." Intisar ta ce, "Ai zan dawo, saboda akwai tambayoyin da suke buk'atar amsa daga gareni, Allah ya kamaka, sai ka fad'a min ta yanda akai kake samun labarin komai game da ni," tana gama fad'in haka ta tashi ta tafi, Shamsu ya bita da kallo yana murmushi har ta shige ciki, sannan shima ya tashi ya tafi yin alwala domin gabatar da sallah.
Bayan ya idar da sallah a dai-dai lokacin ne aka aiko musu da abinci, ya ci nashi. Intisar kuwa, bayan ta shiga cikin gida kai tsaye d'akinta ta wuce ta yi alwala sannan ta fito ta saka hijabi ta shimfid'a dadduma ta tayar da sallah, tana idarwa ta yi addu'a sannan ta tashi ta nannad'e daddumar, wani farin ciki take jin yana ziyartar zuciyarta bayan idar da sallar, lallai ta k'ara gazgata maganar Shamsu tunda gashi yanzu ta tsinci kanta a ciki, istigfari take k'ara yi akan sakacin da tayi akan ibadunta na baya, amma yanzu ta d'auki d'ammarar gyarawa.
Bayan ta idar ta sauko k'asa, tana shirin shiga b'angaren Daddynsu ne sai ta hangosu a dining zasu ci abinci. Wajen ta tunkara tana fad'in, "Wato yanzu ko nemana bakwa yi ko." Hajiya ta ce, "Mun san inda kike ne ai, shiyasa kika ganmu hankalinmu kwance." Intisar ta ce, "To in da gaske ne kun san inda nake ku fad'amin ina na je?" Alhaji ya kalleta ya ce, "Kina wajen abokinki mai gadi mana," Intisar ta kalli Alhaji, suna had'a idanu ya murgud'a mata baki. Murmushi tayi, sannan ta tashi ta je kusa da shi ta zauna, ta ce, "Dad me nayi kuma ake wurgomin harara daga nesa?" Alhaji ya ce, "Gani nayi mai gadi yana shirin k'wace min 'ya." Intisar tai dariya, Hindu ta ce, "Wato kishi kake kenan ko Dad?" Ashe in tai aure kishi zaka yi da mijin." Dukkansu suka yi dariya, sannan Intisar ta ce, "Ai babu wanda ya isa k'wace matsayinka wajena Dad balle har ya k'waceni duka daga gareka, Shamsu yana da kirki ne sosai, kuma ina k'aruwa ta fannin addini, wallahi in ka zauna da shi ba zaka tab'a tunanin d'an k'auye ba ne." Alhaji yai murmushin jin dad'i, ya ce, "Masha Allah, ina farin ciki da duk wanda zai dasa farin ciki a cikin zuciyar yarana," Daga nan suka zuba abinci suka fara ci, bayan sun gama kowa ya kama gabanshi. Intisar kuwa tana tashi ta shiga d'aki ta duba wayoyin nan taga dukkansu sun cika, ta cire a caji ta saka d'aya a cikin kwali tare da d'aukar sabon guda d'aya, cikin leda ta saka sannan ta ajiye a gefe. 'Dayar ta d'auka ta saka d'ayan layin a ciki sannan ta kunnata, tashi ta yi ta d'auki ta cikin ledar ta fito falo, ganin ba kowa yasa kai tsaye ta fita ta nufi wajen Shamsu.
Tana fitowa ta hango Shamsu d'in ya tunkari wajen zamansa inda ya tarar da Bala zaune shi da Habu. Da sallamarshi ya k'arasa, Habu ne kawai ya amsa. Yana zama Bala ya yunk'ura zai tashi, Shamsu ya rik'e mishi riga yana fad'in, "Wai Bala wannan wace irin k'iyayya ce a yanzu kake gwadamin, dan Allah me nai maka ne haka a rayuwa?" Bala ya bige hannun Shamsu wanda ya rik'eshi da shi, ya juyo sannan ya nunashi da yatsa ya ce, "Kar ka sake shiga harkata, babu abinda ya shafeka da rayuwata, ka yi harkarka nai tawa."
Ya juya zai tafi ne idanunshi sukai arba da Intisar wadda ta ga komai kuma ta ji komai duk a kan idanunta. Cikin b'acin rai ta kalli Bala ta ce, "Kai Bala ka san matsayin wannan mutumin da kake rainawa wayau a wajena kuwa?" Shamsu ya ce, "Ranki ya dad'e................." Dakatar da shi ta yi da hannu, ta cigaba da magana da Bala tana cewa, "Wallahi billahil azeem a kanshi zaka iya rasa aikinka, a kan me yana lallab'aka kai kuma kake k'ok'arin gasa mishi magana, me yai maka zaka rik'a kyararshi sama ta ka? Baka san hassada tana tauye ayyukan mutum ba, kuma baka san wanda ake yiwa ita kullum Allah sawa yake yana k'ara yin sama ba? To bari ka ji, hassada bata tab'a sawa ka samu ka kai matsayin da kake burin kaiwa a rayuwa wallahi, ka yi k'ok'arin gyara rayuwarka sai ka ga bud'i ta wata hanyar da bakai tsammani ba kaima, in baka sani ba to yanzu ka sani kai abinda kake yi mawa shi Shamsu kwata-kwata basa gabanshi, ka duba ka ga waya na siya, amma na rasa ta yaya zanyi in sa ya karb'a ba tare da rayukanmu sun b'aci ba, amma tunda kud'i kake so to ka yi k'ok'ari ka sashi ya karb'a ni kuma zan biyaka dubu d'ari. Daga k'arshe ina baka shawara akan kada ka kuskura ka yi sakacin rabuwa da mutum irin Shamsu dan wallahi suna da matuk'ar wuyar samu irinsu, bayan haka duk na sake kamaka kana wulak'antamin shi to wallahi sai ka bar aiki a ranar."
Daga haka bata sake cewa komai ba ta zauna a gefen benci cikin b'acin rai, shima Bala ya wuce fuuuuu ba tare da ya ce komai b, Habu shima ya tashi ya tafi wajen wanki, dama wankin yake ya tsaya hutawa bayan sun ci abinci.
Shamsu ya kalleta yanda ya ga ta b'ata rai tai kicin-kicin da rai ne ya sashi yin murmushi, ya ce, "To saki ran mana Jarumata, na riga da na fahimci matsalarsa, damuwarshi shine na zo daga sama na samu damar da su basu samu ba, kiy mishi uzuri," a haka dai ya lallab'ata ya samu ta sauko.
Intisar ta mik'a mishi ledar hannunta, ba tare da ya karb'a ba ya ce, "Menene wannan?" Intisar ta ce, "Ka karb'a ka bud'e mana ka gani." Karb'a yayi ya bud'e yana dubawa, cikin sauri ya d'ago kai tare da bud'e baki zai yi magana, da sauri ta katseshi, ta ce, "Dan girman Allah kada kai musu, akwai kyautatawa tsakanin masoya, to ka karb'i wannan kyautar tawa a matsayin kyautar so."
Shamsu ya ce, "Shikenan, na gode, Allah saka da aklhairi, amma daga yau kada ki sake," cikin farin ciki ta ce, "To kawu Shamsu." Bud'e wayar ta yi ta saka mishi sim d'in da ta siyo musu tare wanda kusan iri d'aya ne, lamba d'aya ce ta bambantasu, bayan ta saka ta kunna ta fara nunnuna mishi yanda zai yi amfani da ita. Bayan ta gama nuna mishi sai suka shiga batu akan abinda ya shafi addini, nan yaita mata tambayoyi, abun mamaki akan alwala kad'ai saida ya ci gyaranta sau ba adadi.
Nan ya samo ruwa ya shiga fahimtar da ita yanda zatai alwala, sannan ya nuna mata yanda zata yi sallah, daga k'arshe ya k'ara mata da nasihohi.
Bayan sun gama ya kalleta ya ce, "Ya kamata ki shiga gida, tunda kin dad'e a nan kada a zo a nemeki." Intisar ta b'ata rai, sannan ta ce, "Korata ma kake kenan ko?" Shamsu ya ce, "Wane ni in kori gwanar da tafi iya yak'ar zuciyar Shamsu, kawai dai ina tsoro ne kada cigaba da kallonki a gabana yasa in kasa aiwatar da aikina yanda ya dace, kina gani dai d'azu sanadinki nai jinkirin bud'ewa Alhaji k'ofa."
Intisar tai murmushi, sannan ta ce, "Zuciyata tana yin rauni a duk lokacin da zan nisanta da kai, ko kad'an bana so nai nisa da kai." Shamsu yai murmushi, sannan ya ce, "Kar ki damu, ai ga waya zamu cigaba da kasancewa tare, kuma zaki koyamin goagle domin mu rik'a yin brosin ni da ke." Intisar ta kece da wata irin dariya, sai da tayi mai isarta sannan ta kalleshi ta ce, "Zan koya maka yanda ake yin typing domin mu rik'a yin chating zaka ce." Shamsu ya ce, "Eh haka nake nufi," dukkansu suka sa dariya, daga nan suka yi sallama Intisar ta tashi ta shiga cikin gida.
Haka suka kasance da juna a waya, sallah kad'ai ke rabasu, hatta abinci sai sun danni ransu suke tsayawa su kulashi, har dare suna tare a waya sai da bacci ya fara cin k'arfinsu sannan suka hak'ura suka yi sallama da juna shima ba dan ransu ya so ba.
Da asuba wayar Shamsu ne ta tayar da Intisar, dan dama ya fad'a mata cewa ta bar wayarta a kunne, saboda alk'awarin da ya d'aukarwa kanshi na tashinta sallar asuba kullum. Bayan ta yi sallah ta idar bai barta ta koma ba ya sata ta yi mishi karatun Qur'ani amma abun ban takaicin bayan fatiha sai fakak'i da nasi kad'ai ta rik'e suma akwai tarin kuskure a ciki, sauran kuma ta ce mishi ta manta saboda bata muraji'a.
Wannan ne yasa kawai ya ce ta yi addu'o'i sai ta koma ta kwanta. Tana gama yin addu'a kuwa ta sake shemewa.
Sau biyu ana turo Hindu ta duba ko Intisar ta tashi, amma duk ta zo sai ta tarar tana sharar bacci. Wajen sha biyu ta farka cik less

Sau biyu ana turo Hindu ta duba ko Intisar ta tashi, amma duk ta zo sai ta tarar tana sharar bacci. Wajen sha biyu ta farka cikin sauri ta tashi tai wanka sannan bayan ta fito ta shirya ta fito falo neman abun karyawa.
A falo ta tarar da mahaifiyarta, bayan ta zauna kusa da ita suka gaisa, itama Hindu ta gaisheta, sannan ta ce ta d'an kawo mata abun karyawarta nan.
Tana kawo mata ta fara ci, tana cikin ci ne ta ji karar sako ya shigo cikin wayarta, dubawa ta yi, tana karantawa tana zuba uban murmushi, Hajiya kuwa na aikin binta da idanu.
Ita kuwa Intisar bata ma san tana kallonta ba, Cigaba da sake karanta sak'on Shamsu take kamar haka:
_Jiya na kwanta bacci sai nai mafarki mun yi aure da na farka na duba sai naga babu ke, yau kuma da na wayi gari tsawon wannan lokacin ban ganki ba sai naga kina yimin gizo a cikin idanuna, a yanzu kuma sautin muryarki ce naketa jiyowa kina kirana, maza-maza ki hanzarta lek'owa na ganki kafin k'aunarki ta d'imautani har a rasa gane kaina._
Dariya take sosai na jin dad'i, Hajiya ta kalleta ta ce, "Waike ke da wa ki ke wannan dariyar ne." Intisar ta ce, "Ba kowa Mom," bata wani ci abincin kirki ba amma ta tsame hannunta ta ce ta k'oshi.
Mik'ewa tayi, ta kalli Hajiya ta ce, "Mum bari na je wajen Shamsu na dawo," Hajiya ta ce, "To karki dad'e dai, kinsan zakiy bak'o yau, kiy saurin dawowa domin kisa a shirya mishi abinda ya dace." Intisar ta d'an yatsuna fuska, sannan ta ce, "Ba sai na zo ba, a shirya mishi koma menene kawai." Tana gama fad'in haka ta fice.
Tana fitowa a dai-dai Shamsu shima ya taho bakin gate d'in, yana hangota ya b'oye inda ba zata ganshi ba, Intisar kuwa ganin baya bakin gate yasa bata k'arasa wajen ba, kai tsaye sai ta wuce d'akinshi, tana dubawa d'akin taga baya ciki, fitowa tayi ta hau duba ko'ina shi kuwa yana hangota yana dariya, can sai yaga ta d'aga wayarta zata kira yai maza ya sata a silent. Tana kira tai ta ringing ba'a d'agaba har ta katse, sak'o ta tura mishi kamar haka:
_Na duba ko'ina naga ba kowa, kafin na kai ga rasa tunanina dan Allah ka bayyanamin kanka Jarumina._
Sak'on yana shigowa ya duba, cikin sauri ya fito, ya doso inda take tsaye. Ta bayanta ya taho, yana k'arasowa ta ji an ce "Keee." Juyowa tayi tana kallonshi yana mata dariya, numfashi ta sauke tare da dafe saitin zuciyarta, sannan ta dafe goshinta cike da takaici tana kallonshi ta ce, "Wallahi nasha guduwa ka yi, shiyasa na kasa samun natsuwa, har ina shirin fara yin kuka. Shamsu wai shin me yasa na damu ne a kanka? Wannan itace amsar da na kasa ganowa har yanzu."
Shamsu yai murmushi, sannan ya ce, "Me zaisa in gudu na barki bayan nasan cewa a yanzu farin cikina a cikin wannan gidan kad'ai yake, Jarumata had'uwar zuciyoyin mutum biyu sanadin k'auna yakan sa kaji komai, ciki kuwa har da jin zaka iya mutuwa domin wanda kake k'auna, mu k'arasa wajen zamanmu ko?" Intisar ta kalleshi, kallo me had'e da harara, ta ce, "Ban hak'ura ba fa, ka ci bashi, zan rama kuma."
Dariya yai mata, suka k'arasa wajen zamansu suka zauna, suna zama bak'onta yana isowa, Shamsu ya bud'e mishi mota, ita kuma Intisar ta sak'a a ranta cewa zata baiwa bak'onta kulawa ko dan ta rama abinda Shamsu yai mata domin ya gane cewa ba kowane irin wasa bane zuciya ke iya jurewa, akwai wasan da ke sata ta tarwatse lokaci guda.
Ko kafin Shamsu ya rufe gate ya dawo Intisar ta tashi cikin sauri da tsananin farin ciki ta nufi motar wannan bak'on nata.
Tana ganin gayen da aka zab'a mata taji ta tsaneshi, amma sam bata nuna mishi ba, haka ta daure tai mishi sannu da zuwa, ya amsa, sannan ya kalleta ya ce, "Mu k'arasa ciki ko?" Intisar ta ce, "Ai ka bari mu gaisa tukunna ko?" Ya ce, "Eh hakane kuma, to shigo daga ciki mana, dan kyakkyawar yarinya kamarki bai dace ta tsaya a tsaye haka ba."
Intisar ta shiga ciki ta zauna.
Da gayya ta biye mishi sunata hira suna shewa, Shamsu kuwa duk abinda ke faruwa idanunshi na kai.
A sanyaye ya koma wajen zamanshi ya zauna yana ta kallonsu. Fitowa yaga sun yi suka jera suka shige cikin gidan farin ciki bayyane a kan fuskarsu, har suka shige ba tare da Intisar ta k'ara koda kallon inda Shamsu yake ba.
In ran Shamsu yai dubu to ya b'aci, hankalinshi ya tashi, ba irin tunanin da bai yi ba, tunani yake wato dama yarinyar nan yaudararshi take ba son gaskiya take mishi ba, wata zuciyar ta ce mishi ramuwa take so dama ta yi, banda abinka dama kamar Intisar ce zata k'ask'antar da kanta akan kula irinka, ire-iren wad'annan tunanin ne suka addabi zuciyarshi.
Sai wajen biyu saura har ya je yai sallah ya dawo, aka kawo abinci ya dauka ya kai d'aki ya ajiye, sannan ya fito ya zauna zuciyarshi na tafasa, yana mai nadamar saurin amincewa da soyayyar Intisar.
Yana zama sai gasu sun fito, dariyarsu ce ta ankarar da Shamsu fitowarsu, kallonsu yake, suna jingine a jikin mota abinsu, sun dad'e suna tattaunawa, sannan daga k'arshe suka yi sallama Intisar har da bud'e mishi mota ya shiga, Shamsu ya tashi a sanyaye ya bud'e mishi gate d'in, bak'on Intisar ya fice ya tafi.
Yana tafiya Intisar ta tunkaro inda Shamsu yake ta zauna, mik'ewa Shamsu ya yi zai bar wajen ta rik'o hannunshi, fizgewa yayi tare da juyowa, yanda ta ga sauyawar launin idanunshi ne ya sata ta firgita, sake rik'e hannunshi ta yi da niyyar rarrashinsa, ya sake fizgewa tare da wanketa da mari, ya nuna mata yatsa, ya ce, "Kada ki k'ara kulani, macuciya azzaluma, dama ni nai mamakin son da kike min, son farad d'aya, duk da irin matsayinki, ashe d'aukar fansa kike son yi. To tunda kin d'auka ki kama gabanki," Intisar da ke dafe da kumatu ta ce, "Dan Allah ka saurareni," Cikin kuka ya ce, "Ba abinda zaki fad'amin bayan wanda na gani da idanuna, mayaudariya kawai. Yana gama fad'in haka ya shige d'aki abinshi ya barta nan tsaye, cike da da na sanin abinda ta yi.
_Hahahaha masu k'udurin ramuwa a soyayya sai a kiyaye, ba akan ko wacce ake samun nasara ba yasin._π
*πΈπ¦ZAMAN AMANA WRITERS*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)π€π€
*DOMIN SAMUN DUKKANIN LITATTAFANMU A FACEBOOK DA BAKANDAMIYA TSOFAFFI HARMA DA SABABBIN DON YI MANA LIKE DA COMMENT, GROUP 'DINMU NA FACEBOOK BIYU NE, DUK WANDA KA SHIGA ZAKA SAMU LITATTAFANMU A CIKI.*
ππππ
https://www.facebook.com/gidanzamanlpydaamana/
*ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMEEN, A KOWANE IRIN YANAYI GODIYA A GAREKA ITACE FARKO YA MAHALICCINA. YA ALLAH INA GODIYA DA NI'IMAR DA KAIMIN, DUK WATA NASARA DA RASHINTA DUK DAGA GAREKA NE, NAGODE DA NASARORIN DA NA SAMU SANADINKA YA MAHALICCINA, INA K'ARA GODIYA DA RAHMARKA A KAINA, YA ALLAH INA ROK'ONKA KA CIGABA DA JIB'INTAR LAMURANA.πππππ*
*MASOYANA KUN ZAMA MIN JAGORA, YA ALLAH KA ZAMA GATANMU NI DA ABABEN ALFAHARINA MASOYAN GASKE, A KO'INA KUKE INA ALFAHARI DAKUπππππππ*
SHAFI NA SHA UKU
Tana zuwa tasha cikin sa'a ta samu motar da zata kaita k'auyen su Shamsu d'in, kuma cikin ikon Allah saura mutum d'aya tak dama suke jira a samu su tafi.
Shiga tayi ta zauna, Direba ya ce, "Yauwa mota ta cika, ina Direban yake ya zo ya ja ku tafi." Tafiya ya yi nemo Direban dan ya zo su tafi.
Kamar an ce Intisar ta d'ago kanta ta kalli wanda ke kusa da ita, mamaki ne k'arara bayyane a fuskarta na ganin Shamsu zaune a kusa da ita ya duk'ar da kai hannunshi dafe da goshinsa.
Fitowa tayi daga cikin motar, sannan cikin takaici ta kamo hannunshi ta jawoshi da k'arfi, kawai jin an jawoshi yasa ya d'ago kai, wadda ya gani a wajen ce ya sashi zaro idanu. Ba musu ya bita suka fito daga cikin motar, Tashar suka fito, Intisar ta tari adaidaita sahu ta fad'a mishi inda zai kaisu, shiga ciki suka yi suka zauna sannan suka fara tafiya.
Intisar ta kalleshi inda tai sa'a shima ita yake kallo, harareshi tayi, ta ce, "Dena kallona. Kana tunanin duk inda ka shiga ba zan iya zuwa in bincikoka ba? To ka sani duk inda ka je sai na dawo da kai, domin na rama abinda kai min." Shamsu ya kalleta ya ce, "Ranki ya dad'e sakarmin hannuna, Intisar ta ce, "Ba zan saki ba, salon in sakeka ka sake guduwa ko?" Sake rik'e hannun tayi tamau sai kace wani d'an k'aramin yaron da ake gudun in aka sakeshi zai b'ace.
Kallonta yake yana mamakin hali irin nata, tana abubuwa sai kace ba mace ba, shi sam ya rasa ina ajinta da tak'amarta suka tafi, kuma ya rasa dalilan da yasa take bibiyarshi, amma tunda ta ce ramuwa zata yi to ya k'udurta a ranshi ba zai sake guduwa ba har sai ta gama ramuwarta a kanshi. Da wannan tunanin nashi ne suka k'araso har k'ofar gidan. Me napep ya ajiyesu, fitowa sukayi ta cewa me napep d'in yai hak'uri ta shiga ta karb'o mishi kud'inshi, ya ce mata ba damuwa.
Suna shiga ciki suka tarar da Habu da Bala zaune a kan benci suna tattaunawa a kan maganar Shamsu, suna ganinsu Shamsu cikin sauri su Habu suka tunkarosu suna fad'in "Alhamdulillah gasu nan ma sun dawo," Intisar ta kalli Bala ta ce, "akwai dubu d'aya a wajenka?" Bala ya ce, "Eh ranki ya dad'e." Intisar ta ce, "Ka je ka bawa me adaidaita sahun da ke k'ofar gida yana jira, ka bashi duka dubu d'ayan, anjima sai kazo ka karb'a." "Bala ya ce, "An gama ranki ya dad'e."
Duk wannan bayanin da take har yanzu ta k'i sakarwa Shamsu hannu, tana gama magana ta jashi suka nufi d'akinshi, ciki ta shiga da shi, sannan ta sakar mishi hannu. Nunashi da yatsa tayi, ta ce, "Karka kuskura ka sake guduwa wallahi, ka jira ka ji abinda zan fad'a maka tukun, in banda iskanci ma kana fama da raunuka zaka kama hanya kace zaka gudu, ko idan kaje gidan naku me zaka ce musu yasa ka gudo oho," tana gama fad'in haka ta fice daga d'akin ta nufi cikin gida.
Tana shiga falo dukkaninsu suka mik'e suna binta da kallo, cikin sauri Alhaji ya taso ya k'araso wajenta ya rik'ota yana fad'in, "Babynah ina kika je? Kin san irin tashin hankalin da muka shiga kuwa?" Intisar tai murmushi, sannan ta ce, "Dad bafa inda naje, na je na dawo da Shamsu ne." Dukkaninsu cike da mamaki suka had'a baki wajen fad'in, "Shamsu kuma."
Intisar ta ce, "Eh, ai na fad'a muku ba zan tab'a k'yaleshi ya tafi haka kawai ba har sai na rama abinda yai min." Alhaji yai murmushi, sannan ya ce, "Shikenan jeki ki karya abunki Babynah, idan kin gama kiyi wanka ki kwanta ki huta, idan na dawo anjima zan ji irin laifin da yai miki da kuma irin hukuncin da kika tanadar mishi kinji." Intisar ta ce, "To Dad," sai da ta shiga d'akinta tai brush sannan ta sake fitowa. Dining ta wuce kai tsaye ta zauna ta fara cin abinci.
Yayarshi ce wadda take zaune take kallon ikon Allah akan wainar da taga ana toyawa a cikin gidan nan. Kallon Alhaji tayi bayan Intisar ta bar wajen ta ce, "Gaskiya Tajudden ya kamata kai karatun ta nutsu, Intisar fa yanzu ba yarinya bace, a wad'annan shekarun nata yanzu kamata yayi ace tana d'akin mijinta."
Alhaji yai murmushi, sannan ya ce, "Insha Allah zata yi da zarar ta samu wanda yai mata, dan bana so in basu wanda basa so." Ta kalleshi cikin takaici ta ce, "Nima ba nufina kai mata auren dole ba ai, amma taya zaka gane tanada gwani ko babu tunda baka tab'a jin ta bakinta ba?" Kafin Alhaji yai magana Hajiya ta ce, "Maganarki gaskiya ce Yaya, ya kamata mu aurar da Intisar, saboda yanzu shekarunta kusan talatin har da d'aya." Alhaji ya ce, "Insha Allah zata yi aure Yaya, amma yanzu sai mun gama tabbatar da ingancin lafiyarta tukun, bari na tafi wajen aiki yau na makara saboda wannan abun da ya faru." Sallama yai musu, sannan ya fice daga d'akin.
Yana fita ta kalli Hajiya ta ce, "Ni bansan me yasa Tajuddeen ya tsani ai maganar yarinyar nan ba, da an fara sai ya gudu, yarinya ko yaushe sai jin kanta take kamar 'yar jaririya saboda sangarcin da take samu daga gareku musamman ma dai shi. Tunda ku kun kasa saitata ta fahimci rayuwa sosai ai sai ku bari tai aure a hankali shi mijin ya karantar da ita komai game da zamantakewarsu da ma ta rayuwar baki d'aya."
Hajiya ta ce, "Gaskiya ne maganarki, Nima yau ban ji dad'in yanda ya kasa d'aukar mataki akan abinda Intisar tai mana ba, duk da dai muna tunanin ba yin kanta bane wad'annan abubuwan da take. amma duk da haka ya ci ace zuwa yanzu muna tsawatar mata koda cikin hikima ne, amma shi Alhaji sam baya son yaga b'acin ran yaranshi, shiyasa yake mallaka musu duk abinda suke so koda kuwa shi baya so a ranshi, ni kaina abun ya fara damuna, na fara tunani akan rayuwarta ta gaba."
Ita kuwa Intisar tana gama cin abincinta ta zo ta wuce ta gabansu ta haye sama tana hararar Yayar Alhaji a fakaice ba tare da ta gani ba, dan in akwai wadda bata son gani to bata wuce wannan 'yar uwar mahaifin nasu ba, ta lura da ita sosai sam bata k'aunarta, kullum sai ta soketa a wajen mahaifinsu. Wanka tayi ta shirya cikin k'ananan kaya riga da wando, yau haka kawai taji su ranta yake sha'awar sawa. Tana sawa ta kalli kanta a madubi tana murmushin jin dad'in yanda tai kyau. Sak'on Shamsu ta tuno wanda ya fara turo mata akan kayan da tasa irin wad'annan ranar da ta fita.
_Kin koma namiji sak._
Nan da nan sai taji kuma kayan sun fita ranta, cirewa tayi ta saka doguwar riga, wanda dama yanzu yawanci sune kayanta. Bayan ta gama shiryawa tai kwanciyarta.
Sai da taji tafiyar yayar Alhaji ne sannan ta sauko k'asa, tana fitowa falon ta tarar da ba kowa, ficewa tayi daga d'akin.
'Dakin Shamsu ta nufa, Bala da Habu suna hangota suka fara tsegumi, Bala ya ce, "Ikon Allah, nikam ina shan mamaki, mai ji da kai da kuma ji da giyar dukiya da iko yau itace ta koma bin talakanta, talakan ma wanda ya fi kowanne a ciki talauci." Habu ya ce, "Kai dai bari, ni kaina wallahi mamaki abun yake bani, kuma sam Shamsu bai yi kama da masu yin asiri ba balle muce asiri yai mata." Suna ganin ta kusa zuwa kusa da su yasa sukai sauri wajen sauya hirarsu.
Har ta kai dai-dai k'ofar d'akin sai ta fasa ta nufo inda su Bala suke, tana zuwa suka gaisheta ta amsa, kallon Bala tayi ta ce, "Bala ka kiramin abokinka ya sameni a lambu yanzun nan."
Bala ya ce, "An gama ranki ya dad'e, amma ranki ya dad'e ina tunin dubu d'ayana da kika ranta d'azu." juyawa tayi tana fad'in, "Zan ba Shamsu ya kawo maka." Tana gama fad'in haka ta bar wajen, shi kuma Bala ya tafi d'akin Shamsu domin isar da sak'on Intisar.
Da sallamarshi ya shiga d'akin, Shamsu ya amsa, fuska a d'aure Bala ya kalleshi ya ce, "Intisar tana kiranka," Shamsu ya ce, "Tana ina?" Bala ya amsa mishi a tak'aice, "Cikin lambu," juyawa yayi zai bar d'akin.
Shamsu ya ce, "Bala wai me nai maka ne duk ka bi ka canzamin?" Bala ba tare da ya juyo ba ya ce, "Ai yanzu ka fi k'arfina Shamsu, kai da kake soyayya da 'yar masu gida, ai sai dai a kiraka da shugaba kaima," yana gama fad'in haka yai ficewarshi, sai a lokacin ya fahimci cewa lallai Bala yana kishi ne ko kuma bak'in ciki da cigabansa, a fili yai magana ya ce, "Bala kenan, in ka kwantar da hankalinka ni sam d'abi'un Intisar basu yi min ba, koda ma auren zanyi ba irinta zan aura ba, mtssss banda ma abun mutane daga ganin tana d'an kulawa dani sai suyi tunanin soyayya ce, karen mahaukata ne ya cijeta zata fad'a sona har takai ga ta zab'eni matsayin mijin aure." Duk shi kad'ai yake wannan surutun a d'aki, tashi yayi ya saka doguwar rigarshi ya fita, kai tsaye ya doshi lambu inda Intisar ke zaman jiranshi.
Tun daga nesa ya hangota, itama hanyar da zai b'ullo kawai take kallo, wani irin bugu zuciyarshi take mishi har ya k'araso wajenta bata daina ba.
'Dan rissinawa yayi da kanshi, ya ce, "Gani ranki ya dad'e." Intisar ta nuna mishi irin kujerar da ta zauna wadda ke kusa da ita ta ce, "Zauna a nan." Ba musu ya zauna, kallonshi tayi na wajen minti biyar, shi kuwa tana fara kallonshi sai yai sauri ya sunkuyar da kai, be san meyasa ba sam baya iya dad'ewa yana kallonta saboda ji yake adadin bugawar zuciyarshi na nunkuwa. Intisar ta ce, "Meyasa kaketa k'ok'arin guduwa bayan ban hukuntaka ba, kuma ban ce na yafe maka ba?"
Shamsu kanshi yana k'asa ya ce, "Kiyi hak'uri, ai gani kin dawo da ni, kuma nai alk'awarin ba zan sake guduwa ba har sai kin min duk irin hukuncin da kike so."
Intisar ta kalleshi ta ce, "Da kyau, dama hukuncin na kiraka nan in yi maka, zan iya yafe maka kamar yanda ka nema a cikin wasik'arka, amma da sharad'i." Shamsu ya ce, "Ki fad'i ko menene sharad'inki a kaina zan yi na'am dashi komai tsaurinshi muddin zaki yafemin." Intisar ta ce, "Sai ka d'ago ka kalleni zan fad'a maka sharad'in, kuma koda zaka sauke fuskarka sai ka bari har sai na gama sanar da kai tukunna, saboda inaso na fahimci yanayin da fuskarka zata kasance a ciki yayin da zaka ji sharad'ina." Shamsu ya d'ago fuskarshi ya kalleta, ya ce, "Ina saurarenki."
Intisar ta kalleshi ido cikin ido ta ce, "Sai ka amince zaka mallakamin zuciyarka, sannan kuma kaimin alk'awarin zaka aureni, wannan shine................."
Wata irin razana yayi wadda ta sakashi tib'owa daga kan kujerar da yake zaune a kai. A duk'en da yake ne a k'asa ya d'ago da kanshi yana kallonta ya ce, "Ranki ya dad'e Shamsu ne fa a gabanki ba wani ba." Intisar ta ce, "Na san da wanda nake magana sarai, kuma nasan kasan na fahimci da kai nake."
Mik'ewa tayi tsaye, tai tattaki har i'zuwa gabanshi, tsugunnawa tayi kusa da shi, fuskarta daf kusa da tashi, kama hannunshi tayi ta rik'e, sannan ta ce, "Da soyayya ce ake gina k'auna, kamar yanda kaima kayi amfani da ita wajen gina taka a cikin zuciyata. Haka kuma da hak'uri ne ake son juna, kamar yanda nai hak'uri ban d'auki mataki a kanka ba nai jinkiri har na fara sonka, kuma kaima kayi hak'uri a lokacin da naita cin zarafinka kana jurewa. Sannan da shak'uwa ne ake canzawa masoyi suna. Kamar yanda nima sanadin dad'ad'an kalamanka ne ya sakani na shak'u da kai, har na sauya maka suna nake kiranka da Jarumina."
Shamsu cikin rawar murya ya kalleta ya ce, "Ranki ya dad'e hannuna," Intisar ta ce, "Ai ba game da hannunka na kiraka nan ba, fad'amin zaka yi wanne ka zab'a a cikin sharud'aina, eh ko a'a?" Shamsu ya kalleta ya ce, "Ni fa ranki ya dad'e soyayyar da na nuna miki ta wasa ce, ta ramuwa ce kawai. Amma ina ni ina yin soyayya da ke, ko na amince sam amincewata bata da amfani, saboda iyayenki ba zasu tab'a amincewa ba.
Hannunshi ta saki, sannan ta mik'e tsaye, hannunta dafe da goshi, ya lura da ita sosai dafe goshi ya zamar mata jiki a duk lokacin da taji haushin wani abu. Cike da takaici ta d'ago kai tana kallonshi tana nunashi da hannu ta ce, "Wai Kai duk da binka da kasa naita yi kamar wata motsatstsiya har rayuwata nasa a hatsari domin taka rayuwar duk bai maka ba, har sai ka tsaya kana b'atamin lokaci wajen samun amincewarka? Ina ruwanka da amincewar iyayena? Sanin kanka ne duk abinda nake muradi shi nake samu a wajensu. Kai wai saima na tsaya ina yi maka wani bayani ko magiya? To bari kaji magana d'aya, kaine kai mini kutse cikin manhajar zuciyata, har ka koyamin yanda zan k'aunaceka, dan haka a yanzu zuciyata ta karb'i duk wani sak'o naka, dan haka bana ma buk'atar ka yarda, domin kuwa amincewarka ba shine me amfani ba, nawa amincewar shine muhimmi, ko kana so ko baka so to ni naso kuma inaso, kuma ka sani wallahi tun ina yarinya har girmana bansan wani abu wai shi rashi ba. Haka kuma bansan babu ba. Ban tab'a neman abu na rasa ba, Kuma kaima wallahi sai na sameka. Magana ta k'arshe shine ina muradinka, kuma dole ka amince, fak'at magana ta k'are." Tana gama fad'in haka ta tashi ta fara tafiya, waigowa tayi ta kalleshi wanda shima ita yake kallo. Kashe mishi ido d'aya tayi, sannan ta ce, "Jarumina d'an saurayi sai ka zo tad'i anjima, zan d'and'asa ado na kece raini, zan jiraka, kuma in baka zo ba ko, hum sai na shek'eka. Tana gama fad'in haka ta juya tai tafiyarta.
_Wannan fa shine soyayya dole. Naga inda ake wannan mulkin mallakar, masoyana dan Allah ku tayani jin k'arfin hali, ku tayani ganin ikon Allah, yo an tab'a yin haka, shi yace soyayyar wasa yayi ta ramuwa kawai, ita tace sai anyi ta gaske kuma ta dole.πππππ Ke kuwa Intisar ina ajinmu na mata da aka san matan hausawa da girmamashi, naki a cikin wace loka kika b'oyeshiπ€π€π€π€π€ La ta kasa bani amsa, ai shikenan ta b'arar. masoya ku taho mu zauna mu jeru kawai muita salatiπππππ_
BILKISU ZAKARI BK
*ππππππππππ
ππππππππ
*BA ZAKU GA DAI-DAI BA*
ππππππππππ
ππππππππ
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (π ±οΈK)*
SADAUKARWA GA:
*πΈπ¦ZAMAN AMANA WRITERS*
*AISHAN UMMA*
*NI'IMATULLAH*
*UMMU J*
*HAFSAT RUHAZ*
*HAUWA LAWAL*
*BILKISU Z. YA'U (π ±οΈK)*
*πΈπ¦ZAMAN AMANA WRITERS*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)π€π€
*DOMIN SAMUN DUKKANIN LITATTAFANMU A FACEBOOK DA BAKANDAMIYA TSOFAFFI HARMA DA SABABBIN DON YI MANA LIKE DA COMMENT, GROUP 'DINMU NA FACEBOOK BIYU NE, DUK WANDA KA SHIGA ZAKA SAMU LITATTAFANMU A CIKI.*
ππππ
https://www.facebook.com/gidanzamanlpydaamana/
https://bakandamiya.com/group/111/zaman-amana-writers-association
https://facebook.com/groups/171841133699012/
LITATTAFAN MARUBUCIYAR:
1 *RAYUWATA TAKI CE*
2 *KA CUTAR DA NI!*
3 *NA'KASASHSHE MA MUTUM NE*
4 *LAIFIN WAYE?*
5 *LAIFIN WAYE SABON SALO*
6 *SO MAHA'DIN RAYUWA*
7 *ZUCIYAR MUGU!*
8 *ME KE FARUWA?*
9 *LABARIN FATIMA*
10 *NA BAKI RAYUWATA*
11 *AURE*
12 *A SANADIN 'KAUNA*
13 *TASKU!!*
14 *RAYUWAR RAYAM*
LOADING.................BA ZAKU GA DAI-DAI BA.
SHAFI NA SHA BIYAR
_Kai tsaye kamfanin mahaifinki na sake komawa, ina zuwa nai sa'a na tarar yana nan, sai dai da k'yar ya amince zai ganni shima sai bayan ya gama sallamar jerin mutanen da suke gabana. A haka nai hak'uri na zauna domin gani nake ba wajen da zan iya samun taimakon bayan nan d'in. Bayan ya gama sallamarsu aka bani dama na shiga, ina bud'e k'ofa ya d'ago kai ya kalleni ba tare da ko sallamata na samu ya amsa ba, ya ce, "Yauwa malam Mubarak, dama ko baka dawo ba a yau ni zan nemeka?" Na duk'a har k'asa ina kuka na ce, "Alhaji dan girman Allah taimako nazo nema ka taimaka min, ka bani kud'i dubu d'ari da hamsin in kai asibiti mahaifina ke kwance rai a hannun Allah, kuma sam sun k'i tab'ashi, idan na fara aiki ranar monday a hankali sai aita cirewa a albashina." Goga ya d'ago kai ya kalli Intisar ya ce, "A lokacin mahaifinki maimakon ya taimakamin sai ma na tarar da wani tashin hankalin. bayan na gama fad'awa Alhaji sai yai murmushi, sannan ya ce, "Bawan Allah kaine d'azu kazo da takardunka fa nace zan k'ara dubawa. A yanzu koda lokacin albashi yayi ba lallai bane ma'aikatan ciki ma su samu albashinsu a dai-dai wannan watan, balle kai da ko fara aikin ma baka yi ba, kuma daga cikinku akwai mayaudara masu karb'ar kud'i bashi farkon fara aikinsu daga k'arshe sai su gudu. Dan haka ni baka isa ka damfareni ba." Magiya naita mishi ina kuka ina kama k'afarshi, amma a maimakon ya tausayamin sai ma haushi da na bashi, ina nan tsugunne inata faman rok'onshi kawai sai ga wani abokin Alhajin ya shigo shi da d'anshi. Bayan sun gaisa ina nan tsugunne a gabana ina kallo aka d'auki matsayin da aka bani aka baiwa wannan d'an abokin nashi. Bayan tafiyarsu ya kira security ta waya ya ce, su zo Office d'inshi, suna shigowa ya wurgomin file d'ina ya ce dama abinda yake so ya kirani ya fad'amin kenan, bayan ya d'aukeni aiki d'an abokinshi ya nuna yanada buk'ata ya bashi, dan haka in je in nemi aikin a wani wajen dan ya lura banda cikakken hankali ba zai d'aukeni aiki ba yazo yaita tafka asara. Haka suka d'aukeni ina kuka ina mishi magiya a haka suka yi waje da ni. A haka na koma asibiti, ina komawa na tarar da gawar mahaifina ya mutu, sanadin haka ita kuma mahaifiyata ciwonta na hawan jini yai mugun tashi sanadin mutuwar tasa, hakan yasa ta maye gurbin gadon da aka kwantar da shi. Ko kafin a had'a gawar mahaifina in tafi da ita gida a sanar da 'yan uwa da abokan arzik'i a sallaci gawar tasa a lokacin jikin mahaifiyata itama ya tsananta, ni tasa aka kira mata, ta bani wasiyyar in kula da k'annaina kada na bari rayuwarsu ta tagayyar, kuma inyi hak'uri da rayuwa in cigaba da nema, mai nema yana tare da samu. Har ta cika abu biyu take maimaitawa, "Allah ya jik'an mahaifinku, munyi zama na amana dashi bai tab'a b'atamin ba. Sai kuma ta cigaba da fad'in, Mubarak tunanina shine zan tafi in barka da yaran nan bansan waye zai cigaba da kula da komai nasu ba har da makarantarsu, dan Allah kaine babba ka kula da k'anninka, dan Allah ka rik'e zumunci da 'yan uwanka har abada, Allah yai muku albarka yasa ku gama da duniya lafiya." Tana gama fad'in haka tai kalmar shahada itama ta ce ga garinku nan. A ranar naga tashin hankali naji d'aci wanda ban tab'a jin irinshi ba, ni banmsa san inda kaina yake ba sai daga baya na farfad'o, ashe doguwar suma nayi. Haka muka tattara muka koma da gawa biyu gida akai musu sallah aka kaisu makwancinsu._
Tsagaitawa yayi da magana sakamakon kukan da ya ci k'arfinshi. Sai da yai mai isarsa Intisar na tayashi sannan ta kalleshi ta ce, "Lallai ka yi babban rashi, rashin uwa da uba a babu rashin da ya kaishi ciwo, kuma duk a rana d'aya. Amma ka yi hak'uri, Allah ya ji k'ansu ya gafarta musu." Bayan ya amsa mata da ameen sai ya cigaba da bata labari.
_To da yake rasuwa ce muna samun taimako na sadakar abinci daga wajen mutane shiyasa bamu rasa na kaiwa baki ba sai bayan an yi arba'in. Daga nan ne na cigaba da fita nema ina kawowa k'annaina, nasha kawowa su ci ni bana samun komai kuma a haka zan wuni in kwana washe gari in sake fita nema a haka, nan da nan na lalace na rame, ga rashin samun isashshen bacci, kullum in dare yayi kwana nake ina tunani ta yaya zan samu abinda zan kawo gida gobe, a haka kullum rayuwata ta cigaba da kasancewa. Ana haka kwatsam wata rana ina d'aki ina tunani sai na kunna rediona, kawai sai naji ana sanarwar wai yanzu haka ana kan gudanar da taron da Alhaji Tajudden ya shirya na baiwa marayu tallafi, ina jin haka na tashi cikin sauri na fita na doshi wajen domin nima na samowa 'yan'uwana, sai dai abun mamaki ina zuwa na tarar da ashe Babanki ne Alhaji Tajudeen d'in, a wajen ga tarin 'yan jarida sai d'aukarshi hoto ake, duk wadda ya baiwa sai an musu hoto. kafin kice me sai gashi labari ya shiga duniya an baza a ko'ina gidan Telebijin, da gidan redio, da jaridu, hatta a social media. Wai ya baiwa marayu kud'i naira million hamsin, kuma ya d'auki nauyin karatun wasu daga cikin talakawa mutum hamsin. Ina dosar wajen da niyyar nima inje a bani nawa tallafin sai aka dakatar da ni, wai ya gama d'ibar adadin wad'anda zai taimaka mawa. Sai da nai bincike na gane cewa daga cikin mutum hamsin d'in nan da zai d'auki nauyin karatunsu duk mawadata ne wad'anda suke da rufin asirinsu, kuma yawancinsu ma she duk yaran abokansa ne da na 'yan uwansa, duk da haka ban sare ba. Ganin wannan abun ne yasa na samo lambarshi nai mishi sallama a whatsapp ya amsamin har muka gaisa. Sai na rok'eshi akan ya taimakamin nima maraya ne, kuma ga k'annai an barmin masu yawa ni ke kula da komai nasu, nace mishi ni bama so nake ya taimakamin da wani abu ba, aiki nakeso ya taimakamin wanda kullum zanyi a biyani. Haka naita rok'onshi kullum amma sai dai ya hau ya karanta ya share, ko sau d'aya be sake min magana ba tun bayan sallamar da ya amsamin da gaisawar da mukai. Yana jin buk'atata sai be sake kulani ba. Ban gaji ba har tsawon wata d'aya ina mishi magiya, hakan yasa na hak'ura bayan na faffad'a mishi maganganu sanadin b'acin rai sai nayi blocking d'insa, daga k'arshe na fad'a mishi cewa duk abinda yai mini zai ga sakamako. Wata rana na tafi shagon aski zan rage sumar fuskata saje da kuma gemun da ta taru sosai ta maidani kamar mahaukaci, kawai sai naga ana gabatar da wani shiri, ana cikin yi sai naga an nuno wajen masu garkuwa da mutane, da yanda suke yi ma su yi garkuwa da mutanen, nan da nan sai zuciyata ta bani cewa nima me zai hana in had'a mutane kawai in fara wannan harkar tunda itace me kawo kud'i cikin k'ank'anin lokaci. Ba tare da na sha wahala ba na samu mutane ciki harda abokaina wad'anda suke cikin halin tsaka mai wuya muka had'a kai. Da gidan wannan d'an luwad'in muka fara, muka k'wamushe d'ansa wanda yake matuk'ar k'auna, sai da ya bamu Million Goma muka sako mishi d'anshi, a tsakaninmu muka raba kud'in wanda ni da su na samu na aurar da k'annaina guda biyun nan, daga nan sai na fara harin gidan mahaifinki, na dad'e ina neman dama a kanku ban samu ba sai a wannan lokacin, kuma niyyata idan mahaifinki ya zo wajen nan jiya in karb'i kud'in in kasheshi, kamar yanda yai sanadin da na rasa iyayena. Ku kuma sai in barku ku tafi, sai akai rashin sa'a lak'waye sukai ram da mu." D.P.O yai caraf ya ce, "kai ka shiga hankalinka wallahi, mune lak'wayen?" Goga ya ce, "Yi hak'uri yallab'ai labari ne ya taho da sunan fa. Kallon Intisar yayi wadda take ta faman kuka saboda tausayi ya ce, "Ranki ya dad'e wannan shine labarina da dalilin da yasa na shiga wannan harkar, da kuma dalilin da yasa kika ji na zagi mahaifinki, amma dan Allah a yafemin ba zan sake aikata hakan ba, dama ba halina bane rayuwa ce ta maidani haka."_
Intisar ta goge hawayenta bayan ta gama cin kukanta, Shamsu shima hawayen fuskarshi ya goge, kallon mahaifinta ta fara yi wanda kanshi yake k'asa jikinshi duk yai sanyi shima, sannan ta maida kallonta kan Goga ta ce, "Hak'ik'a an yi maka rashin kyautawa, kuma mu ya cancanta da mu baka hak'uri ba kai ba, ta kalli Dadynta ta ce Dad, a labarin nan da Goga ya bayar na fahimci wasu abubuwa, ire-irenku suna da yawa a yanzu wallahi, wad'anda suke yin taimako ba dan Allah ba sai domin duniya ta gani, su yi suna, su d'aukaka a ko'ina, kuma mutanen duniya su yaba musu, Dad kun mance cewa shi suna da d'aukaka na duniya duk mai gushewa ne? amma d'aukakar da ka ginata akan hanyar Allah da koyarwar ma'aiki to wallahi bata gushewa kuma ita ce wadda kake samun d'aukakar lahira da ita. Dad ka manta k'issar karuwar da ta shayar da kare ruwa sanadin haka tai dace da aljanna? Allah yafi farin ciki da taimakon da kaiwa wanda yake mak'ura na buk'atar taimako, shi talaka mabuk'aci tamkar wanda ya fad'a ruwan teku ne ruwan yana gab da shanyeshi hannunshi kawai ake iya hangowa, sai ka mik'a mishi hannu ya fito. kaga kuwa duk wanda ya jawoshi baida masoyin da ya kaishi balle har ya zartashi. to haka talaka yake wanda baida yanda zaiyi kullum, amma a maimakon ku rik'a lalibo irinsu kuna taimaka musu sai ku je kuna taimakon masu shi domin neman suna, shiyasa da yawansu tunani da damuwa ke halaka su, to yanzu bama wannan kad'ai ba, sanadin ire-irenku masu kud'i, sanadin rashin tausayawarku da rashin yin taimako a inda ya dace sai na d'aukaka kad'ai da kuka iya ya jawo mutane da dama suna shiga muguwar rayuwa, suna zama 'yan garkuwa da mutane. Dad wannan yak'in ba na gwamnati bane ita kad'ai wallahi har da ku masu kud'i kunada kamasho. Sai kaga mai kud'i ya tara ya jibge amma ya bar mak'wabtanshi suna kukan yunwa, wai ace taimako ma yanzu sai ka zab'a, a yanzu in masu kud'i basu san mutum ba ma basa taimaka mishi, iya wad'anda suka sani kad'ai ke cin arzik'insu. Yanzu Daddt kaga halin da ka jefa wannan bawan Allahn, kuma wallahi duk abinda ya aikata kaima kanada kamasho, dan haka Dad dan Allah kai da masu irin halinka ku ji tsoron Allah ku daina. ji fa yanda kake bamu kud'i a banza muna facaka da su, amma kana gani talakawa na wahala kana kasa taimaka musu, to ku iyayenmu kuja yin haka taya muma zamu tashi da tausayin talakawa balle har mu yi k'ok'arin taimakawa rayuwarsu? Ji irin wulak'ancin da nake yiwa 'yan aikin gidanmu Dad. bama mu kad'ai ba, duk masu kud'in da suke yiwa talakawa haka to yaransu ma ba zasu tashi da tusayi ba sam. Daddy dukiyarka ba tamu bace mu kad'ai, kuma ka sani ba mu bane iyalinka kad'ai, duk musulmai iyalai ne kuma suna da damar da suka cancanci ka taimaka musu ba sai mu kad'ai ba, kwanaki naji wani hadisi da Shamsu yake karantowa Bala akan cewa "Musulmi d'an uwan musulmi ne, kuma sashensu yana k'arfafa sashe, dan giman Allah mu bar wannan banzar ak'idar na in jifa ya wuce kanmu ya fad'a kan kowa ma bamu damu ba, kuma Dad abun da ka bayar fa shine naka ba wanda ka ci ba, wanda ka bayar domin Allah shine ake d'orawa a mizanin ayyukanka kyawawa. Sannan ka sani Dad shi aikin alkhairi idan ka sirrinta kuma kaiwa wanda ya dace to wallahi Allah zaita bud'a maka ga kuma tarin lada da kake kwasa, ka daina yin kyautar da bata da lada balle la'ada, wato kyautar neman suna ba don samun lada ba, domin na fahimci a baya irinta kaita yiwa mutane, to me kenan ma aka yi k'arawa me k'arfi-k'arfi. Dan Allah Dad ina rok'onka da ka baiwa Goga hak'uri akan abinda ya faru, domin gaskiya ka bada babbar gudummawa a cikin shigarshi wannan halin."
Alhaji ya d'ago kai, sannan ya kalli Goga "ya ce, "Hakane, duk abinda Baby ta fad'a gaskiya ne, a rayuwata ina son naga nayi abu duniya tana maganata, nifa ban k'i ba ma ya kasance ni kad'ai ake labarina fiye da komai. Amma na gane kuskurena da jin wannan labarin naka, da kuma tunatarwar 'yata ka yi hak'uri, ka yafe min." Goga ya ce, "Ba komai ya wuce Alhaji."
Intisar ta kalli "Mahaifinta ta ce, "Dad ni na yafe musu, Shamsu ma haka, Ina rok'on alfarma a wajenka kasa a sakesu." Nan dai aka kashe case d'in aka sallamesu har da yaran Gogan gabad'aya. Dukkansu suka fito. Goga ne ya biyosu yana k'ara yi musu godiya, Intisar ta ce mishi kada ya damu ba wani abu. Kati ta bashi wanda yake d'auke da adireshin gidansu ta ce, gobe in Allah ya kaimu yazo tana son ganinshi. Kud'ad'e ta d'ebo ta bashi masu yawa, kimanin dubu hamsin ta ce, ya nema musu abin ci yanzu kafin zuwa gobe. Goga yaita mata godiya, Mahaifinta ya kalleta ya ce, "to ni zan tafi wajen aiki, na tura miki da million uku nasan zasu isheki siyan waya mai kyau, idan ma kinada buk'atar k'ari sai ki sanar da ni," Intisar ta ce, "Eh sun shigo tun d'azu Dad, nagode sosai." Alhaji ya ce, "To sai in ce sai kun dawo kenan ko?" Intisar ta ce, "To Daddy bye." Motarshi ya shiga ya rigasu ficewa daga Station d'in, inda suma suka shiga tasu. Gaba Shamsu ya shige ya zauna, har Bala zai ja motar su tafi Intisar ta ce ya tsaya, kallon Shamsu tayi ta ce, "Malam Shamsu ka dawo nan baya ka zauna saboda na samu abokin hira kaji ko." Ba tare da Shamsu ya ce komai ba ya fito ya shiga bayan, sannan Bala ya ja suka tafi.
Kallon Shamsu taketa yi, inda shi kuma sam ya k'i kallon inda take, sunanshi ta kira ta ce, "Jarumi," juyowa yayi ya kalleta, kashe mishi ido d'aya tayi cikin sauri ya sake mayar da kanshi k'asa, zuciyarshi na cewa na shiga uku na jawowa kaina jangwam.
Matsowa tayi kusa da shi, sannan ta dafa hannunshi, cikin sauri ya ture hannun nata tare da k'ara janye nashi. Idanun Bala tsaf a kansu, har da k'ara karkato da madubin nashi dan ya gansu da kyau, wani irin burki ya ja, sakamakon saura kad'an yai karo da wata mota garin kallonsu.
Tsabar burkin da Bala yaja ne yasa su Shamsu suka gwaru da juna sannan suka koma dai-dai. Intisar ta kalli Bala ta ce, "Malam ka lura da hanya sosai mana."
Bala ya figi mota da gudu yana cike da takaici. Intisar kuwa kallon Shamsu tayi tare da rage muryarta ta ce, "Wai kai sai yaushe zaka waye ne?" Shamsu ya ce, "Ba rana," Intisar ta ce, "Meyasa?" Shamsu ya ce, "Ai bana buk'atar wayewar ne," Intisar ta ce, "dolenka kuwa ka santa tunda kana tare da ni, a haka kakeso na aureka k'awayena su rik'a yimin dariya?" Sai a lokacin Shamsu ya fuskanceta sosai itama shi take kallo dama, ya ce, "Ashe dama ba zaki iya sona a yanda nake ba?" Intisar ta ce, "Zan iya mana, kai kasan yanda k'aunarka tai nisa a cikin zuciyata ne? Ko a yaya kake ina muradinka, ina muradinka a tare da ni, mallakarka kawai shine burina, amma kasan wani abu kuwa?" Shamsu ya ce, "a'a sai kin fad'a." Intisar ta ce, "Har yanzu mamaki nake ta yanda na fad'a k'aunarka lokaci guda, har na fara tunani anya kuwa ba asiri kai min ba kuwa?" Dariya Shamsu ya hau yi mata, inda ita kuma ta zuba tagumi tana kallon dariyarshi. "Shamsu ya ce, "Ba abinda nai miki, kawai Allah ne ya kamaki, kince zaki hukuntani to a maimakon haka sai ya sa miki sona a cikin ranki. Kuma dama ance in zaka k'i mutum ka k'ishi kad'an dan wata rana zai zama masoyinka, sai ki rok'i gafarata akan abubuwan da kikaita yimin." Duka ta kai mishi ya kauce tare da d'an d'aurewa, ya ce, "Menene haka wai kike son kai hannunki jikina?"
A haka suka k'arasa inda zasu siya wayoyin, fitowa sukayi suka shige ciki, suna shiga ta kalli Shamsu ta ce, "Kai fa zaka zab'armin wayar." Shamsu ya ce, "Ai ni bansan yanda manyan wayoyin nan suke ba, sai dai ki zab'a in tayaki gani." Intisar ta ce, "Akwai wata wadda nake son canzawa dama muje in dubata."
Zagayawa suke ta yi domin zab'ar wadda suke so, daga nesa ta hango wayar da take so d'in, cikin sauri ta nufi wajen, tana zuwa a dai-dai lokacin wata tasa hannu ta d'auko sai Intisar ta fizgi wayar daga hannunta. Wannan yarinyar da ta fara d'auko wayar ce ta ce, "Kan uba! Hajiya mandiya ya zan d'auki waya ki fizge daga hannuna me kike nufi?" Intisar ta kalleta ta ce, "Sai dai kiyi hak'uri ki nemi wata, na dad'e ina neman wannan wayar ban samu ba sai yau, banma yi tunanin zan sameta ba dan ance ta b'ace b'at, dan haka ga wayoyi nan da yawa ki duba wata." Yarinyar nan tai shewa, sannan ta ce, "Wallahi uban kuturu yai kad'an, ko wanene ubanki a k'asar nan sai kin bani domin na rigaki d'auka." Intisar ta ce, "Ba zan bayar ba, ban tab'a neman abu na rasa ba, dan haka yauma ba za'a fara ba sanadinki."
Shamsu yana gefe yana kallon ikon Allah, kokawa suka fara sosai a kan wayar, hakan ne yasa masu wajen suka taru domin rabasu kada su yi musu asarar waya mai shegen tsada. Duk wanda ya ji abinda ya faru Intisar ake baiwa rashin gaskiya, amma duk irin magiyar da akai mata ta k'i bayar da wannan wayar. Mamakin kafiya irin na Intisar Shamsu yake, wani daga cikin masu wajen ne ya zo wajen Shamsu ya ce, "Bawan Allah naga tare kuka zo da waccan yarinyar, dan Allah ka je kai mata magana ko kai zata ji maganarka mu samu ta bata wayar, tunda ta rigata d'auka, ita sai taje ta nemi wata ko taje wani shagon ta duba irinta tunda mu ita kad'ai ta rage mana." Shamsu ya ce, "To," suka tunkari wajen tare, suna zuwa ya kira sunanta ya ce, "Intisar," jin sunan tayi har k'wak'walwar kanta, dan bata tab'a jin ya kira sunanta haka ba. kallonshi tayi ta ce, na'am." Shamsu ya mik'a mata hannu ya ce, "Bani wayar." Ba musu ta mik'a mishi, Shamsu ya mik'awa masu wayar wayarsu sannan ya basu hak'uri. Jan hannunta yayi suka fito daga shagon. A bakin shagon ne ta kalleshi tayi rau-rau kamar zata yi kuka, cike da damuwa ta ce, "Jarumi amma ina muradin wayar fa sosai," Shamsu ya kalleta ya ce, "Na sani Jaruma, nima wayar ta yimun da farko, amma tunda naga an b'ata miki rai sanadinta naji ta ficemin a rai, dan haka mu tafi sauran shagunan ki duba wata kawai kinji, kai muje ma in zab'ar miki da kaina," Da farin cikinta kuwa ta amsa suka tafi wani shagon, suna zuwa sukai ta dubawa har ya hango wata Spark 5, ya d'auko ya bata ya ce, "Ki d'auki wannan tana da kyau, duk da kasancewar wayar bata da wani kud'i bata wuce hamsin da biyar ba, kuma ita ta dubu d'ari biyar take so ko ta d'ari takwas, ki ta sama da haka, amma cike da farin ciki ta karb'a tana dubawa ta ce, "Ka tabbatar ta yi maka kyau?" Shamsu ya ce, "Ai saboda kyawun nata ne ma yasa na zab'ar miki ita." Kallonshi tayi ta ce, "Duk da wayar bata da tsada kuma bata tab'a burgeni ba amma sanadinka yau naji tafi kowace waya a guna." Shamsu yai murmushin jin dad'i, sannan ya ce, "Godiya nake Jarumata." Intisar "To kaima bari na zab'o maka irinta sai muyi anko." Shamsu ya dakatar da ita ya ce, "A'a ki barshi na gode wadda nake da ita ma ta isheni."
Cikin b'acin rai ta ce, "Baka so ka ce ko?" Shamsu ya ce, "Kiyi hak'uri inada waya ta isheni," Intisar ta ce, "To shikenan tunda baka buk'ata nima bana so," d'aga hannu tayi ta buga wannan sabuwar wayar da k'asa tai ratsa-ratsa. Da k'arfi Shamsu ya kira sunanta ya ce, "Intisar!!!"
A BASU MAMAKIπ€ΎβοΈ
*π ±οΈK CE*ππ
Bilkisu iya
Assalamu alaikum,banga novel ko daya ba