Have you read my story INA GATANA? If you haven't ya kamata ki fara I'm sure you'll love it😍😍
Dedicated to stylish, happy birthday dear Allah ya 'kara miki rayuwa mai Albarka.
2nd dedication also goes to KARAMCI WRITER'S ASSOCIATION, happy 1 year anniversary 😍
23
Tana jin sallamarsa ta d'auko hijab ta saka domin ta gaji da mocking d'inta da yake akan cikinta. Amsa mishi tayi daga kwance tace "sannu da zuwa".
"Yauwa, meye na ganki a kwance haka?"
"Banajin dad'i ne luvly dan Allah ka barni yau naje asbiti a duba lafiyata". Ta furta tana lumshe idanunta, ba tareda ya kalleta ba yace "ba akwai kud'i a hannunki ba? Ni ban hana ki zuwa asbiti ba banida lokacin da zan kaiki gaskiya".
" Yanzu luvly sai naje na ciri kud'i sannan na tafi asbiti? Kaga 'karshen wata yayi ATM cika yakeyi ka bani a hannu naje kawai".
1000 ya zaro ya mi'ka mata ta kalli kud'in tace " luvly wannan zai kaini asbiti ya dawo dani sannan na sayi magani?"
" Canjina kenan kuma if I can remember da bakinki kika ce babynki ne I have no relation to him or her so go take care of your baby nayi adalci ma da na baki 1000 d'in".
Bata tanka mishi ba ya shige d'aki ya barta a kwance tana sa'ke sa'ken yanda zata cire kud'i taje asbiti. Tashi tayi ta d'auki takalminta ta fita tareda tarar abin hawa.
Saida taje banks uku layi yayi yawa ga kud'in hannunta 200 kawai ya rage, yanke shawara tayi ta nufi asbitin jin yanda jikin nata yayi mata babu dad'i ta ma rasa abinda ke damunta gaba d'aya.
Ko da taje asbitin basu saurareta ba suka ce baa transfer saidai ka bada cash, haka take d'aukan hanya d'an canjinta ta sake nufar wani ATM d'in. Tayi dacen mutanen dake layin domin wasu mutum biyu suka amince ta shiga ta d'auki kud'in kafin su ganin yanayin da take ciki. Godiya tayi musu ta cire 60k ta koma asbitin.
Anyi mata gwaje-gwaje sannan doctor ya fara tambayarta.
"Akwai wani abu dake damunki ne?"
"Eh, bayana yana ciwo, sai kuma...".
" Ba wannan ba damuwa nake nufi, kinada wani problem ne a gidanki ko a family ko neighbor ko wani matsala?"
Shiru tayi na d'an lokaci sannan tace " babu".
" Are you sure? Saboda jininki ya hau and your baby is underweight, batada kuzari sannan babu jini a jikinki, a wannan yanayin zaki iya shiga early labour".
Zare Ido tayi tace " doctor early labour? Me zai faru da babyna kenan?"
"Abinda ke faruwa da babyn taki kenan, ko heartbeat d'inta is not strong saboda haka sai kin kula sosai kin cire damuwa a ranki kin kuma kula da kanki saboda gaskiya zaki iya rasa babynki".
" Doctor to ya zanyi? Duk abinda aka fad'amin wallahi zanyi nidai banaso na rasa babyna please doctor". Ta furta hawaye na bin fuskarta, kallonta likitan yayi cike da mamaki, shirun da yayi ya saka zuciyarta ta sake karaya ta zage tana mishi kuka a office.
Da 'kyar ya bata baki ta samu tayi shiru sannan ya gindaya mata sharud'an da zata bi domin lafiyarta da na babynta tayi godiya ta kar'bi magunguna ta nufi gida.
Bayan ta koma gida ta zauna tana tunanin yanda zata inganta rayuwar abinda ke cikinta da tata rayuwar, idan zatayi hakan sai ta kauda idanunta daga duk wulakancin da yusuf zaiyi mata.
Tana zaune tana danna fruit salad a bakinta Yusuf ya shigo, sallama yayi ta amsa ya kalleta yace "ni na sani ciwon naki dama na 'karya ne so kike kawai ki fita, to kinje wajen lecturer d'in naki hankalinki ya kwanta? "
Ko kallonshi batayi ba ya cigaba da jifanta da muggan kalamai ya gama ya shige d'aki ya barta a wurin, numfashi ta dinga ja tana saukewa saboda kar tayi kuka.
TV ta saka a gaba ita a lallai sai ta cire abinda ke ranta saidai film d'in da akeyi tamkar saboda ita ake yinsa, ganin zai sakata kuka ya saka ta kashe ta nufi d'aki domin ita a yanzu ko kujera ta kalla sai taji idanunta sun cika da 'kwalla balle kuma ta kalli cikin dake jikinta bata sanin lokacin da hawaye ke kwararowa fuskarta.
Tana Shiga d'akin taji Yusuf yana waya da mace "please kar kimin haka just this once mu sake had'uwa mana da gaske nake miki ban ta'ba samun macen da ta yimin dai-dai yanda nakeso ba sai ke, yanzu fa ke kad'ai ce kuma gaskiya nake fad'a miki sannan indai kud'i ne ko nawa kikeso kin sanni zan baki ko nawa ne........ a'a million ashirin ina na ganta ki dai fad'i abinda zan iya". Dariya yayi yace " indai wannan ne yanzunnan zakiji alert... okay luv you sai goben and please don't be late I hate waiting".
Toilet Muneera ta shiga ta zauna tana jiran ya gama wayarsa ta fito, saida taji babu alamun sautinsa sannan ta fito ta sameshi yana sana'arsa ta chatting, ko kallonsa batayi ba tayi kwanciyarta tace "saida safe luvly".
Ganin ta dena damuwa da lamuransa ya sanyashi bud'e sabon page na wula'kantata, kud'in dake hannunta dashi take bu'katunta bata tambayarsa balle yace bazai bata ba, sannan gabanta yake waya da matan banza yayi ta kalaman da yasan zasu 'bata mata rai, haka zai dawo yayi kwalliya yace "Zan fita bazan dawo da wuri ba so kiyi baccinki kawai saida safe".
Haka zatayi baccinta saidai da safe ta farka ta ganshi a gefe, condom kuwa har ya dena 'boyewa a gabanta zai d'auka ya fita.
Ta dena zubda hawayenta a kansa wanda ita kanta tana mamakin hakan, saidai kawai taji 'kirjinta yayi mata nauyi bayan d'an lokaci shima ya sauka. Ganin cikinta yayi 8 months yasa ta yanke shawarar komawa gida.
Yusuf ya shirya zai fita Muneera ta tareshi tace "luvly inaso na koma gida".
"To Allah ya kiyaye". Ya furta tareda ficewa ya barta a tsaye. Wayarta ta d'auka ta kira Mama.
"Hello Mama".
_"au Muneera kece? Ya gida?"_
"Mama koyaushe na kiraki sai kin tambaya har yanzu bakiyi Saving numberta ba?". Muneera ta fad'i cikin rashin jin dad'i.
_to ai layin naki ne da mun gama waya na ajiye shikenan sai na manta"_
" To Mama....zan taho gida".
Cikin sauri Mama tace _" Zaki taho kuma? Lafiya dai?"
Muneera har ta lura da Mama bataso suyi wata waya mai tsayi saboda kar ta fad'a mata matsala, ta rasa meyasa Mama ke mata haka tana d'iyarta d'aya tal a duniya mace, ina soyayyar da Mama ta nuna mata a baya? Meyasa a lokacin da matsala ta sameta Mama take gudunta?
"Lafiya Lau gani nayi lokacin haihuwa na matsowa kuma nan banida kowa".
Shiru Mama tayi sannan tace " wata na nawa kike yanzu?"
" Takwas".
" Ki bari idan kin shiga na tara sai ki taho zaman gidan mai tsayi baida wani amfani, idan cikin ya shiga wata na tara kinga ba wani jimawa zakiyi ba Zaki haihu da kinyi arba'in ki koma abinki".
Shiru tayi tana tunanin abinda zata ce da Mama, tana so ta furta 'mama meyasa kike guduna a yanzu da matsala ta sameni?' Saidai bakinta ya kasa furta hakan, numfashi ta sauke tace "Mama tun kwanaki doctor ya cemin zan iya shiga early labour saboda babyn baida cikakkiyar lafiya, shiyasa naga ya kamata na dawo tunda kinga ni kad'ai ce shima idan ya fita sai can dare yake dawowa".
" To shikenan amma ba dai yau ba ko nan da sati biyu ne sai ki taho, a gaida mai gidan". Mama ta fad'i tana katse kiran cikin sauri. Kallon wayar Muneera tayi tana girgiza kai tana mamakin rayuwa.
Tana wanka taji shigowar Yusuf, fitowa tayi d'aure da zaninta ta d'auki hijab ta saka domin tasan tabbas ya kalleta sai ya aibata ta da cikinta, parlour ta fito ta sameshi ya bud'e drawer da yake ajiyarsa.
A tsorace ya kalleta yaja tsaki yace "me kikeyi anan? Ba kince zakije gida ba?"
"Na Kira Mama ne tace na bari sai bayan 2 weeks".
" Um kowane iyaye dai na farin cikin ganin 'yarsu idan tayi aure banda ke, ke ko irin iyaye suzo dubaki d'innan ba'a ta'ba yi ba idan kinje ma fatansu su koro ki su huta. A haka kike neman saki a wurina bayan nine rufin asirinki".
Bata tanka mishi ba ta koma d'aki yayi tafiyarsa yawonsa.daga ranar a kullum akwai kalar habaicin da zai sauke mata har saida ta gaji da 'kyar tayi kwana takwas ta tattara kayanta ta nufi gida. Saida ta sauka a Kano sannan ta kira Mama ta fad'a mata sannan ta kira Hidaya ta sanar mata itama.
Murna sosai Hidaya ke yi ta tashi ta nufi part d'in Mama ta hau gyarawa Muneera d'aki, harda yi mata wurin aje kayan baby domin tasan Muneera maybe saida ta kwaso komai na haihuwa ta taho.
Kiranta take ta tambayeta abincin da takeso saidai batayi picking ba, Mama ta tambaya tace "Mama kinga Muneera tunda mukayi waya tace ta sauka har yanzu bata 'karaso ba".
" Tana nan 'karasowa kinsan yanayin hanya".
Hidaya da zainab zama sukayi d'akin Muneera suna hirar babyn da zata haifa, zainab tace mace Hidaya tace namiji, Hidaya tace baby zaiyi kama da Muneera zainab tace a'a da babansa zaiyi kama, sunata hirarsu tamkar su zasu haifi yaron.
"Na fad'a miki namiji ne saboda idan na tambayeta ya baby sai tace yana lafiya kinsan kuwa ai namiji ne, kuma zata zo Zaki gani kayan maza zata taho dasu". Hidaya ta fad'i tana sake duba agogo. Maganar Muneera suka jiyo a parlour cikin sauri dukkansu suka fita.
"Oyoyo twinnie.... Kai na zaci ai haihuwa kikazo har ina gyara wurin aje kayan baby". Hidaya ta fad'a tana turo baki, murmushi Muneera tayi tace "eh mana haihuwa nazo".
"A wannan cikin?"
Tsit Muneera tayi tamkar ruwa ya cinyeta domin maganar tayi mata kama da irin wadda Yusuf yake mata. _a wannan cikin zaki ce wani zakije bikin ma'kwabta ko kunya bakyaji? _
"Ahaf nifa nace tsabar zumud'i ne kawai kika taho da wuri amma cikinnan nidai a idona baiyi girman da zai kai haihuwa ba". Hidaya ta katse ma Muneera tunanin da takeyi.
Kallonta Muneera tayi a jikinta taji tamkar taci zarafinta tace "duk girman cikinnan kice bai isa haihuwa ba?"
Dariya Hidaya tayi tace " nidai wallahi banga girman ba maybe you're in a hurry to deliver shiyasa zaki ga girman cikin amma fa kalli kamar baifi 6-7 months ba ko zainab? Ko dai hijabin da kika dafka ne ya 'boyeshi? "
'bata rai Muneera tayi tace " kina so dai ki cimin mutunci ne kawai twinnie amma cikinnan tun yaushe ake cewa nayi bala'in muni kuma ya fito yayi 'katoto idan na saka Kaya kamar agwagwa? Ko ace kamar cikin akuya? "
" Inji uban wa? " Zainab da Hidaya suka fad'i a tare wanda ya sanyasu 'kyal'yala dariya sannan zainab tace "ko ma waye ya fad'a tsokana ce kawai amma ni banga abinda ya sauya a jikinki ba sai rama da kikayi. Kuma a zaunennan da kike ma ba kowa zai gane kinada ciki ba balle ma cikin fari ai baya wannan mugun girman da yake cika gari har wani ya tsokane ki, ki cire hijabinki ki sha iska ba wani muni da kikayi".
Bata yarda da maganarsu ba ta dai cire hijabin ta aje a gefe, tashi sukayi tare suka nufi kitchen d'auko mata abinci sai tayi tunanin kamar gulmar cikinta zasuyi. Da ta jiyo maganarsu 'kasa-'kasa har ta fara 'kwalla, wato a gidansu ma baza'a barta ba sai anyi mata izgili?
Fitowa sukayi tare suka ajiye kayan abincin sannan suka zauna suka fara ci tare, ko rabi basuyi ba Muneera tace ta 'koshi.
"Haba Muneera shiyasa kikayi rama masu ciki da suke da ci amma ke kalli d'an abinda kikaci zaki tashi? Bazai yiwu ba idan ke kin 'koshi babynmu bata 'koshi ba". Zainab ta fad'a tana kamo hannun Muneera tana maidawa cikin plate d'in. Rabon da ace ma Muneera ci har ta manta balle kuma ace ci domin babynki, babu ruwan Yusuf idan taci kanta idan bata ci ba yafi jin dad'i ko ba komai babynta zai galabaita.
"Kici mana, gwara kici kiyi amai da dai ki zauna da yunwa, oya kici idan miya kikeso a 'kara miki gata, idan yaji ne ma akwaishi idan nama kikeso gashi, muyi mu gama cin abincin muje muga tsala-tsalan kayan baby da kika taho dasu idan na namiji ne wata zata sha dundu a wurinnan". Hidaya ta fad'a tana ma zainab gwalo." Idan kuma na mace ne wata zata sha ran'kwashi".
Dariya Hidaya tayi tace "kina ran'kwashina zan tada aljanu".
" Ba dai na ran'kwashekin ba?" Zainab ta fad'a tareda yiwa Hidaya gwalo. A yau sunyi motivating Muneera har ta ci abinci sosai kuma taji dad'insa sa'banin a Lagos duk abinda taci saidai domin maganin yunwa.
Saida suka cinye abincin tas abin mamaki Muneera harda 'kari sannan suka nufi d'akinta ganin kayan baby, shiru tayi musu domin ita ta manta ma ana sayen kayan baby. Farkon aurenta tana mafarkin yanda zata samu ciki tun a asbiti Yusuf ya nuna farin cikinsa ta hanyar d'agata a gaban doctor, sannan ya yiwa doctor kyauta mai tsoka sai kuma ya kasa ha'kuri sai sun biya baby shop sunyi musu akan mace ne ko namiji, a 'karshe su sayi kayan mace kala d'aya na namiji kala d'aya wanda zasu dinga d'aukowa suna kallo suna hira da babyn dake ciki, Ashe duk wannan mafarkinta ne ba nashi ba. A yanzu tana rayuwa ne without her dreams domin gaba d'aya dreams d'inta sunyi shattering.
"Muneera!" Juyawa tayi da sauri ta kalli zainab tace "magana kikeyi?"
"Tambayarki mukeyi ina kayan babyn suke kina nan kina tunanin labour room".
" Au, oh.... Umm... Dama.... Oh kayan baby ko? Umm..... Cewa yayi... Umm yauwa cewa yayi bayaso nayi kaya da yawa nazo nayita jan nauyinnan sai ya turo min kud'in yace idan nazo sai na saya anan yafi sau'ki".
" Okay.... " Hidaya ta fad'a tana kallon Muneera domin tasan 'karya take saidai bata ce da ita komai ba, idan ta za'bi ta rufe siririn gidanta ita kanta mai mata farin ciki ce domin sirrin aure ba abin bud'ewa bane.
"Kuma hakan dabara ce ko Hidaya? Sai mu saka rana mu sayo abubuwan da ake bu'kata kar haihuwa tazo ba-zata babu shiri". Zainab ta fad'i tana maida kayan Muneera cikin akwatinta.
"Eh muje Mama ko aunty suyi mana list na abubuwan da za'a saya kawai sai mu samu time da babu school muje muyi sayayya d'aya mu huta".
Bayan sunyi sallar magrib suka samu Mama suka mi'ka Mata paper kan ta yi musu list na abubuwan da zasu sayo na haihuwa, kallon paper tayi ta jinjina kai tace "wai, ni yaushe rabona da haihuwa? Nidai bazan tunawa ba gaskiya kuje wurin auntynku ita batada mantuwa amma fa kunsan mu mutan da ne ba lallai kayan haihuwarmu yayi d'aya da naku ba".
Wurin aunty suka je suka mata bayani tace " bari na fad'o muku ku rubuta, akwai zannuwa guda biyu sai kayan uwa suma kala biyu, sai kayan jariri kala biyu..."
" Wai Aunty komai biyu ake sakawa?". Zainab ta katse aunty, ran'kwashinta Hidaya tayi tace " ki mana shiru ana lissafi".
"Sai pad, sai zaitun, sai reza sai...."
" Reza? Wa za'a yanka?" Zainab ta sake tambaya. Dariya aunty tayi tace " wanda ya fiye tambaya".
Bayan ta gama musu list sannan suka tambayeta yanda zasu sayo kayan baby ta basu shawarar yanda ake za'bar kayan baby.
Kwanan Muneera uku ranar lahadi suka jata zuwa baby shop, Kaya suke d'aukowa duk abinda suka nuna mata sai tace eh gashi ta'ki fad'a musu macece ko namiji duk dabarar da sukayi ta'ki fad'a.
Tana zaune ta hango wata baby gown light purple rigar ta d'auki hankalinta sosai. D'aga rigar tayi tana kallo tana tunanin ko zata ma babynta kyau taji cikinta yayi motsi. Farin cikin da taji baya misaltuwa domin motsin babyn tata abu ne mai tsada sai lokaci zuwa lokaci take ji.
D'aura rigar tayi a kan cikinta tana murmushin da ta jima bata yishi ba sannan ta nad'e rigar zata mi'ka ma su Hidaya, ai suna ganin haka zainab ta zage ta zubawa Hidaya ran'kwashi wanda saida tayi d'an 'kara sannan suka koma lodar kayan baby girl.
Kamar mahaukata suka zama duk kayan da suka d'aga sai sunce "woooooowww!!" Har suna jan hankalin mutanen dake gefensu. Muneera babu abinda takeyi sai dariya saida suka gama tace "kun d'ebo kayan mata idan kuma namiji ne fa?"
"Sai mu dawo dasu mu kwashi na maza, final".
Ko da suka koma gida binsu da ido aunty da Mama sukeyi ganin kayan da suka sayo duk na mata Aunty na tsokanarsu tana fad'in idan aka haifi namiji saidai a saka mishi a haka baza'a sauya ba.
Muneera na zuba idanu taga ko Mama zata mata maganar matsalarta amma taji tayi shiru, ko hira basu cika yi ba indai Hidaya da zainab basa nan Muneera tana d'akinta tana tunani saidai idan Aunty ce tayi kiranta, mafi yawan lokuta Aunty ke d'ebewa Muneera kewa tana mata tambayoyi akan lafiyarta.
Hidaya da zee kuwa duk ranar da suke free sai sun bud'e akwatin kayan baby sun sake jerasu, a kullum sai sun yabi kayan babyn.
Yusuf kuwa tunda Muneera ta dawo bai kirata ba, babu text ko flash call bai ta'ba mata ba, saidai tayi 'karya tace da Baba sunyi waya da Yusuf yana gaidashi.
Numbersa ta saka a wayar Hidaya tana duba WhatsApp d'insa, a kullum yana online har status yake sakawa amma bai san ya tuntu'bi lafiyarta ba. Ta yanke shawarar neman saki a hannunsa da zarar ta haihu, gwara tayi zaman kanta akan ta cigaba da zama da mutum irin Yusuf marar imani, mara tausayi kuma wanda baisan darajar d'an Adam ba, Bai d'auki mace aba mai muhimmanci ba a rayuwarsa.
A wannan yanayi har cikinta ya shiga watan haihuwa a lokacin ta fara fargabar abinda zata tarar, kullum zuba ido take taji ta fara labour gaba d'aya hankalinta ya tashi.
Ranar da ta fara jin ciwo ta kira yusuf, saida ta mishi 15 missed calls bai amsa ba wannan takaicin yasa lokaci guda ciwo ya taso mata, kuka take Aunty tana ce mata "ki dena kuka addu'a ya kamata kiyi Muneera d'abia mai kyau itace mace ta haihu da ambaton Allah a bakinta".
Hidaya tana gefe itama jikinta duk yayi sanyi ganin yanayin da Muneera take ciki, saidai kukan Muneera ba na ciwo kawai bane harda takaici. Wayar Muneera ce tayi 'kara Hidaya ta d'auka taga message ne, cikin sauri Muneera tace "waye Hidaya".
"Kamar Yusuf ne, yace he's busy now stop call...... he'll call you back when he's less busy". Hidaya ta yanke 'stop calling me like this' da yace, girgiza kai muneera tayi tace " Aunty banaso muje asbitin".
"Saboda me Muneera? Mu saka ki gaba muna kallo kina ciwo kenan? Ki daure muje cikin yardar Allah sai kiga kin haihu cikin sau'ki".
Har ciwon ya fara lafawa Muneera, kallon Aunty tayi tace "Aunty banaso muje asbiti, ku barni a gida kawai fatana haihuwarnan tazo da matsala ni da abinda ke cikina duk mu mutu mu huta, ku yimin addu'a na mutu na gaji da rayuwarnan".
Hidaya dake gefe a take ta fashe da kuka, itama aunty shiru tayi jikinta yayi sanyi domin bata ta'ba tunanin haka daga bakin Muneera ba, zafin na'kuda yana saka kiran mutuwa amma kowacce uwa tana so d'an da zata haifa ya rayu, zafin ciwo ne ya saka Muneera take kiran haka ko kuwa?"
Dafata Aunty tayi tace " cuta ba mutuwa bace muneera kuma na'kudarnan kowa ita yayi ya haihu, ki dena kira ma kanki mutuwa Allah ya saukeki lafiya ke da babynki".
"ba Amin ba Aunty, dan Allah ki min addu'a na mutu na huta".
Girgiza kai Aunty tayi tace " Hidaya zo ki ri'kemin ita mu tafi asbiti".
Muneera kuwa jajircewa tayi ita babu asbitin da zataje a barta a gida, da 'kyar suka kamata suka sanyata a mota suka nufi asbiti.
Haihuwa tazo ma Muneera ciki sau'ki domin 2 hours da isarsu asbitin ta haifi 'yarta mace, nurse d'in da ta fad'a mata ta haihu ma ji tayi tamkar ta sha'keta domin har cikin ranta so take ta mutu ta huta.
Bayan an goge babyn nurse d'in ta mi'ka ma Muneera tace "ga 'yarki ki mata addu'a". Ta d'aura babyn a kan cikin Muneera, kallon yarinyar Muneera tayi a lokacin babyn ta bud'e idanu ta kalli mahaifiyarta, wani irin yanayi Muneera taji a zuciyarta, d'auke kanta tayi tace " ki d'auketa".
"Kin mata addu'ar?"
"Nace ki d'auketa kawai daga jikina". Muneera ta furta hawaye na zubowa daga idanunta tana nadamar d'aukan cikin da tayi in the first place sannan tana nadamar barinsa da tayi har ya girma ta haifi 'yar da zatayi nadamar samunta a uwa.
Kanta taji yayi mata wani irin nauyi ta runtse idanunta, gaba d'aya taji d'akin ya fara juya mata sai jin muryar nurse d'in tayi tana fad'in "subhanllahi, kira doctor hurry!!!!!!" less