Kamala Minna
ME YA SA...?
Na kasa fahimtar cukumurɗar nan, lamarin yana raunata min lissafi sosai.
Akwai mazaje da yawa da suke yiwa mace kallo wata maras tunani da lissafi a cikin rayuwarta. Bata da iko ko alfarma a fannin a yi shawara da ita,ko a zauna da ita cikin wani zance ko lamari da ya jirkice ake neman mafita.
Sai kaji ana cewa bata da lissafi ko shawarar da za ta bayar har anyi amfani dashi, domin bata san kanta ba, shiririta kawai zata yiwa mutane.
Ba abin takaici da ciwon rai, sai Mazaje da suke yiwa matansu kalar fahimtar nan, sai ka ji namiji na cewa ba zai nemi shawara da matarsa ba, mace ce ita kanta bata san kanta ba shiririta za ta yi masa.
Na kasa fahimtar tunanin mazajen nan.
Shin mace ita ba mutum bane ko kuwa bata da zuciya da kwanyar da za ta yi tunani da ita ce?. Shin namiji ne kawai mai hangen nesa da sanin ya kamata ko ya ya?
Na kasa fahimtar gangan ɗin nan.
Lissafin mace da namiji na sani ba ɗaya bane na amshi Farillar nan.
Amma mai yasa ba za ake yi musu adalci ba wajan ba su dama a cikin neman mafita? wannan tauye haƙƙi ne da mai da mace ta ji a ranta ita ba wata bace hakan kuma damuwa ce da ke sanya ciwuka masu girma a zuciyar mace.
Don Allah ake adalci
Kamar yadda ake ganin mace bata cancanta da lissafin neman mafita ba, to haka shima namiji. Akwai mazajen da tunaninsu in aka sanya shi a sikile wallahi Allah ko an amshe shi a matsayi mafita faɗuwa za ayi warwas macen da aka raina sai ka ga ita nata da aka mai kallon hadarin kaji ya yi amfani.
Kalmar Wasu Mazan da wasu matan ya kamata ace ana ado dashi wajan yanke hukunci ba wai ayi jam'u wanjan faɗin MATA ba hakan rashin adalci ne.
Matarka fa sirrin kace duk yadda za kayi saɓa-ta juya-ta sunanta ba zai taɓa canzawa a sirrinka ba. Ya kamata ake adalci. An san ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, don haka ake saka kalmar 'Wasu' a duk abinda za ayi in har ana son adalci.
Zama kayi nazari da tunanin wani duhu da ka shiga tare da iyalinka ba karamar shakuwa da girmamawa da sanya zukatan iyalan naka alfahari hakan ke yi ba, don Allah ake duba ana saran bakin gatari.
Ɗiya mace daraja ce da ita, girma ne da ita, in ka kira mace duk mara lissafi kana da uwa fa ita a wani mataki zaka ajje ta?🤔
Allah ya kyauta.
KamalaMinna.
Ummyter Abdallah
Madam din Dana kewa aiki jiya ta aikeni na sayo mata semo 2kg,danaje shagon sai na tarar sai 1 kg,so na dawo ban sayo ba shine tace min ni Wawa ne bana amfani da hankalina na sayo 1kg guda biyu ya zama 2kg Kennan idan an hada,na bata hakuri dai ta hakura,yau kuma tace na sayo mata slippers number 8,danaje babu sai lamba 4 shine na sayo lamba 4 guda biyu,na kawo batace komai ba Naga tana hada mini kayana cikin jaka,shine nake tambaya ko wanki zatayimin koko daki zata canjamin🤪🤪🤪
Rufaida Umar
(owner)
Ku je marubuta group kar garaɓasa ta wuce ku!
Mukhtar Musa Karami Abu Hisham
Cinikin mutum ake kamar yanda ake cinikayya a kasuwa,farashi suke yanke wa kamar yanda ake yi a super market,basa yin ragi balle su nuna alamar sauki,idan ka biya kudi su baka,idan ka ki biya su kasheshi.
Basa tsoron kowa,balle su yi tunanin akwai wanda zai iya tunkararsu,dole akwai abin tsoro fa,kasar nan ta mu akwai firgici sosai,Ya Allah ka karemu daga wannan masifar ta satar mutane.
Allah ka bamu lafiya da zama lafiya amin