Sadik : *_SAKON TA'AZIYYA DAGA PEN WRITERS ASSOCIATION._*
*_Assalama alaikum warahamatullahi... more*_SAKON TA'AZIYYA DAGA PEN WRITERS ASSOCIATION._*
*_Assalama alaikum warahamatullahi wabarakatuh._*
*INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN!!!*
_A madadin daukacin mambobin kungiyar marubuta ta *PEN WRITERS*, ina amfani da wannan dama wajen mika sakon gaisuwar ta'aziyya ga 'yar uwarmu Asma'u Abdullahi *(Ummyter Bingyel)* wacce ta yi rashin mahaifinta. Babu shakka wannan babban rashi ne da ba za'a taba mantawa ba, muna taya ki alhini._
_Muna addu'ar Allah Ubangiji ya jaddada rahama a kabarinsa, Allah ya yafe masa dukkan kura-kuransa. Allah ya kyautata makwancinsa ya sa Aljannar Fiddausi ce makomarsa da mu baki daya._
_Bayansa da ya bari muna rokon Allah ya ba su hakuri da juriya bisa wannan rashin da suka yi. Allah ya yi musu albarka Allah ya kara inganta rayuwarsu._
Murja Naikke: MALTINA DA PEAK MILK BASA KARA JINI A JIKIN DAN ADAM:
Diyawa za kaga a kasar hausa a lokocin da aka tabbatar da mutum yana karancin jini, ko tana dauke da juna biyu ko ta Haihu ta zubar da jini diyawa sai kaji ance a bashi malti na da peak milk, a... moreMALTINA DA PEAK MILK BASA KARA JINI A JIKIN DAN ADAM:
Diyawa za kaga a kasar hausa a lokocin da aka tabbatar da mutum yana karancin jini, ko tana dauke da juna biyu ko ta Haihu ta zubar da jini diyawa sai kaji ance a bashi malti na da peak milk, a fahimtar mutanen mu zai kara jini.
Gaskiyar magana babu alaka sakanin karin jini da Maltina da Peak milk, sabida wake kwara daya yafi Maltina da Peak milk wajen samar da sinadaran kara jini.
Idan kun duba jikin gwamgwanin peak milk za kuga babu sidaran karin jini a ciki ( not rich in iron) Haka Maltina ma Babu sinadaran kara jini a ciki.
Tambaya anan shine ta Ina Maltina da Peak milk yazama maganin karin jini ?
Amsa: wannan kawai al'adace ta mutanen mu ba tareda sanin abun ba.
Maltina na dauke da sinadaran:
- Calories
- Carbohydrates
- Fat
- Vitamin
- No Iron
Peak milk na dauke da sinadaran:
- Fat
- Carbohydrates
- Protein
- Salt
- Vitamin A and D
- No Iron
Jikin dan Adam yana samar da jini da kansa, shi jini yana buqatar sinadaran iron daga abincin da muke amfani.
Daga karshe ina bada shawara garemu kudin da muke kashe wajen Maltina da Peak milk domin kara mana jini, muyi amfani da su wajen siyan abinci masu dauke da iron kamar :
- Wake
- kifi
- Nama
- kwai da sauransu
- zogole
- Cashew
- cavage
- salat
- Spinach
- da sauran su.
Allah ya kara mana lafiya gabaki daya.
📝 Zannah Mustapha Wakil
Lafiya Uwar Jiki
lafiyauwarjiki50@gmail.com less
Ciwon kaba, wani ciwo ne da ke faruwa saboda gajiyawa ko raunin jikin naman da ya rufe ciki (wato naman da... moreCIWON KABA (HERNIA)
Ciwon kaba, wani ciwo ne da ke faruwa saboda gajiyawa ko raunin jikin naman da ya rufe ciki (wato naman da yake
karkashin fatar da ta taso tun daga kahon zuci har zuwa mara), wadda kan sa tsagewar wani bangare na naman. Hakan ke sa halittun jikin dan Adam na ciki, kamar hanji ya fito ta wannan
’yar kafa.
ABUBUWAN DAKAN KAWO (KABA)
Abubuwan da ke kawo ciwon kan ka su kashi biyu kamar haka:
1. Gado (Congenital): Ana gadon ciwon tun a ciki, sai jariri ya fito da ita kabar.
2. Wanda ake samu daga baya (Acquired): Wannan nau’i ne da ake kamuwa bayan an girma saboda raunin naman jiki, sanadiyar KIBA sosai ko kuma tsananin aikin da zai wahalar da jiki kamar daukar abu mai nauyi. Duk lokacin da wani bangare na naman jikin mutun ya samu gajiyawa sakamakon daukar nauyi, ko tari na tsawon lokaci, ko ma tsananin yunkuri lokacin ba haya, duk sukan sa naman ya rabu biyu, ta yadda wani sashe na ’ya’yan hanji zai biyo hanyar.
Shan taba sigari ma kan sa mutun ya kamu da cutar saboda tsananin tari sanadiyyar ciwon huhu da sigari ke sa wa.
IRE-IREN SA
Iren-iren ciwon: Ciwon ya fi yawa ne a mahadar kashin cinya da kugu (Inguinal and Femoral Hernia), gefen al’aura.
1- Akwai wadda ke faruwa a saman layin da ya raba kirji zuwa cibiya gida biyu (Epigastric Hernia). Wannan nau’in ya fi shafuwar maza a kan mata. Sama da kashi 75 na cutar a maza aka fi samun ta.
2-Sai wadda ke faruwa a cibiya, takan faru ne idan aka samu gajiyawar jijiyoyin jini da ke kawo jini ga cibiyar. Wannan nau’in kan auku ga yara sa’annan takan bayyana sosai a shekarun 3 zuwa 4 ko ta zauna har tsawon rayuwa idan ba a dau mataki ba.
Iyaye kan lura da ciwon a lokacin da yaro ya yi tari, za ta fito a gefen cibiya.
3-Sai wadda ke faruwa sanadiyyar daukar ciki ko haihuwa ga mata a mahadar kashin cinya (Femoral Hernia).
4-Akwai kuma wadda ke faruwa sanadiyyar fida (Surgical Hernia). Wannan tana faruwa ne sanadiyyar matsalolin da ba a rasa ba, wani lokacin idan aka yi fida, musamman idan babu
kyakkyawar kulawa a gefen da aka yi fidar.
ALAMOMIN KABA
Alamomin cutar:
1- Mutun zai rika jin wani abu ya fada masa a wani bangaren jiki ko ya fice.
2- Sai kuma jin zafi, kamar kuna a bangaren da abun ya faru.
3- Sai kumburi ko a ji dan kululu.
4- Jin zafi lokacin daukar wani abu mai nauyi, ko yayin tari. Zafin kan bazu zuwa sauran bangarorin jiki kamar baya, kafa
ko al’aura.
HANYAR MAGANCE CIWON
Hanyar magance ciwon: Hanya mafi inganci domin kawar da ciwon kaba shi ne fida, domin a gyara wannan wuri da yake rauni. Idan kuma aka ki zuwa a yi aikin, to ciwon ba ya mutuwa da kansa sai dai ya kara girma wani lokaci kuma ya rika zafi sosai, wanda hakan barazana ce ga rayuwar mutum.
Bayan aikin fida mutun zai ji rashin walwala da dan zafi na ’yan kwanaki, kafin ya fara jin sauki. Hakan kan dauki sati daya zuwa shida kafin a ji garau. Amma wadanda ke daukar nauyi ko aiki mai wahala, to za su dauki tsawon lokaci kafin su warke.
Allah yakara mana lafiya, marasa lafiya Allah ya Basu lafiya.
Murja Naikke: AMFANIN DANKALIN HAUSA A JIKIN DAN ADAM:
Kwararru da masana dankalin Hausa sun yi kira ga mutane da su yawaita cin dankalin ganin cewa yana dauke da sinadarorin dake kare mutum daga kamuwa da kowacce irin cuta a... moreAMFANIN DANKALIN HAUSA A JIKIN DAN ADAM:
Kwararru da masana dankalin Hausa sun yi kira ga mutane da su yawaita cin dankalin ganin cewa yana dauke da sinadarorin dake kare mutum daga kamuwa da kowacce irin cuta a jiki.
Dankalin Hausa na dauke da sinadarai kamar haka :
- Calories
- Water
- Protein
- Carbs
- Sugar
- Fiber
- Fat
- Pro-vitamin A
- Vitamin C.
- Potassium
- Manganese
- Vitamin B5
- Vitamin B6
- Vitamin E
- Da sauransu
Wasu daga ciki amfanin da yake yi a jikin mutum sun hada da:
1. Yana kare jiki daga kamuwa da cututtuka.
Dankalin Hausa na dauke da sinadarin Vitamin B6 wanda ke kaifafa kwakwalwa, hana kamuwa da dajin dake kama jini, hana damuwa, kawar da laulayin haila da sauran su.
Dankali na dauke da sinadarin Vitamin C wanda ke warkar da mura, tari, warkar da ciwo ko rauni da sauran su.
Sannan yana dauke da sinadarin Vitamin D dake karfafa aiyukkan hanji, karfafa kasusuwa, hana kamuwa da dajin dake kama fata da sauran su.
2. Yana kara karfin kashi
Dankali na dauke da sinadarin Magnesium da ke taimakawa jikin dan adam wurin hutu inda an gaji kuma yana inganta buguwar zuciya da inganta jijiyoyi da kasusuwan jiki.
Yana kuma dauke da Potassium da ke kawar da cutar koda da kawar da kumburin ciki da taimakawa jiki amfani da sinadaren da ke cikin abinci
3- Yana kara karfin ido
Dankalin hausa na dauke da sinadarin Beta-carotene da jikin dan adam ke sauya ta zuwa Vitamin A da ke inganta lafiyar idanu da karfafa garkuwar jikin dan adam. Karancin Vitamin A a jiki mutum na haifar da wata cutar makanta da ake kira Xerophthalmia.
4. Kara lafiyar kwakwalwa
Cin dankalin hausa musamman mai jan launi yana inganta yadda kwakwalwa ke aiki.
Binciken da masana suka gudanar da dabobi ya nuna cewa sinadarin 'anthocyanins' da jan dankali ke dauke da shi yana inganta lafiyar kwakwalwa da kare shi daga cututuka duk da cewa ba a gudanar da nazirin kan 'yan adam ba.
5. Kawar da cutar daji
Dankalin hausa na dauke da sinadarai masu yaki da kwayoyin cuta 'antioxidant' wanda ke kare jiki daga kamuwa daga cutar daji.
6. Yana Daidai ta Suga
Dankalin Hausa na dauke da sinadaran daidai ta yawan siga a jikin mutum sabida haka yana kawar da cutar siga.
Murja Naikke: TUSAR GABAN MACE (QUEEFING KO VAGINAL GAS)
Tusar gaban mace: itace fitar da wani iska musamman lokocin jima'i da mijinta, ko idan tayi wani motsin sai taji gabanta yana fitar da wani iska harda kara kamar... moreTUSAR GABAN MACE (QUEEFING KO VAGINAL GAS)
Tusar gaban mace: itace fitar da wani iska musamman lokocin jima'i da mijinta, ko idan tayi wani motsin sai taji gabanta yana fitar da wani iska harda kara kamar tusa.
Dalilan da suke kawo wannan tusar gaban sun hada da:
1- Pelvic floor weakness : Sakewar naman cikin farji, idan naman cikin farjin mace ya sake yayi zududu baya iya rike abu yakan kawo wannan matsala.
2- Infection : Shigar kwayar cuta bangaren da ya shafi magaifa ko mafitsara shima yakan haifar da wannan matsala.
3- Feminine hygiene products : chuse-chusen kayan mata, da wassu sabulai marasa asali domin sarkake farji ko matse shi yakan haifar da wannan matsalar.
4- Inserting an object in the vagina : tura wani abun da ba muhallin sa ba suwa cikin farji yakan kawo wannan matsalar.
6- Vaginal Fistulas : Wannan idan akan samu tazara ko wata kofar tsakanin hanyoyin da ta hada farji, mafitsara da wajen kashi akan samu wannan matsalar.
Sai Kuma wassu hallayar mu da take taimaka wajen kawo wannan matsalar:
1- Zama a kasa cikin A.C ba wando kuma a kan tiles.
2- Yawo ba takalmi musammanma a AC kuma kan tiles.
3- Kwanciya ki kunna fanka kuma ba wando a jikinki.
4- Rashin yin tsarki da ruwan zafi.
5- Rashin yin tsarki bayan gama jima'i. Wato barin sparm ya kwana a jikinki ba tare da yin tsarki ba.
6- Yawan yin maganin mata ba gaira ba dalili.
7- Rashin iya positioning na kwanciyar aure da miji.
8- Zama da fant guda daya tun daga safe har dare sai kaga mace ta bar fant tun safe har dare yana jikinta tsaban qazanta.
Hanyoyin samun sauki ko waraka:
1- Ayi kokori zuwa asibity domin ganin likita wanda ya kore a bangaren abinda ya shafi mahaifa (Gynaecologist)
2- A kiyaye dukkanin abinda zai kawo wannan matsalar.
3- Adinga yin kagel exercise lokoci bayan lokoci domin naman farji ya samu karfi.
Bayan anje asibity an tabbata matsalolin da muka irga babu daya daga ciki a gwada wannan:
Ki nemi ganyen magarya da gabaruwa, da "ya" yan hulbah. Sai ki hadasu GU daya kina dafawa sai ki Debi gishirin cikin tafin hannunki ki zuba chiki. Sai ki dinga shiga kina seatbirth da shi na tsawon 20 minutes. Sannan ki nemi farin muski sai ki dangwala da auduga me tsafta ki yi matsi da shi.
Murja Naikke: Aslm matan sirri kece kina da kishiya gidanku daya amma kowacce da bangarenta kece uwar gida kika haihu bata zo tayi miki barkaba Ana nan yaron ya mutu batazo tayi miki gaisuwaba kika gaya wa mijinku yace zai mata magana daganan yashare zancen kuma... moreAslm matan sirri kece kina da kishiya gidanku daya amma kowacce da bangarenta kece uwar gida kika haihu bata zo tayi miki barkaba Ana nan yaron ya mutu batazo tayi miki gaisuwaba kika gaya wa mijinku yace zai mata magana daganan yashare zancen kuma batazoba kwatsam itama tasami ciki taxo haihuwa akayi mata cs aka ciro yara biyu tasha wahala bakije dubata ba a asibitn ranar da suka dawo gida kina ganinsu kika kauda kanki kamar baki gansu ba to shine tana shiga daki ta kama kuka tana fadan maganganu dayake mijinku tare suka dawo shine mijn yazo yadinga yi miki masifa har yana cewa inbakije kinyi sannu ba da barka saidai kiyi gidanku shi bazai iya baqin hali ba bayan kingaya maasa duk abin datayi miki amma sai cewa yayi ai wancen ya wuce maganar yanxu akeyi kuma baki ga yarinya bace ba shin yaxakiyi zakijene kiyi mata barkan ko zakiyi gidanku din? less
Murja Naikke: Aslm Aunty don Allah ki boye sunana saboda akwai wadanda suka sanni a group dinnan.
Mu ukune a gurin mijinmu kowacce gdanta daban Ni mijina mutuwa yayi inada yara uku Mata biyu namiji daya matan Dame shekara Tara dame bakwai namijin HUDU yatafi biyar.... moreAslm Aunty don Allah ki boye sunana saboda akwai wadanda suka sanni a group dinnan.
Mu ukune a gurin mijinmu kowacce gdanta daban Ni mijina mutuwa yayi inada yara uku Mata biyu namiji daya matan Dame shekara Tara dame bakwai namijin HUDU yatafi biyar. Tun Yana shekara daya babansa ya rasu mahaifinsu yanada rufin asiri don yabarmu cikin sutura Amma kash rashin me kulawa duk sai komai ya watse sai gidanmu kadai shine yakai labari mukasa haya muke karbar dubu dari biyu duk shekara dasu nake biyawa yarana kudin makaranta da buqatun rayuwa.
Maza da yawa sun nemi aurena naqi sabida Allah yasani zuciyata tafi karkata Dana tsaya na tallafi rayuwar yarana rayuwa yanzu ta zama dolen yaya uwarsu, shekarata hudu a haka banyi aureba Ina yar sana'ata Ina kula da yarana a gidanmu kwatsam sai wannan bawan Allan yazo fam dinmu daya yayiwa mutane Romon kunne kan cewa zai riqemin yarana mutane suka rinqa cemin na aureshi hakadai banaso na aureshi,
Wlh yau shekara guda kenan nakasa samun farin ciki nace zan dauko yarinyata ko daya ce saboda aike yacemin Wai bayason harhardewa sannan Babu kulawa idan yatafi gurin matansa sai yayi sati biyu Bai waiwayeni ba dari biyar zaibani saidai inci kudina Kuma sana'ar ma neman hanani yakeyi tunda online business ne idan ansai kaya saina fita nakai tasha tunda bani da me kaimin.
Babbar damuwar wai sai yake cemin idan inason ya riqemin yarana saidai nabashi hayar gdanmu saina shiga na zauna sannan ya kawo nasa hudu daya rabu da uwayensu na hada na riqe kada ki manta na fada Miki komai ni nakewa kaina.
Nayi shawara da mahaifiyata tacemin ita dama tun farko tasan yaudarace bazai iya ba tunda shima bai iya riqe nasa ba basa karatu Babu suturar arziqi balle ya riqe na wani to Amma bazatacemin komai ba gdane dai bazaa bashiba domin ba biyan haya zaikeyi ba qarshe abin ya zama rigima ta rantsemin dama bani yakeso ba hangen ambarmin want abune ya kawoshi Kuma yaga Babu komai shine yake wulaqantani.
To yanzu haka tashin hankalin da nake ciki inada qaramin ciki wata biyu ga Babu kulawa abincin kirki Babu saidai maida yaji Kuma wlh ba Babu bace yanadashi kawai mugunta ce nidai na yanke shawarar zan sameshi na roqeshi ya sawwaqemin Kuma zan zubar da cikin kawai.
Aunty bazai riqemin yarana ba shikuma Yana burin kawomin nasa banci wahalar yarana ba naci wahalar nasa mgn ta Allah akwai zalumci bayyananne sannan gashi banida kwana fah a gdan sai sanda yaga dama yake leqoni yakwana daya ya tafi.
Please kuce wani Abu ko zanji sanyi shawara ta tsakani da Allah zaku bani wlh Ina cikin gagarumar matsala kullum gani akeyi nice banason riqe yarana kullum cikin kuka nake da nadama wlh na zabi sallama komi da kowa akan rayuwar marayu na abin tausayine mahaifinsu daya mutu bashida uwa bashi da uba balle nakaisu can gdanmu basuda hali abinda zasuci ma yakanyi musu wuya nikuma bawan Allan nan son kasheni yakeyi da baqin cikinsa idan ya kasheni yarana sun qara shiga garari wlh qanina jiya yake fadamin wataran haka suke tafiya makaranta Basu karya ba Babu abinda zaa Basu a gdanmu sanda Ina gdan kuwa duk lalacewa bana rasa abin basu yarana matane suna buqatata.
Wlh Ina rubutun Nan Ina kuka aunty less
Zinnira Muhammad\uD83D\uDE2DSo Sad zaluncin kam tabbasss ya ta'azzara gskiya rabuwar kawai shine maslaha domin ba halayya bace bare kace mutum zai daina, wannan quduri ne kawai, yaso kansa da ya kam \n\nMagana ta gaskiya ki nema saki ku rabu, ciki dai garki zubar domin... more\uD83D\uDE2DSo Sad zaluncin kam tabbasss ya ta'azzara gskiya rabuwar kawai shine maslaha domin ba halayya bace bare kace mutum zai daina, wannan quduri ne kawai, yaso kansa da ya kam \n\nMagana ta gaskiya ki nema saki ku rabu, ciki dai garki zubar domin bakisan Mai Allah zaiyi Nan gaba ba, yadda rayuwar Nan ta zama wlh kula da yayanki babu abunda yafishi Sai bautar ubangiji, domin idn suka lalace ke Zaki fi kowa Jin baqinciki. \n\nAllah yayi Mana mafita d muwafaqa
Ummyter Abdallah: aslm a naga wani post na mata datake maganar wankin,miji wlh tallahi nima naga illar iyama miji wanki,lkcn da ya aureni yana da mata da yara hudu mqtarsa bata masa wanki hk aka auroni dangin miji suka dunga zuganibakan nadunga masa wanki tunda ita bata... moreaslm a naga wani post na mata datake maganar wankin,miji wlh tallahi nima naga illar iyama miji wanki,lkcn da ya aureni yana da mata da yara hudu mqtarsa bata masa wanki hk aka auroni dangin miji suka dunga zuganibakan nadunga masa wanki tunda ita bata masa zaipi qaunata,wlh hk tunvina amarya nake masa wanki tapiya yapara tapiya bazo nai yaro daya bandaina b wataran ma baya bani na klin nazo naqara haihuwa na biyu wahala tapara qaruwarmun gashi kullum saiya cire kaya koh dakin kishiyata wankinsa suka taru hk zata kwaso ta jibgemin kayansa a pakin qopa idan na wanke kuma baida kunyar kwasan kayan yakai dakinta nace masa zan daina yace shi baida kudin dazai bada wanki da goga kuma wlh lkcn kapun ya aureni wanki yake kaiwa wlh abun.ya isheni gashi nima da.ciki hk zan tille nai masa wanki da goga 😭 nace yanxu ya raba mana nida kishiyata tqce wlh ban isa b duk narasa.wanki mapita zan dauka wlh dan allah nima kuban shawara🙏🙏 less
Auwalu Adamu Sabongida
Ba wani aibu cikin yiwa miji wanki, sai dai kawai ki ce ya kwatanta adalci yadda kike yi ita ma ɗayar ta yi ko kuma ke ma ya ɗauke miki.
Ummyter Abdallah: Assalamu alaikum Dan Allah kimin post ammaki boyesunana.
Inatareda saurayina muna mutuwarson junanmu amma wani lokachin innamai laipi yazagen ta uwata uba yatsinemin yaduken dagabaya saiyaban hakuri kuma wlh yanasona sosae, badama yaganni dawani ko yaga... moreAssalamu alaikum Dan Allah kimin post ammaki boyesunana.
Inatareda saurayina muna mutuwarson junanmu amma wani lokachin innamai laipi yazagen ta uwata uba yatsinemin yaduken dagabaya saiyaban hakuri kuma wlh yanasona sosae, badama yaganni dawani ko yaga number wani, hatta chatting yahanani, amma bukata ko ta 10k neyanamin bayakyashi, Dan kuban shawara yen uwa🙏🙏🙏inazaman jira.
Ali Aliyu Haruna
Assalaam alaikum warahmatullaah
Annabi (SAW) ya ce: "LALLAI NE JAMA'A SU HANU GAME DA BARIN JUMU'O'I, KO KUWA ALLAH ZAI RUFE ZUKATANSU, SA'AN NAN TABBAS ZA SU ZAMA CIKIN GAFALALLU".
{Muslim; 865}
Ya Allah du abin da zai hana mu zuwa Sallah ta juma'a, Allah ka nesanta shi damu, Allah ka yaye mana masifu ka karemu.
Ummyter Abdallah
(owner)
Madam din Dana kewa aiki jiya ta aikeni na sayo mata semo 2kg,danaje shagon sai na tarar sai 1 kg,so na dawo ban sayo ba shine tace min ni Wawa ne bana amfani da hankalina na sayo 1kg guda biyu ya zama 2kg Kennan idan an hada,na bata hakuri dai ta hakura,yau kuma tace na sayo mata slippers number 8,danaje babu sai lamba 4 shine na sayo lamba 4 guda biyu,na kawo batace komai ba Naga tana hada mini kayana cikin jaka,shine nake tambaya ko wanki zatayimin koko daki zata canjamin🤪🤪🤪
Rufaida Umar
(officer)
Ku je marubuta group kar garaɓasa ta wuce ku!