Rahmatu Lawan: Assalam alaikum. Barkanmu da jumma'a jama'a. A yau ma mun dora videonmu na 10 akan Microsoft Word. Ku duba ta menu a "Bidiyoyi" ko kuma ku duba profile nawa a gefen "videos" za ku same su. Sannan kuma za ku iya searching idan kun... moreAssalam alaikum. Barkanmu da jumma'a jama'a. A yau ma mun dora videonmu na 10 akan Microsoft Word. Ku duba ta menu a "Bidiyoyi" ko kuma ku duba profile nawa a gefen "videos" za ku same su. Sannan kuma za ku iya searching idan kun shiga gefen bidiyoyi da sunan Microsoft Word.
Rahmatu Lawan: Assalam alaikum, Technology Abokin Aiki group, kar ku manta za ku iya duba videos na mu na Microsoft Word daga menu sai ku je “bidiyoyi” sai ku yi scrolling down. Ko kuma ku shiga profile nawa a gefen videos za ku same su a jere.
Wannan zauren an bude shi ne domin kawo muku ire-iren technologies ko applications da za ku rika amfani da su domin samun sauki wajen ayyukanku na yau da kullum.
Mustapha Salmanu
Tun a farko-farkon shekarar 2016 ne
farashin kayayyaki ya fara tashin
gwauron zabi a Najeriya, al'amarin da ya
sa mutane suka shiga halin ha'u'la'i.
Farashin kayayyaki, musamman na abinci,
ya ta tashi ba kama hannun yaro, har ta
kai abinci na gagarar al'ummar kasar da
dama.
A dabi'ar dan-Adam, a duk lokacin da aka
shiga sabuwar shekara, ya kan dauka
matsalolin da aka fuskanta a shekarar da
ta gabata sun wuce ke nan sai a tarihi.
Amma a zahirin gaskiya ba haka batun
yake ba, don kuwa an yi dakon matsalar
hauhawar farashin, wadda aka fara cin
karo da ita a watan Fabrairun 2016,
zuwa sabuwar shekarar 2017, har ma
masana tattalin arziki na ganin muninta
ya fi na bara.
Hukumar kididdiga ta Najeriya ta fitar da
rahoto a karshen watan Disamban da ya
gabata, inda ta bayyana cewa farashin
kayayyaki ya ci gaba da tashi a watanni
11 a jere.
A watan Disambar ne farashin kayayyaki
ya tashi zuwa kashi 18.6 cikin 100 daga
kashi 9.6 cikin 100 a farkon shekarar ta
2016.
'Hasashen 2017'
Hukumar kididdigar ta kuma yi hasashen
cewa farashin zai ci gaba da karuwa
zuwa kashi 18.71 a watan Janairu, da
kashi 18.78 a watan Fabrairu, da kuma
18.84 a watan Maris din bana.
Najeriya: Mawuyacin halin tattalin
arziki
Sarki Sanusi ya ja hankalin Buhari
kan tattalin arziki
'Musabbabin hauhawar farashi'
Najeriya kasa ce da ke da dumbin arzikin
man fetur da ma'adinai, sai dai ta fi
samun kudin shigarta ne ta hanyar sayar
da man fetur din ga kasashen duniya;
hakan ya sa galibin kudin shigar da take
samu daga waje ke fitowa daga cinikin
man.
Tun a shekarar 2015 ne dai farashin
danyen man fetur din ya fara faduwa a
kasuwar duniya sakamakon yawan fitar
da shi da ake yi, don haka yawan kudaden
kasashen wajen da Najeriyar take samu
ya ja baya sosai.
Sakamakon haka kuma mutane,
musamman 'yan kasuwa, da ke shigo da
kayayyaki suka fara fuskantar matsala
wajen samun kudin musaya.
A duk kuwa lokacin da bukatar dala ta yi
yawa to farashin dalar kan karu ne a
hukumance da kuma a kasuwar bayan
fage.
'Fargaba'
Ko a wannan makon ma an yi samu
rahotanni daga bangarori daban-daban a
kan yiwuwar dorewar wannan yanayi na
tsadar rayuwa, da kuma kiraye-kiraye ga
gwamnatin Najeriya kan cewa ta dauki
matakan gaggawa don magance
matsalar.
Misali, wani kamfanin zuba jari mai suna
Afrinvest ya fitar da wani rahoto da ke
cewa farashin kayayyaki zai ci gaba da
hauhawa cikin hanzari a shekarar 2017
saboda yiwuwar kara farashin
makamashi da kuma rage darajar kudi.
Ita ma kungiyar kwadago ta kasa, NLC, ta
koka da yadda ake ci gaba da rufe
masana'antu, al'amarin da ke jawo rashin
aikin yi da tsadar kayan abinci da na
bukata.
Shugaban reshen kungiyar na jihar
Anambra ya ce, ''Albashin ma'aikata -
wanda dama bai taka kara ya karya ba - a
yanzu haka ba ya isa su sayi abinci balle
sauran kayan bukatu.''
Shi ma jagoran jam'iyyar APC mai mulki
kuma tsohon gwamnan Lagos, Asiwaju
Bola Tinubu, ya yi irin wannan korafi,
inda ya yi kira ga gwamnatin tarayya da
ta gaggauta daukar mataki.
Wani shahararren mawakin kasar ma,
wato TuFace Idibia, ya yi kira ga 'yan
Najeriya da su mara masa baya a zanga-
zangar lumana da zai gudanar a watan
Fabrairu don yin kira ga gwamnati ta san
na yi a kan wannan batu.
'Halin ha'u'la'i'
Wannan al'amari ya jefa mutanen kasar
cikin halin ka-ka-ni-ka-yi, har ta kai sun
fara sukar gwamnatin Buhari da gazawa
wajen cika alkawuran da ta yi na inganta
abubuwa.
A wata muhawarar da Sashen Hausa na
BBC ya shirya a shafinsa na Faceebook
a kan ko an fara samun sauyi a halin da
ake ciki na tsadar kayayyaki ko kuma da
sauran rina a kaba, mutane daga sassan
kasar daban-daban sun bayyana cewa,
'har yanzu ba ta sauya zane ba.'
Mafi yawan mutanen sun bayyana cewa
'a kulliyaumin farashin kaya kara hawa
yake ba ya sauka.'
Ga kadan daga cikin sakwanni da mutane
suka rubuta mana:
Shafi'u Abdu: "Gaskiya talaka yana cikin
mawuyacin hali sakamakon wannan
yanayi. Allah dai ya kawo mana mafita"
Haruna Boda Inkaibi: "A nan jiharmu ta
jigawa ma haka matsalar take; babu wani
abu mai sauki, batirin rediyo da muke
saya N60 a da, yanzu N120 ne".
Bawa Abdullahi Maska: ''Farashin kayan
masarufi ya kan tashi kusan kullum, idan
ka sayi batir a kan naira 50 ba mamaki
gobe ka ji an ce maka ya koma N60,
kuma mun rasa inda laifin yake - a wurin
'yan kasuwa ne ko kuwa kamfanonin da
ke sarrafa kayan masarufin ne?"
Mustapha Ibrahim Dan Malumfashi:
"Rayuwarmu a yanzu ta yi wahalar
gaske, saboda hauhawar farashin kaya,
abin da ka saya yanzu a kasuwa, idan ka
kai shi gida, ka dawo ka sake sayensa, to
tabbas sai ka ji ya kara kudi maimakon ya
rage. Gwamnati ba ta yin komai a kan
hauhawar farashi saboda talakawa ne
abin yake shafa."
Ahmed Elrufai Girei: "Gaskiya daya ce: ko
ina a Nigeria komai ya yi tsada, yadda
ake maganar nan gaba kadan komai zai yi
sauki ba abin da ya sauya, haka
abubuwa suke ta hauhawa don Allah ta
ina talaka zai samu saukin rayuwa ne?"
Farashin wasu abubuwa a watan
Janairun 2016 zuwa Janairun 2017
Buhun shinkafa babba N8000 -
N19,500
Buhun Semovita N1,300 - N3000
Buhun fulawa N6,000 - N12,000
Kwanon dawa - N140 - N600
Kwanon wake N400 - N800
Kwanon sikari N400 - N900
Indomie N35 - N70
Tulun gas matsakaici (kilo 12.5)
N2,500 - N5,300
Litar kananzir N100 - N500
'Ina mafita?'
Masana harkar tattalin arziki sun yi ta
tsokaci a kan hanyoyin da za a bi a
shawo kan wannan matsala da take sake
gawurta.
Daga ciki akwai batun cewa dole babban
bankin kasar, wato CBN, ya tsara wasu
manufofi don tallafawa manoma da
bangaren masana'antu da rance mai
kudin ruwa kadan.
Kamar dai yadda Dokta Obadiah Mailafiya,
wani tsohon mataimakin gwamnan
babban bankin na Najeriya yake cewa,
"Dole gwamnati ta tallafa wa manoma da
isasshen taki da kayan aikin gona na
zamani don magance matsalar hauhawar
farashin abinci.''
Ya kuma ce akwai fargabar halin da za a
shiga ciki nan da watanni biyu masu
zuwa sai ya fi wanda ake ciki a yanzu
muni.
"Daga nan zuwa watan Maris da Afrilu
kudin abinci zai rubanya fiye da yanzu,
saboda manoma ba su da isassun kayan
bukata don noma da kuma yawan tashe-
tashen hankulan da ke sa musu fargabar
zuwa gonar,'' in ji shi.
Da yake magana a kan CBN kuwa cewa
ya yi:
Dole a dinga martaba manufofin
babban bankin.
Dole kasuwar musayar kudi ta zama
daya, saboda ana samun
almundahana a wannan bangaren
idan ya kasance akwai kasuwannin
musayar kudi biyu a kasa.
A hanzarta kashe kudaden da aka
ware don gudanar da ayyuka
wadanda za su inganta rayuwar
al'umma da kuma samar da ayyukan
yi.
Haka kuma wasu masanan da dama na
gargadin gwamnati cewa kada ta yi wani
tunani na kara kudin harajin da take
karba daga mutane.
Wannan ita ce matsalar hauhawar
farashin kayayyaki mafi girma da aka
samu a Najeriya cikin shekara 10 da ta
gabata.
A yanzu dai a iya cewa 'yan Najeriya sun
zuba ido don ganin ko gwamnati za ta
dauki matakan shawo kan wannan
matsala kafin shekarar nan ta yi nisa ko
a'a.BBCHAUSA