Bakandamiya
(Admin)
GORON JUMMA'A
Assalamu alaikum Malam,
Mutum ya rasu sai ya bar yayye biyu maza, da yayye mata wadanda suke uba daya, da kuma mahaifiyar sa, ya za a raba musu gadon?
Amsa:
Wa alaikum assalam,
Za’a raba dukiyar kashi shida, a bawa uwa kashi daya, ragowar kashi biyar din a bawa yan'uwa su raba, namiji ya dauki rabon mata biyu.
Amsawa:
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
Daga zauren Fatawowin Rabon Gado Guda 212
Rahmatu Lawan
GORON JUMMA'A
INA YAWAN FITAR DA MANIYYI SABODA MIJINA BA LAFIYA
Tambaya:
Assalamu Alaikum , Dr macece mijinta ba yada lafiyan aure tsawon lokachi, sai ya zamana tana yawan releasing ba sai tayi wani dogon tunani na sha'awaba, ya matsayin ibadarta yake?
Amsa:
Wa alaikumus salam
To gaskiya abin da yake daidai shi ne: ya nemi magani, in kuma bai samu ba, ana iya raba auran, tun da yana daga cikin manufofin aure, katange ma'aurata daga fadawa haramun, kamar yadda shararren hadisinnan ya tabbatar.
Yawan fitar maniyyi zai iya zama lalurar da za ta iya haifar da saukin sharia, saidai na ki ba zai zama lalura ba, saboda iyayenki za su iya wajabtawa mijin neman magani, in kuma bai samu ba, za ku iya rabuwa, Allah ya azurta kowa dağa falalarsa.
Cigaba da zamanku a wannan halin yana iya jefa ki cikin hadari, mata nawa ne suka zama mazinata ta hanyar wannan sababin?
Ya wajaba ki yi wanka duk sanda maniyyin ya fita, tun da ya fita ne ta hanyar jin dadi.
ALLAH NE MAFI SANI
Daga zauren Filin Fatawa na Dr. Jamilu Zarewa
12/6/1437
yusus Ahmed
#wakokiEven though, that time lagos has 43 local
government councils with 16 million population. so I dont thing is fair to
judge 16 million people with just 500 respondents