
Loading ...
-
-
????????*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*????????
♻♻ *PWA* ♻♻
_08185819176_
••••••••••••••••••••••••••••••
????????????????????????????
*BIRNIN... more????????*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*????????
♻♻ *PWA* ♻♻
_08185819176_
••••••••••••••••••••••••••••••
????????????????????????????
*BIRNIN SAHARA*
????????????????????????????
••••••••••••••••••••••••••••••






_______
*ѕtσrч/wríttєn ву✍????:*
????????
*_Haiman Raees_*
(℘ᾰ❡ḙ 02)
_______
Bayan wani ɗan lokaci sai ta buɗi baki a cikin Sassanyar Murya tace dani: '' Barka da zuwa Birnin Sahara yakai Haiman! kasani cewa abin alfahari ne kasancewar wanzuwarka a cikin wannan Birni namu mai albarka!'' Nayi ajiyar zuciya sakamakon jin kalamanta domin na fahimci cewa akwai yiwuwar zan iya samun damar barin wajen Lafiya. Amma duk da wannan tunani da nayi, hakan bai hanani tambayarta abinda ke damuna ba, ''Diana ina ne nan? Na tambayeta yayinda na dai daita yanayin fuska saboda kada ta fahimci wani abu dangane da abinda ke damuna.
''Birnin Sahara kenan, kuma nan inda muke yanzu shine gidan da ake baiwa jarumaina horon yaki. Ta bani amsa. ''ehmm Jarumanki fa kika ce? Kina nufin duk waɗannan Samudawan a ƙarƙashinki suke? Na tambaya cike da mamaki. ''hahaha ta fashe da dariya, ta ci gaba da dariyarta har saida ta gaji sannan sai tace dani: ''tabbas waɗannan jarumai suna ƙarƙashina ne kuma ko rabin su ma baka gani ba, kuma su sun kasance masu biyayya tare da girmamawa a gareni kasancewata sarauniya a gare su.
'' ''Oh! Wai dama ke sarauniya ce? Na tambaya ina mai riƙe ƙugu tare da girgiza kai, to amma me yasa baki taɓa faɗamin ba? ''kai!!! Wani garjejen ƙato ya daka min tsawa yana mai nuna ni da wani ƙaton mashi wanda saboda kaifi har walƙiya yake a cikin hasken rana. Na ɗanja da baya sakamakon ganin wannan al'amari, amma bisa mamaki na sai naga Diana ta bashi umurnin ya ƙyaleni. ''Haiman ka sani cewa ni sarauniya ce mai ƙarfin iko, don haka ka kyautata kalamanka a gareni, in kuwa ba haka ba to zaka fuskanci hukunci mai tsanani irin wanda baka taɓa fuskantar kamarsa ba. Diana ce tayi wannan furuci.
''to naji Sarauniyarsu, yanzu mene dalilin kawo ni nan? Na tambayeta cikin alamun jin kai da taƙama. ''hmm tayi ajiyar zuciya sannan taci gaba da cewa: na fuskanci har yanzu kana tantamar girman sarautata don haka ina mai baka Shawara da ka ajiye zafin kanka kayi biyayya domin nan fa Birni na kake in kuma ba haka ba zan nuna maka cewa da dayanzu ba ɗaya bane'.
SARAUNIYA Diana ce tayi wannan Furuci. Ko da jin haka, sai nima na bushe da dariya irin ta keta, bayan nayi ta ishe ni, sai na Kalli Diana ido cikin ido na ce da ita: "Amma lallai na lura cewa kwakwalwar ki ta samu matsala, yanzu in banda tsabar rashin adalci da tsantsar Mugunta, ta yaya za'a yi ki Sato mutum daga gidan su ki kawo shi wannan rairayin kuma kice kina bukatar yayi miki biyayya? Kuma ki rasa Wanda ma zaki yiwa hakan sai ni? Shin Kin manta cewa ni ruwa ne bana son takura? Lallai ya kamata ki sake tunani, domin abinda kike tunani ba fa zai yiwu ba". Wadannan kalamai nawa ba karamin batawa Diana rai suka yi ba domin tunda na fara dariya ta naga ta turbune fuska, ai kuwa ina gama wannan jawabi nawa sai Sarauniya Diana ta kalli wadannan Lafta laftan Samuwadan a fusace tace da su: "Ku kamashi ku kaishi kurkuku! Nan take suka nufo kaina da nufin su yimin Kamun kazar Kuku...
Zan Ci Gaba In Shaa Allaah.
_*Phone:*_
08185819176
_*Web:*_ www.haiman.com.ng
_*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees
_*Twitter:*_ @HaimanRaees
_*Instagram:*_ Haimanraees
_*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
????????*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*????????
♻♻ *PWA* ♻♻ less
-
????????*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*????????
♻♻ *PWA* ♻♻
_08185819176_
••••••••••••••••••••••••••••••
????????????????????????????
*BIRNIN... more????????*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*????????
♻♻ *PWA* ♻♻
_08185819176_
••••••••••••••••••••••••••••••
????????????????????????????
*BIRNIN SAHARA*
????????????????????????????
••••••••••••••••••••••••••••••






_______
*ѕtσrч/wríttєn ву✍????:*
????????
*_Haiman Raees_*
(℘ᾰ❡ḙ 01)
_______
Na buɗe idanuwana a hankali yayinda hasken rana yake ƙoƙarin sani in rufesu. Cikin yanayin dagewa nayi yunƙurin tashi daga kwanciyar da nake amma sai abu ya faskara, domin kuwa ji nake tamkar an ɗauramin dutsen
# kwatarkwashi a ƙirjina.
Koda yake ina cikin hayyacina , amma sai kuma
gaɓobina suka kasa amsar umurnin da zuciyata take basu na su miƙe tsaye.
Tambayoyine sukayimin kwayam a cikin kwakwalwata a dai dai wannan lokaci; A ina nake? Me ya kawo ni nan Kuma ya akayi nazo nan?'' Waɗannan tambayoyine da bazan iya baiwa kaina amsar su ba. Na runtse idanuwana tsawon kimanin daƙiƙu talatin ina mai karanta kalmar shahada tare da yiwa Annabi S.A.W Salati, aikuwa ina buɗe idanuwan nawa sai abin mamaki ya faru domin nan take naji duk wata gajiya ta kau daga jikina tamkar a mafarki. Na miƙe tsaye yayinda na ke duban hagu da dama na.
A wani babban fili na tsinci kaina mai cike da rairayi, ga dukkan alamu dai a sahara nake. Filin a zagaye yake da wata irin murtikekiyar katanga mai matukar kauri da kuma Tsawo, yayinda a gefe ɗaya kuma wasu 'yan ƙananan gidaje ne masu kama da bukkoki. Gaba gare ni kuma wasu ɗirka_ɗirkan mutane ne masu kama da samudawa. kaida ganinsu kaga ƙarfafa. Ko wanne daga cikinsu sanye yake da wata baƙar riga ga kuma zabgegiyar takobi riƙe a hannun sa. Dakarun zasu kai kimanin dubu da ɗoriya. Nayi matuƙar mamakin ganina a wannan wurin, domin abun da zan iya tunawa shi ne, kwanciya bacci a daki na da nayi. Na ɗanyi taku ɗaya da nufin yin 'yar tafiya. Aikuwa sai waɗan nan dakaru suka zare takubbansu da nufin haiƙe min. Cak!
Zan Ci Gaba In Shaa Allaah
_*Phone:*_
08185819176
_*Web:*_ www.haiman.com.ng
_*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees
_*Twitter:*_ @HaimanRaees
_*Instagram:*_ Haimanraees
_*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
????????*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*????????
♻♻ *PWA* ♻♻ less

Loading ...
There are no more results to show.