Abba Abubakar Yakubu : Yawaitar Kashe Kashe Da Garkuwa Da Mutane A Arewa Abin Ɗaga Hankali Ne... Cewar Marubutan Arewa
Daga Abba Sani Pantami... moreYawaitar Kashe Kashe Da Garkuwa Da Mutane A Arewa Abin Ɗaga Hankali Ne... Cewar Marubutan Arewa
Daga Abba Sani Pantami
Cikin mako guda 'yan bindiga sun kashe kimamin mutanen da ba za su kirgu ba, a jihohin da ke yankinmu na Arewa, tare da garkuwa da mutane masu yawa da zummar karɓar kudin fansa.
Wannan ta'addacin da 'yan ta'addan suke yi wa al'ummar yankin mu ya shafi jihohi da dama a yankunan Arewa, da suka hada da Jihar Kaduna, Zamfara, Katsina, Sokoto, da wasu ɗaiɗaikun jihohin ga ta'addacin Boko Haram da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a yankin Arewa maso gabas.
Ta'addacin da ake yi wa al'ummar yankin Arewa a waɗannan jihohi ya yi matukar muni, ana bin su har gida ana kashe wa tare da ƙona wasu da ransu, ana salwantar da dukiyoyinsu da rayukan da su ba su ji ba basu gani ba, a musamman a wasu yankunan na jihar Zamfara. An hana wasu mazauna ƙauyuka da yawa zuwa gonakinsu matukar ba su biya 'yan ta'addan wasu kuɗaɗen da suka nema ba.
Haka zalika masu garkuwa da mutane don biyan kudin fansa sun addabi hanyar Abuja zuwa Kaduna da wasu jihohi, wanda a ranar Litinin da ta gabata sun kama dalibai masu yawa, tare da neman kudin fansa kimamin kudin da ya kai Naira miliyan 270.
Da wannan ne ƙungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani ta "Arewa Media Writers" ke kira ga gwamnatin tarayya da Majalisar Gwamnonin Arewa, da su gaggauta ɗaukar matakin kawo ƙarshen ta'addacin dake faruwa a jihohin su, don al'ummar yankin mu na Arewa su zauna lafiya.
Fatan mu har kullum shine Allah ya kawo wa Arewa zaman lafiya mai dorewa. Amin
*Kwamred Abba Sani Pantami, shi ne shugaban ƙungiyar Arewa Media Writers na ƙasa, ya aiko da wannan rubutu ne daga Jihar Gombe less
Daga Abba Abubakar Yakubu... moreHANKALINKA JAGORANKA: Kowa Ya Ci Zomo Ya Ci Gudu...
Daga Abba Abubakar Yakubu
Rayuwar dan Adam cike take da buri iri daban daban, bukatu da hasashen yadda yake kwadayin ya ga rayuwar sa ta kasance. Komai yawan shekaru, arziki, ilimi ko matsayin mutum a rayuwa ba ka raba shi da buri. Masana ilimin falsafa na cewa, buri shi ne adon dan Adam. Shi ne abin da ke samar wa rayuwar sa manufa, hadafi da makoma mai kyau ko marar kyau.
Burin yaro ya girma ya kai matsayin yanke hukunci da yin abu bisa zabin sa. Dalibi yana burin ganin ya gama karatu a kowanne mataki yake, domin ganin ilimin da ya samu ya taimaka masa a rayuwa ya zama mai amfani da iliminsa wajen cin guminsa. Mai arziki na son dukiyarsa ta karu har a rika lissafinsa cikin manyan masu arziki, ko kuma ya kai ga wani mataki na mulki da samun karfin iko. Haka shi ma mai mulki kullum burin sa ya samu karfin iko da fada a ji har ya kai ga matakin da kowa shi yake kallo yake koyi da karbar umarni.
Ni da kai duk muna da buri, walau na zahiri ko na badini. Ko da yake ba lallai ne bukatu da burikan mu su zama daya ba, saboda kowanne dan Adam daban Allah ya halicce shi, kamar yadda masu ilimin zanen yatsun mutane suke cewa.
To, amma shin mun kama hanyar cimma wannan burin namu kuwa? Ta wacce hanya muke ganin za mu kai ga burin mu na rayuwa? Shekaru nawa muka dibar wa kan mu har mu kai ga cimma nasara a burin da muka sa a gaba? Wanne irin buri muka sa a ran mu da muke ganin zai kai mu gaci? Akwai wani abu da muke ganin yana da tasiri ga cimma burin mu, amma ba mu kai gare shi ba?
Wadannan tambayoyi da wasun su ya kamata mu rika yi wa kan mu, don ganin sun zama mana alkibla ga hadafin mu na rayuwa. Kowanne buri yana da matakin kai wa gare shi, kamar tashar mota ce, kowacce akwai garin da ta nufa. Wanda zai je Kano ba zai shiga motar Sakkwato ba. Wanda ke neman ruwa ba zai hau bishiya ba.
Idan burinka samun ilimi ne to, makaranta za ka shiga. Haka kuma idan burinka zama babban dan kasuwa ne to, sai ka kama hanyar kasuwa ka fara saye da sayarwa.
Kowacce harka akwai matakin da ake hawa kafin a kai gare ta. Kuma ba za ka cimma abin da ka ke buri ba har sai ka nemi sanin matakan da ya kamata ka taka daki daki, har bukatar ka ta biya. Babu abin da ake samu tashi daya sai an neme shi, kuma an bi hanyar da za ta kai mutum gare shi, ko da kuwa kofi ne a gabanka za ka sha ruwa sai ka mika hannu ka daga kafin ya kai bakin ka.
Matakin farko na cimma nasara a rayuwa shi ne mu gano burin da muke da shi, da abin da za mu yi da wannan abin da muke nema, idan mun kai gare shi. Sanin yadda za mu isa ga cimma burin mu wani babban kalubale ne a gare mu, kuma shi ne mabudin samun nasara ga bukatun mu.
Wani lokaci idan ana maganar yadda ya dace mu yi wa rayuwar mu tsari da linzami, don tsayawa a kan turba ba tare da wani abu ya dauke hankalin mu ko shagalar da mu daga fuskantar abin da muka sa a gaba ba. Wasu na ganin kamar tsawwala wa rai ne, domin a ganin su komai tsarin ka, sai Allah ya yarda za ka zama abin da ka ke so ka zama, ko kuma kaddara ta canza maka manufa. Amma kuma suna manta cewa, Allah madaukakin sarki da kansa ya ce, idan ka yi harama to, ka mika al’amuranka gare Shi. Ba zai yiwu a ce mutum ya je kasuwa sayen gishiri sai ya sayo goro ba!
Mai ka ke so ka zama a rayuwarka? To, yi haramar bin hanyar da za ta kai ka gare shi. Ba a kama zomo daga zaune! less
Abba Abubakar Yakubu : HANKALINKA JAGORANKA: Kowa ya gyara ya sani, kowa ya bata ya sani
Daga Abba Abubakar Yakubu... moreHANKALINKA JAGORANKA: Kowa ya gyara ya sani, kowa ya bata ya sani
Daga Abba Abubakar Yakubu
Karin maganar da aka yi amfani da shi a kanun wannan rubutun kadai ya isa ya fahimtar da mai karatu ya sani cewa, duk abin da mutum ya aikata a rayuwarsa, alheri ko sharri, kansa ya ke yi wa ko da kuwa yana tunanin kai tsaye abin da ya aikata wani ya shafa ba shi ba.
Abin mamaki ne ka ga wani ya zauna ya shirya yadda zai cutar da wani ta hanyar kulla sharri, ko yaudara ko munafurci, don dai shi ya amfana da dan wani abu da bai taka kara ya karya ba, ko kuma don ya raba wancan da wata ni'ima ko alfarma da yake samu. Irin wadannan mutane ne Allah ya cikin Alkur'ani mai girma ya ke ambaton su da masu nuna bakin ciki ga aikin alheri, ko kuma wadanda suke da mugun kulli (na cuta) a zukatansu, ba sa son ganin cigaban wani a rayuwa in ba su ba.
Wata rana na shiga kasuwa ina tafiya, sai wata mata mai alamun tabin hankali ta gifta ta kusa da ni, tana tafe tana sambatu. Caraf, sai kunnena ya jiyo min tana fadin, "Don Allah ku gyara halinku..." tana fada tana maimaitawa ba tare da ta damu ko akwai wanda yake sauraronta ba. Wadannan kalamai da matar ke fada sun yi matukar sanyaya min jiki, yayin da kwakwalwata ta shiga dawurwura game da sakon da wannan baiwar Allah take fada, masu kama da wa'azi da nasiha.
Babu shakka ba a kasuwa kadai ba, hatta a ofisoshin gwamnati, ma'aikatu, unguwanni da gidajen mu, akwai bukatar mu rika tunatar da junan mu, don Allah mu gyara halin mu. Saboda gaskiya akasarin mu halayen mu ba su da kyau, a wajen mu'amala, cinikayya, zamantakewa, da auratayya, wasu da dama tunanin su shi ne yadda za su zalunci wani, ko su kware shi ko ma su kuntatawa rayuwarsa.
Abin har ya kai ga ko mutum rantsuwa ya yi maka kana kokwanton gaskiyarsa, maimakon ka samu natsuwa sai ka ji ka fara wasiwasin anya abin da ya fada din nan kuwa haka ne.
Yaudara, algus da rantsuwar karya sun yi wa mutane yawa, ba a gane mai gaskiya daga kamalar fuskar sa, gemu ko hijabin da ta ke sanye da shi.
Akwai wata kabila a kasar Sudan da aka ce idan za su yi rantsuwa sai dai su ce, 'Alhaji' suna nuni da ubangijin Alhaji. Asalin hakan kuwa an ce, sun taba zama ne da wasu Hausawa Musulmi masu tsananin gaskiya da rikon amana, wadanda suka yada zango a garinsu kan hanyar su ta dawowa daga aikin Hajji. Saboda tsananin yardar da suka nuna wa wadannan bakin nasu ne aka ce, idan za su yi rantsuwa sai su ce, 'Alhaji' domin bayyana kurewar gaskiyar su.
Amma abin takaici ne yau a kasar Hausa garin Musulunci ka ga Musulmi yana ta rantse rantse a kan karya, don wani abin duniya kalilan da zai samu. Babu kunya, babu tsoron Allah.
Har ma ya zama jiki a wajen 'yan siyasa su rika fadar abin da har ga Allah sun san karya suke yi, kuma masu sauraron su ma sun gane ba gaskiya suke fada ba, amma tunda haka abin ya ke duk sai a tafi a haka kawai. Ko da kuwa an san wanda aka zaba ba mutum ne mai halayen kwarai ba, amma jama'a sun gwammaci su zabe shi don kwadayin abin da za su samu a wajen sa. Duk kuwa da sanin cewa, hukumomin gwamnati suna zarginsa da cin amanar kasa ko almundahana da dukiyar al'umma.
Mutane sun canzawa ha'inci, rashawa, da cin amana suna zuwa ga kalmomi masu kyau na alheri, alfarma, rufin asiri da sauran su. Saboda nuna cewa, babu wata matsala don mutum ya yi rantsuwa ba a kan gaskiya ba, ko don mutum ya karkatar da wasu kudade da ba nashi ba.
Nijeriya ta taba zama kasar da ta fi sauran kasashen duniya yawan ayyukan cin hanci da rashawa, a lokaci guda kuma kasar da ta fi sauran kasashe riko da addini. Kenan a nan kishin addinin mu da ikirari da aiki da sunna ba su hana mu aikata laifuka da suka sabawa koyarwar addinin da muke bi ba. Duk kuwa da sanin cewa akasarin halayen da muke nuna wa a zamantakewar mu ta yau da kullum ba su dace da mutanen kwarai ba.
Akwai wasu malamai da ke fada cikin wa'azin su cewa, Allah yana ba mu shugabanni ne gwargwadon irin halayen mu. Don haka ba za mu ga canji a rayuwar mu ba, har sai mun canza halayen mu. Mun kiyaye dokokin ubangiji, mun kyautata alakar mu da jama'a, mun tausayawa na kasa da mu, mun yi hani da mummuna, mun yi umarni da kyakkyawa.
Ya kamata mu ji tsoron Allah, mu nisanci duk wani abu da zai bata mana suna, ya kuma sa mu cikin fushin ubangiji. Abin da muke fada da harsunan mu ya zama haka yake a zukatan mu har ga Allah. Mu sani cewa, za a yi mana hisabi, kuma mala'iku suna rubuta dukkan ayyukan da muke aikata wa a zahiri da boye! less
Abba Abubakar Yakubu... moreHANKALINKA JAGORANKA: Babu Maraya Sai Rago...
Abba Abubakar Yakubu
Wani lokaci idan ka ji mutum na kukan talauci da kuncin rayuwa, za ka yi mamakin yadda wasu ke samun kansu cikin wannan hali, duk kuwa da kasancewar yana da cikakkiyar lafiya, kuruciya da damarmaki da yawa da suke kewaye da shi, wadanda zai iya duba wanda zai iya samu ko za ta dace da yanayinsa.
A nan ba wai ina musun babu talauci ba ne, kwarai jama'a da dama na rayuwa cikin talauci, amma wasu daga cikin su rashin abin yi da mutuwar zuciya ce ta sanya su cikin wannan hali.
Babu yadda za a yi kana zaune arziki ya biyo ka har gida ya same ka, sai ka fita ka nema. Ko Allah ma ya ce bawa tashi in taimake ka, kamar yadda masu azancin magana ke cewa.
Abin takaici ne, ka ga matasa majiya karfi sun kashe zuciyar su, saboda gadarar sun yi karatu ko suna da iyaye masu hali, suna samun abin da za su ci, ka gan su zaune a gefen hanya suna labarin wasu manyan masu arziki, ko manyan motoci da ke wucewa, da bin gangamin 'yan siyasa suna yawon jagaliya, ba tare da nuna kishin zuciyarsu ba.
Kai ma za ka iya zama babban mai arziki, ko babban jami'in gwamnati, ko babban dan siyasa, ka gina babban gida, ka hau babbar mota, idan ka nuna juriya da hakuri, kuma ka bi hanyar da shi ma wanda ka ke wa fadanci ya bi.
Idan ka zauna ka yi tunani za ka iya gano wata hikima ko basira da kai ma Allah ya yi maka da idan ka mayar da hankali a kan ta za ka samu nasara a rayuwar ka. Wata sana'ar wani ka ke bukata ya nuna maka inda za ka yi cinikin kayan ka samu riba mai yawa, wani lokaci jari ka ke bukata ka fara juya wata harka da za ka amfana, idan karatu ne ba za ka rasa wanda zai taimaka maka ka koyi darasin da yake ba ka wahala ba, ko ya yi maka bitar abin da ka manta, don ka samu ka ci jarabawa. Babu wanda aka haifa da kai biyu ko kwakwalwa biyu. Kai ma Allah ya yi maka taka baiwar, gano ta ne kawai ba ka yi ba.
Ya zama dole a daidai wannan nan in yabawa gwamnatin tarayya da ta jihohi da suke bullo da tsare tsare iri iri, domin tallafawa mata da matasa da hanyoyin da za su samu sana'o'in dogaro da kai, don yaki da talauci da zaman kashe wando. Kuma babu shakka irin wadannan shirye shirye sun amfani jama'a da dama, wasu sun samu sana'a, wasu sun habbaka jarinsu, wasu sun samu ayyukan yi, sun daina bani bani, da rokon 'yan uwa da abokan arziki.
Tallafin dubu goma goma da shirin NPowar na gwamnatin tarayya sun taimaka sosai, kuma in har da zai dore a haka, 'yan Nijeriya da dama za su kubuta daga takunkumin talauci da zaman banza. Haka ma gwamnatocin jihohi a wasu sassan sun kafa tsare tsare na koyar da sana'o'i da ba da kayan sana'a har da jari ga masu karamin karfi.
In da gizo ke sakar shi ne, shin wadanda aka tausayawa suka samu sana'a da jari, za su yi tattalin dan abin da suka samu har ya bunkasa kuwa, ko kuma sa wa a gaba za su yi su cinye don ba gumin su ba ne!
Idan har muna kukan talauci da rashin galihu, sai wani dan uwa ko mai hali a makwafta da 'yan siyasa suka yi mana hanyar samun wannan jari ko tallafi, ya kamata mu ma mu tausayawa kan mu mu yi tallalin abin da muka samu, domin wasu ma su amfana da mu, kuma al'umma ta rage yawan masu zaman banza.
'Yan kasuwa da masu kananan sana'o'i sune kashin bayan bunkasar al'umma, domin hatta gwamnatoci da su take alfahari har ma take neman jari a hannun su.
Marigayi Dakta Mamman Shata Katsina ya yi wata waka mai taken, 'Ku tashi mu farka 'yan Arewa' inda a ciki ya kira matasa da sauran al'umma mu daina barci da zaman banza, saboda kwadayin samun arziki da albarkar rayuwa.
Masu azancin magana dai na cewa, babu maraya sai rago! less
Halayen kwarai ababen koyi daga rayuwar manzon Allah... moreHANKALINKA JAGORANKA:
Halayen kwarai ababen koyi daga rayuwar manzon Allah 🌙
Watan Rabi'ul Awwal shi ne wata na uku a cikin shekarar Musulunci, kuma a cikinsa ne aka haifi fiyayyen halitta Annabi Muhammad, mai tsira da aminci. A watan ne kuma Musulmi mabiya koyarwar darikun Sufaye suke gudanar da tarukan Mauludi, don murna da kewayowar watan haihuwar manzon Allah (SAW).
Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW) shi ne ya kasance cikamakin annabawa da manzannin da Allah ya aiko da sakon shiriya ga al'ummomin duniya, domin kyautata rayuwarsu da makomarsu, a lahira. Bayan kasancewarsa Manzo kuma Annabi, duniya ta shaida Muhammad dan Abdullahi a matsayin amintaccen mutum mai kamala da halayen kwarai, wanda ba a taba sanin sa da wani mummunan abu ba. Duk da kasancewar ya tashi maraya a hannun raunanan mutane masu karamin karfi, amma duk wanda ya rabe shi yana kasancewa cikin ni'ima da albarka mai yawa.
Tun yana dan karami ake yi masa lakabi da 'Al-Amin' wato amintacce, saboda gaskiya da rikon amanarsa. Haka ya girma a matsayin matashi mai cike da kwarjini, natsuwa da jarumta, wanda kowa ke sha'awarsa.
Ko a lokacin fara bayyanar da sakon Musulunci da Allah madaukakin sarki ya aiko shi shugabannin larabawa da mabiyansu sun shaida shi mutumin kirki ne da ba a san shi da karya ba, kuma ba a zaton zai zo da wani abu wanda ba gaskiya ba.
Dukkan mu'amalarsa da mutane, a gida da waje, ta kasance abar yabawa. 'Yan uwansa na jini da na nesa, iyalansa da sahabbansa duk sun shaida yadda yake karfafa zumunci, tsare gaskiya da kiyaye hakkokin iyalinsa da na sauran jama'a. Ba ya cin amanar kowa, ba ya zaluntar hakkin kowa, a fili ko a boye, kuma ba ya yarda da tauye hakkin wani.
Ya zo a cikin hadisi cewa, ma'aikin Allah mai girma da daukaka yana fadin, an aiko shi duniya ne domin ya cike kyawawan dabi'u, don jama'a su yi koyi da su a rayuwarsu, ta yadda duniya za ta samu kamala ta cika da haske da zaman lafiya.
Malamai masana tarihi sun yi rubuce rubuce da bayyana wa a cikin karatuttukan su irin yadda ma'aikin Allah ya rinjayar da zukatan wadanda a baya kafirai ne, amma saboda kyawun dabi'unsa, tausayinsa da tsare gaskiyarsa, suka karbi Musulunci kuma suka sadaukar da rayuwarsu wajen daukaka shi da kare shi.
Musulunci ya samu daukaka da kwarjini a idon duniya ne ba domin kaifin takobi ko mamayar Musulmi ba, sai don kyakkyawar mu'amala da gaskiya da adalcin mabiyansa.
Abin dubawa a nan shi ne shin har yanzu akwai irin wannan yarda da aminci da ake sha'awa daga Muhammadawa masoya manzon Allah (SAW)? Mai ya faru har rayuwar Musulmi ta zama abin tozartawa da kyama, bayan yana da kyakkyawan abin koyi da ya haskaka duniya da kauna da aminci? Gaskiya, adalci da rikon amana sun yi rauni a wajen Musulmi, mun yi sake da kyawawan darussan da ake koyar da mu na rayuwar fiyayyen halitta. Mun koma rayuwa irin ta marasa addini, da mu ake hada baki a cutar da dan uwan mu, ba ma karfafa zumunci, babu kishin kasa, masu kishin addini muna yi musu kallon 'yan mayar da hannun agogon baya, marasa wayewar kai.
Abin sha'awa ne yadda dafifin matasa maza da mata suka rika fitowa cikin kwalliya da kasaita don nuna farin cikin su da haihuwar fiyayyen halitta, a wuraren Mauludi da tituna, suna rera wakokin yabo ga rayuwar Annabin Rahama. Sai dai kash, anya yadda muke zumudin nuna shauki da kauna, haka muke nunawa wajen aiki da koyarwar sa a harkokin mu na rayuwa? Ko kuwa sai dai a inda ya dace da son zuciyar mu?
Soyayyar mu da shaukin mu ga ambaton manzon Allah (SAW) ba su wadatar ba, har sai mun hada da koyi da halayensa a dukkan al'amuran rayuwar mu. Ma'aikin Allah mutum ne mai kyawawan dabi'u ababen koyi.
Allah madaukakin sarki yana shaidar sa da cewa, 'Lallai kai (Muhammad) kana da mafiya kyawun halaye!' less
Daga Abba Abubakar Yakubu... moreHANKALINKA JAGORANKA: Girman kai rawanin tsiya
Daga Abba Abubakar Yakubu
Wannan karin magana tana nuni ne da illar mutum ya kasance mai nuna girman kai, raina mutane da nuna fifikon sa da sauran mutane. Nuna halayyar ni na fi karfin a yi min kaza, ko na wuce a yi min abu kaza.
Girman kai na daga cikin munanan halayen da ake kyama tare da nisantar mutane masu nuna wannan halayya. Mai nuna halin girman kai bai cika shiri da mutane ba, kuma yana kasancewa mai yawan rikici da mutane, saboda ba ya ba da uzuri ga kuskuren da aka yi masa.
Masu girman kai suna nisanta kansu da arziki da soyayyar mutane, kuma suna tsallake damarmaki da yawa da gangan ko cikin rashin sani.
Girman kai na daga cikin halayen 'yan wuta, kamar yadda wani hadisi ya kawo. Don haka ba hali ne da aka san mutanen kirki ko Musulmin kwarai da shi ba.
Ya kamata mu rika fahimtar cewa, duk abin da addini ya koyar game da halayen kwarai yana da nasaba wajen samun tsirar mutum har a lahira.
Ma'aikin Allah, Annabi Muhammad (SAW) mutum ne mai matukar saukin kai da rashin nuna fifikon sa a cikin mutane. Yana mu'amala ta kwarai da makusantansa da na nesa da shi, yana nuna girmamawa da martaba mutane, ba tare da ware wannan da ne ko bawa ba.
Wadannan na daga cikin halayen da suka kara sanya kaunarsa a zukatan jama'a Musulmai da wadanda ba Musulmi ba.
Akwai wasu mutane da ba sa sassautawa na kasa da su, kuma hatta wadanda suka girme musu ko suke gaba da su ba sa mutunta su.
Idan har kana haka domin a zatonka hakan ne zai sa a rika ganin girmanka, shakkar yi maka raini ko kusantarka to, a maimakon ka samu yadda ka ke so daga wajen mutane sai ma ka samu akasin haka. Mutane za su tsane ka, a daina kusantar ka da duk wani abin alheri ko girmamawa.
Yana daga munanan halayen da ake tir da su, a kowacce al'umma da kowanne addini. Har ma Musulunci yana nisanta kansa da mutumin da mutane ke shakkar sa don munin halinsa.
Duk mai son ya yi mutunci a idon mutane to, ya mutunta kowa, shi ma kuma ya tsare mutuncinsa. Sannan Wanda yake son a girmama shi ya girmamawa duk wanda hulda da zaman tare suka hada su. Ma'aikin Allah (SAW) yana cewa, ku girmama furfura ko da ta kafiri ce. Ma'ana, mutum ko ba Musulmi ba ne a girmama shi, domin wasu na ganin sa da martaba. Shi ya sa ba a son a wulakanta shugabanni da raina magabata.
Duk wanda Allah ya sa shi ne gaba da kai, a wajen aiki ko a makaranta to, ka ba shi girmansa, ko da kuwa ka girme shi ko ma danka ne. A dalilin haka shi ma sai ya ba ka naka girman, ba tare da wani raini ko kaskanci ba.
Allah ya karrama dan Adam kuma ya fada a Alkur'ani mai tsarki, an rawaito daga hadisai yadda kyakkyawar mu'amala take sanya kauna da zaman lafiya. less
Umar1984
Aslm. Yau da Gobe da juyawar Dare da Rana sun isa mai hankali yasan inda ya dosa.
Auwalu Adamu Sabongida
Assalamu alaikum
Da fatan dukkan jama'ar wannan gida su lafiya?
Mun shigo don karuwar Ilimi.
Abba Abubakar Yakubu
(owner)
Ina farin ciki da wannan sabuwar manhaja ta Bakandamiya, da fatan za ta ci gaba da kasancewa matattarar bayanai masu inganci da samun abokan arziki masu kishin addini da cigaban juna.
musa Idrisjakara
matasa ka da ku yarda wani ya zuga ku akan kuyi tarzoma.
Yin zanga-zanga ba shi ke samar da 'yanci ba, zaman lapia ya fi mana komai, ko don tsira da lapia, dukiya da rayukan mu.
Muyi tunani muyi wa kan mu karatun ta natsu, mu bi al'amarin a hankali, komai mai wucewa ne, mu ci gaba da addu'a da sannu Allah zai mana magani.
BA BU NI A ZANGA-ZANGA INA SON YANKIN AREWA Allah ya daukaka qasata Nigeria Allah yabamu zama lafiya
Muhammad Jamiu Abdulfatah
Assalamu Alaykum...
Q1. 114
Q2. Abul-Hasan: Aliyu Bn Muhammad Bn Muhammad Ashazaliy Almalikiy
Q3. Saboda ya Auri Yayan manzon Allah guda biyu
Q4. Abul-Laith, Nasir Bn Muhammad Bn Ahmad Bn Ibrahim As-Samarqandiyy
Q5. Bazara
Q6. Hankaka
Q7. Niger ce
Q8. 1960