Turanci a Saukake » Discussions


Darasin Farko: Parts of Speech (rabe-raben kalmomi jikin jumla)

 • Leader
  December 29, 2017

  A yau za mu fara karatu a kan ‘Parts of Speech,” wato yadda julma ya rarraba, ko kuwa mu ce rabe-raben kalmomi cikin jumla.

  Farawa a kan wannan yana da muhimmanci saboda duk magana da mutum zai yi, zai gina tana a kan jumla. Saboda haka, idan mai karatu ya san yadda jumla ya rarraba, zai ba shi saukin yadda zai gina na shi jumlar.

  Bisa mashahurin bayanai na masana harshen Turanci, kalmomi cikin jumla sun rarraba har zuwa ababuwa guda takwas. Ma’ana idan mutuum ya gina jumla, rubuta wa ya yi ko furtawa, a na iya samun wadannan ababuwa guda takwas ko kasa da haka. Ba dole a samu dukkaninsu ba, amma dole ne ya zamo an samu wasu da ga cikinsu. Wadannan ababuwa sune:

  1. Noun (Suna)
  2. Pronoun (Wakilin suna)
  3. Adjective (Siffan suna)
  4. Verb (Aiki/Fi’ili)
  5. Adverb (Siffan aiki/fi’ili)
  6. Preposition (kalma ce da ke yawan zuwa kafin suna – za mu yi cikakken bayaninta a gaba)
  7. Conjuction (Kalma mai hada sunaye – shima bayaninsa zai zo a nan gaba)
  8. Interjection (Motsin rai)

  A takaice, za mu iya cewa darasinmu na yau ya kasance a kan rarrabuwan kalmomi cikin jumla, wanda kamar yadda muka yi bayani, sun rarrabu har gida takwas kamar yadda muka kawo su a lissafe.

  A dasari na gaba, za mu dauke su daya bayan daya mu yi bayaninsu da kuma yadda za a yi anfani da su cikin jumla. Domin abun bukata a nan, ba wai saninsu ne kawai ba. Shin yaya mai karatu zai yi anfani dasu ya gina jumlarsa mai kyau?

  Sai darasi na gaba in Allah ya hada mu. Allah ya bamu ilimi mai amfani.

 • Member
  June 11, 2019
  Allah yasaka da alkairi
 • Leader
  June 11, 2019
  Amin, Abdussalam. Idan kuma kana da wata taimbaya, kana iya rubutowa. Na gode.
 • Member
  June 11, 2019
  Gaskiyane ayanzu fatan alkairi zanyi agareka dasauran abokan aikinka dafatan Allah yadaukakeku yaqara muku ilimi mai anfani nagode
 • Leader
  June 12, 2019
  Amin Ya Rabb. Mun gode kwarai. Allah Ya bar zumunci.
 • Member
  November 7, 2019
  Assalamu alaikum.. Wannan zauren da matasa sun gane da ya fi yawace yawace marar anfani a Facebook domin ko a Kwai karuwa sosai. Allah saka da alkhairi
 • Leader
  November 8, 2019
  Wa'alaikum Assalam. Mal Bashir godiya nake. Allah Ya saka da alkhairi.