Magana Jari Ce Littafi na Farko » Discussions


Labari na 28: Shaihu Dan Hodiyo Da Wani Malami

 • Leader
  April 16, 2019
  Wata rana wani malami daga gabas da ya ji labarin Shaihu sai ya yiwo wa Sakkwato tsinke, ya zo ya ga abin da a ke fadi da idanunsa, domin an ce gani ya kau da ji. Da ya kusa da Sakkwato ya yi shiri irin na alhazai, ya shiga kokuwa, ya tafi wajen Shaihu Mujaddadi, ya ce, “Ina da fatawa, ya Shugabana.”

  Shaihu dan Hodiyo ya amsa, “Allah ya sanasshe mu!” Mutumin nan ya ce, ‘Ya Shugabana, da me a ke miya a nan kasarku?”

  Shaihu ya ce, “Da kuka, da gishiri, da tosshi, da daddawa.”

  Mutumin nan ya ce, “To, ashe sun sha bamban da na kasarmu.” Ya yi ban kwana da Shaihu, ya fita. Shaihu ya ci gaba da sha’anin da ya ke ciki na jihadi. Aka ci kasashe, aka ba wadansu tutoci, sai can bayan shekara biyu har an manta da wannan mutum da ya yi tambaya, sai mutumin nan ya dawo, ya sami irin kayan Hausawa, ya yi shiri yadda ba mai ganewa shi ya zo bara waccan. Ya tafi wajen Shaihu ya gaishe shi, ya c,e “Da me kuma?”

  Da ya ke Shaihu dan Hodiyo a;’amarin nasa ya yi nisa, ya tuna tambayar bara. Ya dubi mutumin nan, ya ce, “Idan da wadata a kan sa nama.”

  Ko da bakon nan ya ji haka, sai ya fadi ya nemi Shaihu dan Hodiyo gafara, ya sallame shi ya koma garinsu.

  “Tsakaninka da Allah, Allah ya ba ka nasara, ka taba jin wannan irin labari na Shaihu Mujaddadi in ba yau ba?”

  Musa ya ce, “Gaskiya dai, ban taba ji ba. Shin don Allah ko kai ka kaga shi yanzu?”

  Aku ha kada kai, ya ce, ‘Haba, Allah ya ba ka nasara, wallahi ba yanzu na kera ta ba, ni ma haka na ji shi. Ko mutum na hauka, irin karairayin nan da a ke wa tatsuniyoyi a yi wa tarihi kamar na Shaihu Mujaddi dan Hodiyo? Haba, a wargi wuri ya ke yi.”

  Musa ya ce, ‘To, ko da ya ke haka, kana tsammani wannan ya fi wanda na gaya maka jiya ban mamaki?”

  Aku ya ce, “Allah ya ba ka nasara, ai ba gardama na ke ja da kai ba. Wadannan al’amura ne na waliyyai, idan aka yi zurfi ciki, sai a tasam ma yin aabo. Ba mu da wata ta cewa, sai Allah ya ba mu albarkacinsu, amin, amin, amin!”

  Musa ya ce, “Gaskiya ne, Allah dai ya kiyashe mu azabobin Jumma’ar da ba ta da Asabar, domin alfarmar Shugaban talikai!” Ya juya zai tafi.

  Aku ya ce, “Af, Allah ya ba ka nasara kana ya sami me?”

  Musa ya waiwayo, ya ce, “Kana ya sami me fa?”

  Musa ya ce, “Me ka ke nufi da Kana ya sami ne?” Wa ka ke maganarsa? Wane abu zai samu? In kana tambayar wani abu ne ka fadi mu ji. Kai ba abin da ke dibarka sai samartaka. To, ni na aske.”

  Aku ya duka, ya ce, “Allah ya huci zuciyarka, yallabai, Sairam ta,bauar da ma uo ,ala jiya, da na so in gani in ka iya lyad da jawabin da ka fara ba ni, don ka ce tarihin da na bayar yanzu na Shaihu Mujaddadi ba shi ba bam mamaki kamar wanda ka bayar jiya.”

  Musa ya ce, “wane tambaya ka yi mini jiya?”

  Aku ya bushe da dariya, ya ce, “jiya-jiya har ka manta, rankaya dade? Na tambaye ka shin sai mutum ya sa me da me a jikinsa za a san lalle ya yi ado, ba kushewa To, ina ga wannanda aka yi da shekara biyu?

  Musa ya dubi aku ya ce, “Ho dan nema! Kai dai ba ka barin ko ta kwana, duk inda mutum ya fito maka kana make kana ko ta kwana, duk inda mutum ya fito maka kana make kana kallonsa.” Ya duba haka sai ya ga gari ya waye, ya harari aku, ya ce, “In don mugunta ka ke mini wannan abu, ba kome, Allah ya isa.” Ya shige gida.

  Azahar na yi sai ga Sarki Abdurrahman ya aiko da dan bushara an ci nasara, gobe kuwa tun d safe ga shi nan tafe. Musa ya tambaya. “Ina Mahmudu? Ya warke? Dan busharan nan ya ce, “Ai da ma ba bain da ya same shi, gove ka gan shi.” Kafain Musa ya sami damar tambayarsa sai ya hau ya koma, don an ce kada ya zauna. Duk gari ya rude da gude-gude, ana ta murna, Waziri ko sai ka ce an yi masa mutuwa.

  Magariba na yi sai ya kira wadansu samari hudu daga cikin yaransa, ya gaya musu abin da a ke ciki duka, ya yi alkawari in sun yi kokarin da suka kashe Musa daren nan na yau, ko da su murde wuyansa ne, shi ko ya ba su fam ashirin ashirin.

  Bayin nan suka ce, “Don wannan har wani aiki ne?” Suka shiga neman kayan ado irin na mata suna sawa.

  Aku kuwa da ya ke ya san haka zai faru, magariba na yi sai ya ce wa Musa, “Yallabai, yau bai kamata a yi barci ba, sai mu koma babban zaure, mu gamu da bayin nan a yi ta hira.”

  Musa ya ce, “Ai ko hakanan ne,” Aka kai kujera, Musa ya tafi ya kame bisa, bayi suka kewaye shi.

  Jimawa kadan aku ya biyo, ya duba ya ga bayin nau ba mai wani makami kusa da shi, sai ya ce, “Ashe ku duka mata ne, yaya za a bar ku kumu ku rika zama ba mai ko sanda? Halal kun manta da duniya.” Bayi suka ga gaskiyarsa, kowa ya dauko takobinsa ya zare ya aijye a gabansa, aka shiga hira.

  Can lisha sai ga bayin nan na Waziri su biyar, har da Barakai, suka shige gida sai ka ce mata, aku kadai ya gane maza ni. Suka sami wani zaure suka make, su ba su cikin gida, su kuwa ba su waje. Suna nan suna jiran Musa ya shigo, don su tarye shi nan su halaka shi, hira ta ki karewa. In aku ya ga za su dan dakata sai ya yi musu wani abin dariya. Suka yi ta yin haka har asuba ta yi.

  Da aku ya ga sun gaji da hira, wadannan sun fara gyangyadi, sai ya ce, “Bari in yi muku wani labari mai dadi.”

  Musa ya ce, “Ai ko hakanan ne, ku tsaya ku ji fasaha wurin dan tsuntsun nan nawa.” Wadanda ke jin barci suka murje idanunsu.

  Aku ya sami ruwa ya kora, ya yi kaki ya zubad da yawu, ya fara.

  Latsa [url=https://www.bakandamiya.com/music/47/magana-jari-ce-littafi-na-farko-na-alhaji-abubakar-imam]WANNAN WURI[/url] don sauraren labarin cikin sauti.