KUNGIYA D'AYA TAMKAR DUBU, KUNGIYA MAI AMFANI DA NAZARI DA TUNANI,BURIN M.W.A SHINE YA FAD'AKAR, YA NISHAD'ANTAR SANNAN YA ILMANTAR DA MASOYAN TA.
MUNA ALFARI DA RUBUTU SABIDA ALKALAMI YAFI TAKOBI.
Nagarta Writers Association kungiya ce ta marubutan yanar gizo, (online writers) mai zaman kanta.
An bude k'ungiyar ne domin taimakon juna da k'arfafa ma juna gwiwa. Kungiya ce da zata rink'a tsabtace littafan marubutanta kafin a fitar da su ta yanda... moreNagarta Writers Association kungiya ce ta marubutan yanar gizo, (online writers) mai zaman kanta.
An bude k'ungiyar ne domin taimakon juna da k'arfafa ma juna gwiwa. Kungiya ce da zata rink'a tsabtace littafan marubutanta kafin a fitar da su ta yanda za'a samu kaucewa duk Abu da zai kawo gurbacewar addini, tarbiyya da kuma al'adun Hausawa.
K'ungiyar za ta taimakawa wada'nda suke tasowa a harkar rubutu, ta hanyar hada su da wad'anda za su rink'a taimaka musu domin suma su samu isar da sakon da suke son isarwa ta hanyar rubutu. Kungiyar tana kunshe da marubutan da ake alfahari dasu, wanda su kan taimaka wurin kawo cigaba a duniyar adabi. less