Kainuwa dashen Allah, duk wanda ya shiga cikin ki ya amfana da ke, Allah ya ?ara ma zuma za?i dan masu sai da sugar susha haushi. Ma?iyanki fadawanki. mu munsani ko mutane basu fa?a ba sun amfana da ke.
A wannan zamani da amfani da na'ura mai kwakwalwa ya zama ruwan dare, kuma fannoni daban-daban na rayuwa suke amfani da shi wajen inganta ayyukansu.
A wannan tafiya ba a bar sashen ilimi a baya ba. Tuni kasashen da suka ci gaba suna amfani da kumfuta da... moreA wannan zamani da amfani da na'ura mai kwakwalwa ya zama ruwan dare, kuma fannoni daban-daban na rayuwa suke amfani da shi wajen inganta ayyukansu.
A wannan tafiya ba a bar sashen ilimi a baya ba. Tuni kasashen da suka ci gaba suna amfani da kumfuta da Intanet wajen inganta ilimi da karatu.
Ina malaman makaranta da masu bincike a fannin koyarwa da karatu, har ma da dalibai, ku zo Bakandamiya ta sama mana farfajiya inda za mu baje kolinmu don koyar da darussanmu ga dalibai ta hanyar amfani da fasahar zamani.
Babu iyakan abinda za mu yi a wannan taska sai iyakan abinda tunaninmu da fasahar da Allah Ya bamu ya tsaya.
Don haka ku shigo wannan zaure mu tattauna, kuma za mu gaya muku hanyoyi daban-daban da za ku iya amfani da Bakandamiya a ajujuwanku da bincikenku, sannan kuma za ku iya kirkiro wasu.
Ku latsa alamar shiga zauren don ku shigo mu tattauna. less
Nagarta Writers Association kungiya ce ta marubutan yanar gizo, (online writers) mai zaman kanta.
An bude k'ungiyar ne domin taimakon juna da k'arfafa ma juna gwiwa. Kungiya ce da zata rink'a tsabtace littafan marubutanta kafin a fitar da su ta yanda... moreNagarta Writers Association kungiya ce ta marubutan yanar gizo, (online writers) mai zaman kanta.
An bude k'ungiyar ne domin taimakon juna da k'arfafa ma juna gwiwa. Kungiya ce da zata rink'a tsabtace littafan marubutanta kafin a fitar da su ta yanda za'a samu kaucewa duk Abu da zai kawo gurbacewar addini, tarbiyya da kuma al'adun Hausawa.
K'ungiyar za ta taimakawa wada'nda suke tasowa a harkar rubutu, ta hanyar hada su da wad'anda za su rink'a taimaka musu domin suma su samu isar da sakon da suke son isarwa ta hanyar rubutu. Kungiyar tana kunshe da marubutan da ake alfahari dasu, wanda su kan taimaka wurin kawo cigaba a duniyar adabi. less
Wannan zauren zai tattauna irin tsofaffin kalmomin hausa wadanda yanzu ba kowane bahaushe ne ya san su ba saboda zamani. Zai kuma zakulo Sana'o'in mu da al'adu na tun taletale.
Wannan zauren an ?ir?ireshi ne don tattauna matsalolinmu na yau da kullum, musamman matsalolin da su ka shafi zamantakewa, bada shawarwari ga duk wani mai neman shawara.
Wannan zaure ne da aka kirkira don kawo muku labaran dake cikin Magana Jari Ce littafi na farko da kuma tattaunawa da muhawarori game da littafin.
Har ila yau, zaure ne don tunawa da mawallafin Magana Jari Ce, Alhaji Abubakar Imam, tare da irin... moreWannan zaure ne da aka kirkira don kawo muku labaran dake cikin Magana Jari Ce littafi na farko da kuma tattaunawa da muhawarori game da littafin.
Har ila yau, zaure ne don tunawa da mawallafin Magana Jari Ce, Alhaji Abubakar Imam, tare da irin gudumawar da ya bayar a fannin rubuce-rubuce da adabin Hausa.