Labari na 27: Shaihu Dan Hodiyo Da Madugu

 • Leader
  April 18, 2019 9:18 PM BST

  Wata rana wani madugu yana dawowa daga Gwanja, ya iso Kwara ya shiga jirgi. Suna kan tafiya cikin jirgin nan, sai igiyoyin Kwara suka murda, jirgin ya yi nan tangan tangan, ya birkice. Sai madugun ya kama, “Shaihu dan Hodiyo, ka taimake mu! Shaihu dan Hodiyo, ka yi agaiji! Ni dai kam wallahi in na kubuta daga wannan halaka, in na je Sakkwato sai na kai maka sadakar goro kwaraya goma.” Yana fadin haka sai ya ga wani ya zo ya kama shi, ya fid da shi duk da kayansa. Ya duba ya ga kowane ne, sai ya ga ba kowa.

  To, a cikin wannan lokaci kuwa Shaihu Mujaddadi dan Hodiyo yana Sakkwao, yana ba da karatu, kuma yana wa’azi ga jama’a. Sai aka ga ya yi shiru. Can sai aka ga yana matsa hannun rigarsa, ruwa na zuba tsurururu. Jama’ar da ke nan suka nemi bayanin wannan al’amari daga gare shi.

  Shaihu ya ce, “Wani bawan Allah ne ya nemi taimakommu a Kwara da jirginsa ya kife. Allah ya nufa muka je muka taimake shi.”

  Jama’a suka rike baki suna cewa, “Allah ya sa mu cikin ceton Annabinsa, ya ko ba mu albarkacinku, Mujaddadai!”

  Bayan an yi kusan wata biyu, ran nan sai ga madugun ya zo Sakkwato, ya debi goro kwarya uku ya tafi wajen Shaihu ya kai masa don ya cika alkawari, ya kuma nemi albarka. Bayan ya gaishe shi, ya gaya masa abin da ya faru duka ga jirginsu sa’ad da suna tsakiyar Kwara, da kuma yadda ya roke shi, ya zo ga taimakonsa, ya ga kamar wani ya zo ya fid da shi, amma da ya duba bai ga kowa ba. Shaihu dan Hodiyo ya tambaye shi wace rana ce wannan hadarin ya auku, kama nawa ga wane wata ne.

  Madugu ya fadi ranar da watan, ya lissafa kuma ya fadi kwanan watan sa’ad da wannan a;’amari ya auku. Da almajiran Shaihu su kuma suka lissafa, sai suka ga ya kama daidai da ranar da Shaihu Mujaddadi ya yi shiru cikin wa’azi yana matsar hannun rigarsa. Abin ya kara ba da mamaki.

  Madugu ya fitad da goro ya mika wa Shaihu, ya ce, “Ga abin da na yi alkawari zam ba ka in Allah ya nufa na kubuta.”

  Shaihu dan Hodiyo9 ya yi godiya, ya karba ya ajiye, ya yi murmushi, ya dubi madugun, ya ce, “Ai ko ba ka cika alkawari sosai ba. Kwarya goma ka ce, ga shi ka kawo uku.”

  Madugu ya rasa abin da zai ce don kunya, ya tafi gida ya ciko kwarya bakwai ya kawo wa Shaihu, ya fadi ya yi godiya, Shaihu ya karba, ya raba wa mutanen da ke nan sadaka.

  Musa ya dubi aku, ya ce, “Ka ji labari daya da ba ka sani ba cikin mu’ujizozin Shaihu Mujaddadi dan Hodiyo. Yanzu kana daya. In dai ga labarun Shaibh ne, in na fara na iya gaya maka goma ba ka sami wanda ka sani ba.”

  Aku ya tuma nan ya tuma can, ya karkata kai, ya ce, “Allah ka ga duk da haka sai da ka yi babban kuskure cikinsa. Shi ya sa ka ruda ni, na ji kamar ban sani ba.”

  Musa ya ce, “To, ka fara ba? Kai dai wani ba ya yin abin kirki in ba kai ba. Wannan labari na ji shi ya fi sau kam, amma duk ban taba jin inda suka saba ba.”

  Aku ya ce, “Saurara, Allah ya ba ka nasara, abin da na gaya maka duk na labarin Shaiju dan Hodiyo sai ka yarda, Madugu da ka ce ba madugu ba ne, farke ne. Ai ka ji batan da ka yi.”

  Musa ya ce, “Wasalam! Ka ji ka ba? To, me ya raba dambe da fada?”

  Aku ya yi dariya, ya ce, “Allah ya ba ka nasara, zage-zage.”

  Sai Musa ya yi dariya, ya yi tsaki, ya ce, “Kai dai ba ka gajiya da surkulle. Ko mutum ya tashi yin hushi da kai sai ka ba shi dariya. Allah ya kai mu dare, kai ka gaya mini naka wanda ba mutum duka ya sani ba. In na bi taka yanzu, har lokaci, ya wuce ban yi salla ba.”

  Aku ya kada fiffike, ya ce, “Allah ya kai mu. Amma ina da fatawa. Don Allah, Shugabana, shi sai mutum ya sa da me da me a jikinsa za a san lalle ya yi ado, ba abin kushewa?”

  Musa ya ce, “Kai fa na san ka, wadansu tambayoyinka duk na ba’a ne. Kai ba ka kan gani da kanka ba? Ai ko tsuntsu ya san ba abin da ke kambama mutum irin ya sa wando mai zina, da jabba, da riga aska takwas a binanta, kana ya sami--.”

  Aku ya ce, “Allah ya ba ka nasara, ai ma ado ya kare. Kada in tsai da kai, sai da dare.”

  Musa ya ce, “Allah ya kai mu da alheri.”

  Da dare ya yi, barci ya share Musa, sai can da asuba ya farka ya tashi, ya shiga damaru, ya dauko mashi ya zo wajen aku, ya ce, “Madalla, ai kowa ya yi karyar dare gari ya waye! Ka ce labarin Shaihu da na bayar jiya ko na goye ya san shi. To, ina son in ji naka wanda ba a sani ba.” Aku ya kada fiffike, ya dukad da kai, ya c,e “Allah ya ba ka nasara, yanzu ko ka ji.”

  Don sauraron wannan labari cikin sauti sai ku latsa nan.