Entities Special and Societal Development Association » Discussions


Barace-Barace (matsaloli)

 • June 24, 2019
  INA GOYON BAYAN A HANA TURO YARA BIRNI DA SUNAN BARACE-BARACE

  95percent na yaran da ake turowa Karatu nan cikin Birni ba Qur'anin suke samu ba kawai yawace-yawace sukeyi a jin Wake-Waken Films suke karewa domin basu da buri banda suyi aikatau ko sata su siyi waya (Handset) su ringa kallon films suna jin kade-kade irin yadda yaran Birni sukeyi Wallahi ko Shekaran Jiya ina wajen wani Abokina Mai Chajin Waya' wani almajiri yazo bai wuce 17years yana tambayar wai Mallam Kana Tura Blue Film?

  Takaici ma ya hanani magana sai nacewa da abokin nawa daka karbi Wayar ka tura masa Qur'ani yafi duk nasan karshe gogewa zaiyi.

  Sai Mace ta shigo Birni siyayya danta da suka turo bara shine zai daukar mata dakon kayan yakai mata tasha, ta bashi Naira 50 ya juya ya tafi watakila tama manta wannan danta ne da suka turo Birni karatu.

  A shekarun baya tabbas wadanda ake turowa Karatu suna yin ilimin mai amfani kuma su amfanar amma banda yanzu.

  Idan Karatun Ake So Ayi Su Yayyensu Meyasa Da Sukazo Suka Koyi Qur'anin A Birni Basa Komawa Kauyukan Suna Koyawa Kannensu.

  Ko Kuma Gwamnati Idan Da Gaske Takeyi Ta Fito Da Wani Tsarin Binsu Kauyukan Ana Basu Ilimin Tunda Suma Yan Nigeria Ne Kamar Kowa...