Skip to content

Gurbin magani cikin karin maganar Hausa

Share |

A ƙarƙashin kiwon lafiya, kalmar magani sananniya ce ga kowane Bahaushe. Wasu masana, sun yi hasashen cewa, kalmar ba ta rasa nasaba da kalmar ‘gwaji, wato a gwada abu a ga ko zai yi. Suna ganin kalmar ‘hatsin bara’ ce, wato haɗe-haɗen kalmomi ne na Hausa suka samar da ita. Kalmomin su ne: “ma” da “yi” da kalmar “gani”.

Idan Bahaushe ya sami wata cuta ko rashin lafiyar da yake son kawarwa, sai ya sami ‘yan ganyayyakinsa da saiwowi ya harhaɗa ya ce: “Ma gwada wannan mu gani”, har dai kalmar ta koma ‘ma yi wannan mu gani”. Daga baya ta koma, ‘ma yi ma gani”, har ya zuwa kalmar ta koma: “magani”, ma’ana, bari mu yi ma gani (Bunza: 135).

Ma’anar magani

Dangane da ƙunshiyar ma’anar kalmar magani, har ila yau wasu masana da ɗaliban nazarin al’adun Hausawa sun sha ɗauki-ba-daɗi kan haƙiƙanin gano ma’anarta.

Da farko ga yadda Kamusun Hausa na Jami’ar Bayero Kano (2006) ya fassara ta:

(i) Abin da ake sha ko shafawa a jiki ko ɗurawa a jini ta hanyar yin allura, don neman samun lafiya.

(ii) Abin da samuwarsa kan kore wani daban, misali, tarko yana maganin Beraye.

(iii) Sammu, wato harhaɗa wasu abubuwa da yin surkulle da nufin cutar da wani, musamman abokin gaba.

(iv) Harhaɗawa ko yin wasu abubuwa na musamman don shawo kan wani, ko samun galaba a kan wani abu.

Kasancewa magani ba a yin rayuwa babu shi ya sa Bahaushe ya kirkiri wasu maganganun azanci da su. Ga kuma misalansu a kasa kamar haka:

1. Maganin kada a yi kada a fara.

2. In kura ta na maganin zawo ta yi wa kanta.

3. Jan biro maganin takaddarin ɗalibi.

4. Gobara daga kogi maganinta Allah.

5. Sana’a goma maganin baccin rana.

6. In ka san halin mutum ka sha maganin zama da shi.

7. Tafiya maganin gari mai nisa.

8. Ɗauri maganin bajewar kaya.

9. Hadarin ƙasa maganin mai kabido.

10. Karen bana maganin zomon bana.

11. Maganin shege sai ɗan gatan uwa.

12. Maganin Bawa sanda.

13. Maganin maƙi gudu ban kashi.

1.4 maganin ƙiyayya rabuwa.

15. Barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa.

16. Hannu da yawa maganin ƙazamar miya.

17. Idan so cuta ne haƙuri magani ne.

18. Haƙuri maganin zaman duniya.

19. Mu wasa ne? Babarbare ya ba da magani an sha an mutu

20. Magani a sha ka a warke

21. Hauka maganinki turu.

22. Haske maganin duhu.

23. Ƙoshi maganin yunwa.

24. Haihuwa maganin takaicin duniya.

25. Haihuwa maganin mutuwa

26. Maganin biri karen maguzawa.

27. Abu naka maganin a kwabe ka.

28. Araha butu maganin mai wayo

29. Riga-kafi ya fi magani.

30. Anin wani bai yi wa wani magani.

31. A busa a bari ba ya maganin ɗan ban,

32. Gida goma maganin gobara

33. Bakar ajiya mai maganin bakar rana.

34. Ciwon da ba ka da magani a mutu ya fi.

35. Da tsohuwar zuma ake magani.

36. Fitina sai ka ce shan maganin Bature.

37. Gangar baka maganin hasarar fata.

38. Gudu da mari ba ya maganin bauta.

39. Gudu da mai ruwa ba ya maganin dauɗa.

40. Haukar ba ni maganin amshi.

41. Hannu da yawa maganin mai ƙwange.

42. Hauka maganinki ɗanyar geza.

43. Jini ba ya maganin kishin ruwa.

44. Linzami da wuta maganin mahaukacin doki.

45. Mu je mu gani maganin mai karya.

46. Maganar ciki maganin mai tsegumi, bai ji ba balle ya karasa.

47. Naman kura da magani yake karewa.

48. Sha yanzu magani yanzu.

49. Yunwa maganin mugunyar dafuwa.

50. Zamani ba ka jin magani.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue Reading