Featured Create an Ad

Mambobi

 • Rahmatu Lawan Tunatarwar Jumma'a: Kar mu manta da karatun Surah Al-Kahf
  Fri at 8:14 AM

 • Bakandamiya LEFE Hamdullahi godiya gun Sarki Ɗaya, Shi ne wanda yai mu bai taɓa laifi ba. Bayan godiyar Ta’ala Sarki Ɗaya, Na yi yabo ga wanda bai taɓa wauta ba. Shi ne Mustafa madubin maiduba, Me kyautar da Nura bai taɓa ƙyashi ba. Sunnar Al-Aminu yace duk mui aure, Don haka zan riƙai ba zan taɓa a’a ba. Sharaɗin yinsa ne a miƙa sadaki kuma, A yi _siga_ a zo da shaidu su yi duba. Tilas ne a san waliyi gun mata, Na bi Nabiyu ni ba zan masa bore ba. Haka nan nai sani huɗun nan ke aure, Amma kyautayi ba zai zama laifi ba. Bayarwa ba tai kama da su cuta ba, _Ihasani_ ba zai kama da mugunta ba. Kyauta kyautayi halinsa kamanni ai, Miƙawa ba zai kamar a ci miƙe ba. Al’adar ƙarai abar a yaba ce ai, _Urfi_ an faɗe shi in har kun duba. Mata ai ado sukan yi abin kalo, Sun canci basu ni ban ƙyashi ba. Ga amarya a sai atamfa kyakkyawa, Mai daraja da ta saka wasu sui duba. Ga leshin ado da takalmi ƙwasƙwas, Sanya jakar ado ba zan mata zambo ba. Ga zoben ciki da sarƙa mai walwal, Kayan kwaliya ba sui mana laifi ba. Al’ada daban da addini mun san, Don haka ba ni cakuɗasu na kan duba. Ita _ada_ daban da ma _bidi’a_ mun san Ba lada ake biɗa idan ada kai ba. Addini ya ce a bar ada daidai, Mutuƙar dai ba zata kawo ɓarna ba. In har zata rusa _dini_ akan watsar Ni kam zam bi ko da ɗai ni ban ja ba. Kowa mai ado yake nema aure, Wa ye zai biɗar kucaka mui duba. Mai yin kwaliya ta fece tai fesfes, Ni kam na sani ba zan ja-in-ja ba. Ai da ado akan gani amare ma, A gayan inda zata samu ba lefe ba? Ba laifi a ce ka miƙo mai gwaɓi, Kowa gwargwadonsa ba da mugunta ba. Ni na kasa gane me wasu ke nema, To ka hana a baka ba aibu ne ba. Mu ma sai mu baka ‘ya haka ba komai, Makwafin yin hakan ga lefe kai duba. Babu koba mu baka daidai ne mu ma, Mutaƙar ka zaƙe ba za ka yi lefe ba. Mu haka za mu baka babu gadon kwana Domin ka matsa ba za ka yi lefe ba. Ba murhun _kitchen_ da kayan yin _juicy_ , Duk ai ka siya ba zaka yi lefe ba. Ko leda ba za mu baka ka mora ba, Har firij ba za ya zam ɗakin nan ba. Yadda ka ce hakan ga zan ba komai, Ba ƙira ba za ni ƙona icen nan ba. In har zan siya ka ce ba laifi ba, Lefe ma hakan bai zama laifi ba. Fata rabbana ya bamu mu ne mu Mui kyauta mu kyautata ba laifi ba. Ni kam Murtala gani na kenan ai, Ban yi faɗa ba ban ki da lefe ba. Murtala Uba Mohammed 7:55pm 17/07/2020
  Sep 13

 • Lawan Dalha Barka da Sallah! Muna rokon Allah Ya karbi ibadunmu Ya maimaita mana na badin badada. #Barkadasallah #EidMubarak
  Jul 31

 • Saudat Musa Barka da juma a
  Fri at 6:20 PM

 • Imrana Abubakar Assalamu alaikum
  Feb 16

 • Nasiru Muhammad kajiji ALHAMDULILLAH ALAH KULLI HALEEN
  May 18

 • Musa D Lalo Yarinya tun amakaranta suna lalacewa gurin niman ilimi, haka gurin niman aikinyi, tunda wasu iyayen duniyace agabansu baba Allah ba.
  May 28