Mambobi

  • Bashir Adam BAKANDAMIYA (1) ???? “IN KA ƘI JI....” ???? GABATARWA: Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Ƙai, Tsira da Aminchi su Tabbata ga Shugabammu Annabi Muhammadu (S.A.W) Da Alaye Da Sahabbansa baki ɗaya, Amin. Bayan haka: “IN KA ƘI JI...” Labari ne akan wani matashi mai suna Gagare, wanda ya gagari mahaifanshi, ya zama riƙaƙƙen mashayi ɗan bangar Siyasa. Abubuwa marasa kyau na wa'azi sun same shi amma bai tuba ba, ya biye wa Shaiɗan har ya ƙauracewa iyayensa. Dalilin hakan ne a ƙarshe har ƙwaya ta sanya ya haukace ya zama wulaƙantacce a cikin al'umma. Ina fatan labarin zai nishaɗantar, ya ilmantar kuma ya faɗakar. A sha karatu lafiya. — Bashir Adam. *** *** *** A DANDALIN SHAYE-SHAYE Zaune a dandalinsu na shaye-shaye suna fuskantar juna kamar yadda suka saba zama, matasa ne guda uku: Gagare, Goje da Ƙazaza, kowanne ya tuzguɗe dafe da hannu guda a ƙasa, gudan hannun kuma rike da tsumma yana zuƙar Sholisho. Hira suke yi irin tasu ta bugaggun mashaya waɗanda suka yi nisa cikin harkar chaskalewa. Gagare ne ya fara magana cikin murya irin ta bugaggu, ya ce, “Kai! Wallahi bãbã ba abinda ya fi rusu daɗi! Don ni in har ina da ƙwaya ba ni da wata matsala! Wallahi ni fa da in rasa ƙwaya gwamma in rasa abinci!” Goje shima cikin muryar makakku, yace: “Ƙwarai kuwa bãbã, Wallahi gwamma rashin abinci da rashin ƙwaya! Ai ni shi yasa ma kuka ga kwata-kwata ba na bari ƙwaya tana yanke min! Loading...
    October 28, 2019

  • Sani Saleh Ina wuni to everyone.
    September 30, 2018

  • A.AABDULLAHI Slam Barkan ku dawarw al-uman Bakandamiya. Dafan kwowa ya na cikin kushin lafiya? Allah ya sa haka amin.
    June 22, 2017