Mambobi

  • Jamilu Abdulrahman Ku shiga wannan link domin ku karanta labarin FATALWAR SINU complete a kyauta. https://www.wattpad.com/story/263776987?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=JamiluWriter&wp_originator=PbjxA%2F9gXOTxXRtYgtAO7Ygqz6xCC7DfpX34AgaWmhlX6qxiuoG45Go%2BBoRIVMAfaL2HClYQvXrENneosptmM29cWYU%2B1RrQmbV5euqIjwVCVH37rwgpcgFn%2FLWgFez%2B
    March 27, 2021

  • Sanah WA ZAI YI ZUBI A DASHIN DA ZAI KWASHI NINKIN ZUBINSA? A duniya babu baiwar da ubangiji ya yi wa bawa bayan karramawar yinsa a musulmi sama da lafiya. Tabbas lafiya wani jigo ne da ubangiji ya yi wa bawa ita, kuma ita ce kaso casa'in na jin daɗinsa. Ya ka ke ji yayinda ka samu naƙasunta koda na ciwon kai ne? Hakane yake ga wannan baiwar Allah tana fama da matsalar zuciya ne, yayinda zuciyarta ta kumbura sai cikinta ya kumbura kamar mace me ciki. Ka kisima a ranka yadda me lalura irin wannan zai iya bacci da sallama. Babban abin tashin hankali shi ne, mace ce me rauni kuma me ƙaramin ƙarfi. Idan ana cin ɓaure ba a tona cikinsa, ni da ku mun san yadda me ƙaramin ƙarfi yake rayuwa a yanzu. Ɗanta guda ɗaya ne yake ɗawainiya da ita kuma shi ma mabuƙaci ne, idan na ce mabuƙaci ina magana ne kan wanda bai tsaya da ƙafaffunsa ba mai faffutukar nema ne yau da gobe. Yanzu dai gashi abin yana neman ya ci tura, ba zai iya ɗaukar ɗawainiyarta ba, yanayi da jikinsa da zuciyarsa amma lalura irin wannan tana da wuyar sha ani ko ga me ƙarfi. Tana kwance a gadon asibiti yanzu haka. Ƴan uwa wanda Allah ya horewa me ficika ƙwandala ko ƴa biyar ya taimakawa wannan mata saboda Allah. Kadda mu manta sai mun tausaya ubangiji zai tausaya mana, haka kuma sai mun taimaka ubangiji zai taimaka mana. Ka bada biyar ubangiji ya yi ma sanadin samun goma. Shi alkhairi danƙo ne, inda ka yi shi ba nan zaka tsinceshi ba. Zaku iya tura taimakonku ta wannan hanya. Hassana Suleiman Isma'il Zenith Bank 2250859537
    February 10, 2021