Mambobi

 • Princess Aisha Aliyou Haiydar Nifa ban gane ba Dan Allah Nan Facebook ne?
  Mar 13

 • ALIYU MUHAMMAD IAM A NEW HERE, I WISH U ALL DE BEST AND SUCCESS.
  Mar 13

 • Bashir Isyaku Hotoro *MU SAN HAUSA* *SUNAYEN HAUSAWA DA MA'ANONINSU* *TANKO*: Yaron da aka haifa bayan an haifi mata biyu ko fiye. *KANDE*: Yarinyar da aka haifa bayan an haifi maza biyu ko fiye. *KILISHI* :Yarinyar da aka haifa kuma a dadai wanna lokacin babanta ya samu arziki ko sarauta. *BARAU*: Yaron da aka haifa ya rayu, amma an haifa wasu kafin shi ba su rayu ba. *SAMBO*: Yaron da aka haifa bayan maza da yawa kuma ya Zama Dan autan maza. *TALLE* :Yaron/yarinya da mahaifiya ta rasu tana gama haihuwarsa/ta. *AUDI* :Yaron/yarinyar da mahaifi ya rasu kafin a haife shi ko ta. *MIJIN-YAWA*: Yaron da aka haifa dukkanin kakannin sa suna raye. *DIKKO*: Yaron da aka fara haifa (Dan fari). *SHEKARAU*: Yaron da ya shekara a ciki *MAIWADA*: Yaron da aka haifa iyayensa suna cikin wadata. *GAMBO*: Yaron/yarinyar da aka haifa bayan tagwaye. *CINDO*: Yaron/yarinyar da aka haifa da yatsu shida. *MARKA*: Yarinyar da aka haifa lokacin marka-marka. *ALHAJI*: Yaron da aka haifa lokacin aikin haji. *AZUMI* ; Yaron/yarinyar da aka haifa lokacin azumi. *SARKI*: Yaron da aka sa wa sunan sarkin garinsu. *SUNAYEN NA'URORIN BATURE DA AKA HAUSANTAR DA SU* *Ford = Hodi* *Bedford = Bilhodi* *Mercedes = Marsandi* *Peugeot = Fijo* *Volkswagen = Baksuwaja* *Volkswagen Beetle = Ladi ba duwawu* *Fiat = Fet* *Austin = Ostan-Ostan* *Bus = Kiya-kiya* (borrowed from Yoruba) *Station wagon = Dafa-duka* *1973 Mercedes-Benz W114/W115 = Bagobira* *1982 Toyota Corolla = Bana ba harka* *Hatchback/coupe = ‘Yar kumbula* *Long bus = Safa* *Ten-wheel = Tangul* *Mercedes 911 truck = Roka* *Mercedes 1413-1414 truck = Bargazal* *Mercedes 1312 (and similar sizes) truck = 'Yar Fakas* *Max Diesel = 'Yar Rasha* (Kirar Kurma) *Man Diesel (12-Wheeler) = Kwamanda* *Truck with wooden body = Shorido* *Hearse = Motar gawa* *Towing van = Janwe* *Tractor = Tantan/tarakta* *Trailer = Titiri/tirela* *pick-up van = A kori kura* *Bulldozer = Katafila/buldoza* *SUNAYEN WASU YANKUNA DA HAUSA* *Ibadan = Badun* *South West Nigeria = Kurmi* *Port Harcourt = Fatakwal* *Onitsha = Anacha* *Africa = Afirka* America = Amurka *Turkey = Turkiyya* *Istanbul = Santabul* *Parsia = Fasha* *Russia = Rasha* *Germany = Jamus* *Britain = Birtaniya* *Sierra Leone = Salo* *Chad = Chadi* *Cotonou = Kwatano* *Port Lame = Fallomi* *Yemen = Yamal* *Israel = Isira'ila* *China = Sin* *Niamey = Yamai* *SUNAYEN WASU ABUBUWA NA TURANCI DA AKA HAUSANTAR DA SU* *Conductor* = Kwandasta *Scrutiniser = Sakwaneza* *Brake = Birki* *Gear Box = Giyabos* *Bumper = Bamba* *Radiator = Lagireto* *Carburator = Kafireto* *Distributor = Disfuto* *Coil = Kwayil* *Valve = Bawul* *Bearings = Boris* *Rings = Ringi* *Plug = Fulogi* *Crank Shaft = Karanshaf* *Grand Overhaul =Garanbawul* *Sunayen Igbo da Yarabawa da Turawa da sauran kabilu wandanda Hausawa Suka Hausantar da SU* *1) Tope = Takwai* *2) Kingsley = Kirsili* *3) Gbenga = Biyanga* *4) Ifreke = Cikurege* *5) Ngozi = Ingozi* *6) Nwankwo = Nawanko* *7) Gbagyi = Gwari* *8) Luggard = Lugga* *9) Bordeaux = Bod'o* *10) Awolowo = Awwalaho/Auwalawo* *11) Nnamdi = Namandi* *12) Balat Hughes = Balatus* *13) Taylor Woodrow = Tal'udu.*
  Mar 13

 • Abdulsalam A Musa To Assalamualaikum barkanku jama'ar wannan farfajiya
  November 23, 2020