Mambobi

 • Danladi Haruna *SAKAMAKON MUHAWARA* *RANAR MAGAJI DANBATTA (19/01/2021)* *KARAWA TA 55 FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION:- MAKI= 77 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION:- MAKI =76 *KARAWA TA 56 KARAMCI WRITERS ASSC.:- MAKI= 81 MARUBUTA KARE HAKKIN AL'UMMA WRITERS ASSOCIATION:- MAKI= 80 #MuhawararBakandamiya2020
  Jan 20

 • jauro wakili Duniya tana kama da tashar mota ce kowa dakansa yake zuwa yabiya kudin mota akaishi Lahira.
  Mar 1

 • Jiddah Washah ZAMAN AMANA WRITERS ASSOCIATION. Gajeren Labari kuma ƙagagge Na Hauwa'u Adam Suleiman (Jidda Washa) AZAL 2021 GABATARWA Dukkan yabo da ɗaukaka sun tabbata ga Allah buwayi gagara misali mahaliccin Mutane da Aljanu, Allah ka ƙarawa Annabinmu Rahama Aminci da sallama a bisa garesa da Sahabbansa da Alaye, sannan ka sa mu dace. Amin. GARGAƊI Ba a yarda wani ko wata su yi anfani da wannan Labarin ba ta hanyar juyawa ko sanfurashi ta wata sigar sai tare da izinina, saboda haka a kiyaye. Na gode. SADAUKARWA Na sadaukar da Labarina gareku a halin Zaman Amana Writers Association. Cikina ne ya kama wani irin kƴarma tamkar ana kaɗa ma sa gangi, cikin motar gabaɗaya kowa ya tsure daga masu ihu sai masu salati, lokaci guda muka kama kƴarma tamkar ana shaɗi. Harbin bindigar ke ƙara tsananta, yayin da direbanmu ke gudun fanfalaki tamkar ba gobe, duk gabaɗaya na kiɗime ba abin da ke fita daga zuciyata sai salati da tunanin bijirewa maganar Inna da na yi na taho ba tare da izininta ba. Can kamar ɗaukewar wutan lantarki, bayan kiftawa da Bismillah lokaci guda harbin ya tsaya cak, inda ko wani mahalukaton na cikin motar ya dunga sauke ajiyar zuciya ba kaukautawa tamkar an kammala gasar gumurzun kiba na tsere. Mun samu tafiyar mintina akalla ba aƙasara ba don zai iya kaiwa dakika arba'in ko fiye da hakan, hankalin kowa ya dawo garesa, wasu daga cikin motar har sun fara hirar siyasa da ta boko haram. Daidai wani daji, da zai sada da mu ya zuwa garin da zamu, wato jihar Ƙoɗau. Kamar a mafarki, muka ji hargagin wani sautin harbi na bindiga, wanda tunda nake ban taɓa jin irin ƙarar bindigar ba. Ras kirjina ya buga "Wayyo Allah kuɗina!" Cewar wani matashin saurayi fari mai saurin magana ya faɗa gami da ɗora hannaye biyu a tsakiyar kai. Dirar wasu manyan kartai muka ji daga cikin wata mota mai matukar kyau da ɗaukar hankali, duk ilahirin fuskokinsu a rufe, suna ta magana da junansu amma ko kaɗan Hausar su bata fita irin tamu, waɗanda suka haɗar da mata manya masu sanfurin samudawa guda biyu ɗauke suke da bakaken kaya ba ɗankwali a kayuwansu, gashin kansu bakin kirin amma babu halamun gyara balle kitso, ragowan biyar ɗin mazane tika tika tamkar bugun adawa suma shigarsu iri ɗaya. Cikin wani razanannen ihu na tsawa, ɗaya daga cikinsu ya ce "Kowa na cikin motar nan ya sauko ya rusuna a ƙasa" Wani ƙara mara misaltuwa cikina ya sake bugawa, inda hantar cikina ta kaɗa, wani tsillin gudawa ne ya so ya kufce min, kowa daganinsa duk mun tsure, sai raba idanu muke tamkar waɗanda aka ritsa a gidan ƴan sanda. Jiki na karkarwa haka muka sauka ɗaya bayan ɗaya cikin azama, dayawa daga cikinmu wasu sun ɓata jikinsu da fitsari, gudawa da kuma kuka. "Duk wani ɗan shegiya daga cikinku da ya sake min kuka ko fitsari ko kashi babu makawa sai ya cinye sa ko ya lashe kayansa tas" Ras, kirjina ya sake tafiya garin bugu cike da rashin lissafi. Wani ruɓaɓɓen kango suka kai mu, suka zube mu ƙasa tamkar kayan wanki, inda suka yi mana kawanya, sannan suka bi kowannen mu da bulala goma goma. "Ina son kowa ya mikawa Shaiɗan wayarsa domin za a kira iyayenku a faɗa musu kuɗin fansarku" A karo na uku ƙirjina ya sake wani ganga, da sauri na ɗago da kaina sama, cikin zaro idanuna waje, nanne na kasa daurewa damuwata har wasu tsirarin hawaye suka kufce mini. "kai dalla ba mu wayarka, wawa kawai, shashasha" Wata murya mai ban tsoro ta faɗa gami da zuba min yatsu a fuska, sanadin da ya sada ni da ƙasa har na kai ga rasa fahimtata na tsurarin dakiku. Bayan faɗuwar yammaci, magariba ta bugo sallama, dukkanin mu ba mu san halin da muke ciki ba, ni dai tunani na dai bai wuce akan abu biyu ba, na farko mu talakawa ne wanda na abinci wani zubin gagararmu yake, sai kuma ƙin jin maganar Innata da na yi na bijirewa umarninta saboda son zuciyata, wanan shi ake kira da tashin hankali wanda ba a sa ma sa rana ko lokaci, lallai yau ita ce ranar tonan siriri gareni na duniya. "kai! kai!kai!" Wani mai runannun idanu jazur tamkar gauta ya faɗa cikin zare idanu yana nuna ni da wani sanƙamemen manuninsa. "Lallai zamu kasheka idan har bamu ji bayani daga wurin Uwarka ba" Kalamansa ne suka dunga yi min shawagi a tsakiyar kwakwalwar kundin kaina. Zamu kashe ka! na tambayi kaina cike da kyarmar maganar, nan da nan na ji wani irin hawaye gaiyar soɗi sun min hawan ƙawara wanda basa jin hakuri tare da wasu majina marasa kiranye suka dunga sharɓo min. Abin mamaki kusan dukkanin ilahirin wanda ke gurin kuka ne ya zamar ma sa sana'a ba kaukautawa. Yau kimanin mako ɗaya kenan muna cikin halin ha'ula'i a cikin wannan bakin ƙangon, kullum tunanina ɗaya a wani irin hali Inna take ciki, ina da ina zata kareɗe wajen neman kuɗin fansata? na sake tambayar kaina a ƙaro na biyu, ga shi kullum sai an yi mana bulala goma goma, abinci ma sau ɗaya suke bamu a yini, ko ta sallah ma ba a yi duk da hakan ya tsaya min a kokon ramin zuciyata. "Da kai da kai da ke, ku taso mu tafi yau Allah ya kwace ku" "Alhamdu Lillah!" Suka furta inda suka mike da sauri suka bi sahun sa. Abu dai data gaba gaba yake, kowa an biya kuɗin karɓar fansarsa saura mu biyu, ni da wani saurayi bakin kirin tamkar makuba, yau ga shi saura kwanaki uku daga cikin kwanakin da aka sanyo na jarabawar mu ta unibasitin da nake yi a garin da na bari na shigo cikin wannan ibtila'in a Jihar KOWA. Tagwayen makonni sun shuɗe daga cikin wata ɗaya da muka share a wannan bakin kangon, babu wani labari na abin sha'awa dangane da batun tsirana daga hannayen azzaluman nan, duk na rame na fita a haiyacina saboda irin azabar da suke bamu ni da matashin saurayin nan, kullum sai sun yi mana bulala goma goma safe zuwa dare sannan su samu wanki da kuma yi musu tausa gami da ɗaga bulo zuwa safa da marwa. Yau take ranar da ba zan taɓa mantawa ba a rayuwata ba, saboda tsabar zulumi na rasa da wani suna zan raɗawa ranar domin na ga aya ta rayuwar duniya. Zaune muke a rakaɓe a jikin wani bango na cikin kangon, sai ga wani mahalukaton ya shigo cikin zafin nama, inda yayo kanmu da faɗin. "Yau zaku daina jin kamshin duniya sai dai na barzahu" Maganar da ta haddasa min wani faɗuwar gaba mai tafiya da hanjin ciki da ruwan sassan dake cikin jikina da gangar waje suka kama kyarma da kiɗima. Wani irin tsorata na yi, Matashin nan take ya kwalla wani razanan nan ihu, wanda tsigar jikina sai da ta tashi, lamarin da ya haddasa min tausayinsa, inda Kasurgumin basamudan nan ƙato ya sharara ma sa wani gigitaccen mari, lamarin da ya sa Matashin ya zube a ƙasa sumamme, haka ya dunga jansa a ƙasa cikin birjin ciyayi da duwatsu da gwazazzaɓa har muka isa bayan wani daji gab da wani kwari mai ɗauke da siraɗin nisa na rami. "Aikin ka ya yi kyau, Boka" Inda suka sa dariya, cikin wani mummunan sauti mara daɗin fasaltuwa. "Muguwa! ke ce zaki karasa wancan na kusan" Inda ya kai hannu ya nuna wannan Matashin da ke kwance rai a hannun Allah, da sauri ta ƙaraso tare da saita kan bindigarta ya zuwa kan kirjinsa, kan ka ce kwabo ta zuba ma sa dalmar alburushi, wanda ya yi sanadiyar fitar wasu ɗanyun jini daga kirjin. Kafin su furta wata kalma, tuni na saduda na barwa Allah komai, ban da istigifari ba abin da nake yi, saboda na san ba zasu bar ni ba. "Dawo nan ka tsugunna sannan ka juya ka kalli bayanka" Wata murya mara imani da tausayi ta faɗa, da hanzari na bi umarninsa. "Makira ta ho ga aikinki ya fito, zo ki aika mana shi kiyama, su je ma taho, tunda iyayensu ba sa sonsu" Da sauri na runtsa idanuna, sannan na fara maimaita kalmar shahada cikin wani kufceccen hawaye wanda ya taho ba da umarnina ba. Cikin kiftawa da Bismillah, na ji dirar wata kara ta ƙugi, wanda ban san ta me ye ba, sakamakon idanuna a rufe ne. "ku mu gudu! ga sunan sun ƙaraso zasu kashe mu" Abin da na ji ɗaya daga cikinsu ya furta, da sauri na buɗe idanuna, wani katon wadataccen jirgine da ake kira ds jirgi mai sauƙar ungulu ya nufo ni, wanda tuni su sun ɓar wurin a ɗari, da sauri na fara neman tashi don ceton raina amma na ji wani sauti na faɗin. "karka motsa idan ba haka ba, zan sauke maka dalma" Jin haka ya sa na dakata da ƙudurina na naƙi mikewa dan ganin kayan sojojin dake jikinsu. Bayan mun dawo jihar Kowa, kai tsaye ma'ajiyar sojoji muka nufa inda suka dunga min tambayoyi a yadda na tsinci kaina a wannan halin, inda na kwashe labarin komai na faɗa musu. "Innata! Innata!" Abin da na tsinci bakina na furtawa, inda naga an kallo ni, bisa halamu maganar zuciyata ta fito sarari. "Innar ka tana tafe domin mun sanar da labarin cikiyarka a gidajen tibi da gidajen rediyo" Wani nauyayyen ajiyar zuciya na sauke wanda ya tarar min tun gabanin makonni uku da suka gudana. Bayan mintina goma da kammala cin abincina na jiyo sautin Inna cikin kuka ta na faɗin. "Yana ina Faisal? yana ina Faisal?" Haka ta runka faɗi har ta ƙaraso inda nake a tsugunne ta taho ta rungume ni tare da shafamin kai da faɗin. "Ba ga irinta ba Faisal! lokacin da na ce maka karka je wannan garin saboda abubuwa da suke faruwa, amma ka tubure sam ka ƙeƙasa ƙasa ka furzar da maganata ka yi gaban kanka, to yanzu dubi halin da ka shiga, da yanzu labarin ya sauya daga rayuwa zuwa mutuwa" Shiru na yi saboda tausayin Innata ni kaɗai ta haifa ga shi ta tsufa, wasu hawayene suka sake kufce min, inda Inna ta ɗora da. "wannan kaddara ce babba, an sauke karatun alqur'ani sau ba adadi duk akan ka, sanadinka na je ƙauye na sayar da abin da mahaifinka ya mallaka da dabbobinsa, amma san ko rabin kuɗin da suka nema daga miliyan uku ɗin ba a samu ba, ko da na saka gidanmu a kasuwa yau ne ranar da za a kawo min kuɗin, sai ga shi Allah ya kwatoka da kyar, lallai na sha wahala Faisal a ɗan takin nan, saboda haka wannan darasi ne gareka ga kuma waninka"
  Apr 1

 • Jibrin Adamu Rano ZOBENA 02 ©Jibrin Adamu Rano Bayan ta sa ƙaninta ya ɗakko mana tabarma ta shimfina mana a rumfar ƙofar gidan su mun zauna ne na fara bata labarin BABI NA FARKO    "A wata makaranta ce ta 'ya'yan masu yatsu da yawa al'amarin ya faru, yau kimanin shekaru shida zuwa bakwai da bamu labarin..."    "Su waye kuma masu yatsu da yawa?" Nafisa ta tari numfashina.    "Masu hannu da shuni mana." Na yi maganar cikin yanayi na murmushi da mamakin yadda aka yi ta kasa ganewa. Abin da ya ƙara bani mamaki shi ne shima hannu mai shunin bata san me ake nufi da shi ba, don haka ne na yi mata ta yaren gwari.    "Masu kuɗi nake nufi to." Na ɗan tsahirta kana na ci gaba.    "Makaranta ce sakandire ta mata zalla, makaranta ce ta jeki ki dawo. Amma fa kamar yadda na faɗa miki duk yarinyar da kika gani a cikin wannan makarantar ko dai 'yar mai kuɗi ce ko kuma wani ne ya tsaya mata.    To a ajin manyan ɗalibai na makarantar ne wasu ɗalibai su biyu Salima da Rufaida suna zaune suna rubutu kamar da wasa Rufaida ta ƙyalla ido a kan yatsan Salima wanda ta hangi wani zobe na gwal mai matukar ƙyalli a jiki. Cikin wani yanayi na murna, ɗoki da kuma zumuɗin ganin zoben ta fara yiwa ƙawar tata magana.    " 'Yar rainin wayo! Dama ke kika ɗaukar min zobena kina ji ina ta cikiya kika yimin kunnen uwar shegu? To asirin ki ya tonu na gan shi sai ki bani abuna." Ta yi maganar ne cikin dariya, don haka Salima ta yi tunanin cewa zoben ne ya burgeta shi ya sa take tsokanarta. Kawai sai itama ta yi dariya bacin ta fakaici idon malamin da yake yi musu darasi a wannan lokacin kar ya hangosu suna surutu, ta yi magana cikin raɗa-raɗa.    "Kema zoben ya yi miki kyau kenan?" Bata jira ta amsa ba ta ci gaba.    "Wallahi Muttaƙa ne ya bani shi jiya da daddare da ya zo gidanmu zance, kowa dai yana yabawa da zoben." Jin haka ne ya sa Rufaida haɗe rai, tunaninta ta yaya Salima za ta raina mata hankali, ta sace mata zoben da saurayinta Kamal ya bata tana cewa itama wai saurayinta Muttaƙa ne ya bata. Don haka rai a ɓace ta sake jaddada ƙudirinta cewa lallai nata ne.    "Don Allah ba na son wasa ki bani zobena tunda dai na riga na gan shi. Wallahi zoben nan da kike gani tun daga Indiya Kamal ya kawo min, shi ya sa kika ga na damu sosai da ɓatan shi saboda nasan halin Kamal cewa zai yi ban damu da shi ba ne shi ya sa har na yi sakaci da zoben shi ya ɓata." Ta ƙarasa maganar ta na mai miƙa hannunta kan yatsan na Salima da niyyar ta cire zobenta kamar yadda zuciyarta take raya mata ta yi.      "Mtwsss..!" Salima ta ja tsaki ganin yadda Rufaida ta wani daƙumi zoben zata fusge mata shi.    " Bana son iskanci. Don Allah sakar min zobena ni kar ki sa ya yi datti, don Wallahi ina ji da Zoben nan kamar yadda nake ji da Muttaƙana, shi kuwa Muttaƙana ina ji da shi kamar yadda na ke ji da raina. Kinga kuwa bai kamata ki yi min irin wannan wasan ba don gudun kar a samu matsala." Ta ƙarasa da dariya dai dai lokacin da ta fusge hannunta daga cikin na ƙawar tata tana mai bin zoben da kallo tare da yabawa da yadda yake ta faman wani sheƙi da walwali.    Rufaida fuska a ɗaure ta ce    "Wasa!" Ta maimaita kalmar ne tana kallonta da alamun mamaki.    "Ban gane me kike nufi da wasa ba? Ko an faɗa miki yadda ba kya wasa da abin da ya shafi Muttaƙa nima ina yin wasa da duk abin da ya shafi Kamal ne? Don Allah ni ki cire min zobena ki bani bana son iskanci da wulaƙanci." Ta ƙare tana turɓune fuska, a wannan karon yanayinta ya fi koyaushe nuna cewa lallai da gaske take furucin zoben nata ne.    Abin na ƙawayen biyu kamar da wasa haka ya fara, kafin daga bisani da kowaccen su ta fahimci ashe fa da gaske ƙawar tata take yi. Ita Rufaida kallon ɓarauniya take yiwa Salima wacce ta sace mata zobenta da ta daɗe tana nema, zobenta da ɓatan shi har bacci ya hanata yi. Yayin da ita kuma Salima take kallo Rufaida a matsayin wata hamshaƙiyar 'yar rainin hankali wacce tana ji tana gani Muttaƙanta ya bata zobe amma zata dinga da'awar wai nata ne har tana daƙumar mata shi. Wannan shi ne abin da ya sa rigima ta kacamewa ƙawayen biyu a cikin ajin ta yadda dole sai da Malamin ya fahimta, rigimar da ta yi ƙarfin da ta fi ƙarfin malamin har ta je gaban shugabar makarantar Hajiya Rukuba Maryama (Kamar yadda take amfani da sunan). Hajiya Maryam cikin takaici da ɓacin rai take tambayarsu abin da ya haɗa su har suke faɗa a gaban malam, sanadin da ya sa malamin mai amsa suna malam Nasir ya ɗakko zoben kenan yake nunawa shugabar makarantar akan abin da suke faɗan. Hajiya Maryama ta karɓi kyakkyawan zoben da ya burgeta bisa ganin yadda yake ta faman wani sheƙi da walwali tana jujjuya shi a hannunta cikin ƙare masa kallo da tunanin lallai zoben kam ya cancanta a yi rigima a kan shi saboda kyan tsarin shi da alamar da ke nuna tsadar shi. Aikuwa kafin ta bud'i baki ta yi magana yarinyarta budurwa sa'ar matasan 'yan-matan biyu Salima da Rufaida mai amsa suna Hajara da take zaune a kan kujerar gaban teburinta ta yi farat ta miƙe tsaye tare da bararo idanuwanta waje cikin ƙarewa zoben kallo tare da alamun da ke nuna mamakinta ƙarara ta ce. "Wallahi Umma zobena ne ba nasu ba ne! Wallahi Umma zobena ne wanda nake ta faɗa miki cewa ya ɓata ɗinnan tun kwanaki." Ta furta hakan jikinta har wani rawa-rawa yake yi tana ƙoƙarin fusge zoben a hannun mahaifiyarta. Ba mahaifiyar tata da ta bita da kallo ba, hatta aminan biyu Salima da Rufaida da kuma shi kansa malam Nasir da kallo kawai suka bita kowa zuciyar shi a cunkushe da mamakin yadda daga ganin sarkin fawa zaisa har miyarta ta yi zaƙi haka, daga ganin zobe kawai sai ta ce zobenta ne?"
  Jan 15

 • saadiyya husaini 1.114 2.Abu hassan Abu malili Al shadhili ya rasa a 939 A.H a cairo. 3.sayyaduna usman sbd ya aure yayan manzon Allah guda biyu rukayya da ummu khursim 4.Na r ibn muhammad abu al laythal-samardaqandi 5 bazara-zara 6.shamuwa-uwa 7.Niger (niger state) 8.1october 1960
  November 16, 2020