Mambobi

  • Lawan Dalha Just a test post to see that....
    October 26, 2021

  • Rukayya Ibrahim lawal *HALITTAR ALLAH CE* 🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼 *(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)* *ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *A SANADIN KAMA* *RASHIN GATA* *WATA ƘAWA* *AND NOW* *HALITTAR ALLAH CE* Ga masu buƙatar na tallata masu hajojinsu a shafukan littafina dama shafukana na sada zumunta kamar instagram, whatsapp, telegram, facebook da sauransu sai su tuntuɓe ni ta wannan number __08109634202__ Kowacce irin haja je gareka zamu tallata ma cikin rahusa insha'allah. ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* PAGE 59-60 Nan fa mutanen dake gidan suka birkice, yaya Habi ta ajiye cokali tana neman guduwa amma ina! Kafin ta gudun abun ya ƙaraso. A kiɗime Hajiya ta ɗaga kanta don ganin menene ke wannan Masifar ƙarar. Wani curin dunƙulallen abu ne a hankali yake ƙara girma har faɗinsa ya mamaye ilahirin inda yake. Zuwa can kuma ya rabu gida goma. Hanne da tashin hankali ya korota daga kitchen ta nufo falon, a nan ta tarad da sabon tashin hankali. Amma duk da haka bata yi kuskuren komawa kitchen ba, domin kuwa duk abinda ya koro ɓera har ya faɗa wuta ba ƙaramin abu ba ne. A hankali waɗannan curin suke mulmulowa sai hayaƙi suke fitarwa ga wasu sautukan Muryar yara iri-iri dake fitowa daga curin. Suka nufo inda yaya Habi, Hajiya da Hanne suka manne waje ɗaya don tsoro.. Wani tsalle yaya Habi ta daka, tana yin sa'ar ƙetare abun ta yi wuf ta faɗa ɗaya daga cikin ɗakunan dake falon ta rufo da makulli tana mayar da ajiyar zuciya. Hajiya kuwa ganin curin na nufo ta, tun bai ƙaraso gare ta ba hankalinta ya gushe ta fadi a gun kafin ta kai ga suma ta ji wata mummunar murya na faɗar "Kin tsani ganin Musakai a rayuwa koh? To kishirya don kina dab da tsanar kanki." Daga haka aka bushe da matsananciyar dariya mai ƙara birkita birkitacce. Kafin idonta su ƙarasa rufewa ta hango bayyana wata mummunar halitta a gabanta mai ido ɗaya saman hanci da wani wagegen baki. tsaya faɗa maku munin halittar bata lokaci ne don tafi Abdul muni nesa. Haka halittar ta ƙarasa ga hajiyar ta rungume ta. A take idon hajiyar ya rufe ruf alamun ta suma. Hanne kuwa yau taga tashin hankali da bata taɓa ganin irinsa ba. To wai duk me wannan abun ke nufi? Me ya janyo musu wannan masifar? Tana tsaka da wannan tunanin ta ji an sure ta anyi sama da ita. Waige-waige ta hau yi tana ƙwala ihu amma bata ga abinda ke riƙe da ita ba. Kawai ta ganta a sama. Can kuma aka makata ga ƙauren ƙofar falo ta faɗo a galabaice. Zahirin siffar Abdul ce ta bayyana a gabanta, amma wannan ba Abdul bane don ya ninka tsawo da kaurinsa sau biyar. A haka ya nufota ya shiga yin Ball da ita tun daga ƙofar falon har zuwa harabar gidan. Sai ihu take amma a banza banda Ƙasimu mai gadi ba mai jinta. Sauran ma'aikatan gidan duk barci suke. Shima Ƙasimun ashe rabon ya girbi abinda ya shuka ne. Don haka aljani Mazkud da ya zo a siffar Abdul ya haɗe su gu ɗaya shida Hanne ya ci gaba da wahalar da su har zuwa lokacin da ya tabbatar sun karɓi saƙo sannan ya ɓace yayin da suke jiyo kakkausar muryarsa na faɗar "Sai ku kiyaye gaba, ko wane mai kama da Abdul kuka kuma wulakantawa zamu gamu ne." Daga haks suka ji tsit kamar Muryar bata taɓa wanzuwa a gidan ba.. Ai da gudu suka watse kowa ya nufi maɓoyarsa. @@@@@@@@@@@@ A bangaren Abdul kuwa haka ya cigaba da yawo cikin gari yana Bara, ko kwano baya da daƙyar aka samu wata mata ta taimaka ta ba shi kwanon. Haka ya yi ta yi, wani lokacin idan mutane suka gan shi su gudu musamman yara. Masu ƙarfin halin cikin mutanen ne ke tsayawa su ba shi haƙuri, masu abin ba shi su bashi. Idan yamma ta yi ya dawo malaɓarsa ya zauna. Haka ya ci-gaba da aikatawa tsawon shekara biyu zuwa uku, har wasu daga cikin mutanen yankin suka fara sabawa da shi suna saka shi aiki kamar wanki,wanke-wanke suna biyan shi. Don a lokacin ya kai shekaru 16 a rayuwa. Ɓangaren Mahmud kuwa har zuwa lokacin yana waccan ƙasar bai san halin da ake ciki ba. Don kuwa tun bayan fitar Likitansu daga gidan ya samu kiran gaggawa zuwa ƙasar Turkiyya, wannan dalilin ne ya mantar da shi kudurinsa na sanar da Mahmud halin da ya samu Abdul ciki. Shiko Mahmud duk sanda zai kira Hajiya sai ya nemi ta haɗa shi da Abdul su gaisa amma sai ta samu karyar data masa. Daga ƙarshe ma tace masa ta maida yaron boarding school ne. Sosai ya ji daɗin ganin Hajiyarsa ta karɓi yaron. Bai san cewa ta ɗinke shi a bai-bai ba ne. @@@@@#### A gidan Hajiya bayan ƙura ta lafa yaya Habi ta buɗe ɗakin ta fito. Nan ta samu Hajiya a some, kinkimarta suka yi zuwa asibiti. Sai da likitoci suka kwashe tsayin wasu awanni a kanta kafin ta dawo hayyacinta, amma jininta ya hau sosai. Kuma tun tashinta take jin ƙafarta ɗaya wani iri. Sosai ƙafar ke ciwo, likitoci sun yi iya ƙoƙarinsu ba su gano komai ba. Daga ƙarshe suka yi tunanin ko hawan jinin ne ya taɓa ƙafar don haka suka ɗora ta akan magani. Tun a lokacin Hajiya ke fama da matsanancin ciwon ƙafa, anyi maganin har an gaji. Bayan dawowar su gida yaya Habi ke tambayar musabbabin wannan tashin hankalin. Cikin damuwa Hajiya ta dube ta tace "Wani nakasasshen yaro ne Son ya zo da shi nan gidan, da zai tafi ya ban amanarsa, shine na saka aka jefar da shi. Dalilin haka aljanu suka zo mana a siffarsa suka tsorata mu don ɗaukar masa fansa. Wannan shine tunani na." Girgiza kai yaya Habi ta yi tace "Meyasa kika kore shi?" "Halittarsa nake tsoro, don wannan bai yi kama da mutane ba,rabin fuskarsa fa a shafe take." Zaro ido ta yi tare da nisawa ta ce "Tab! Wannan yaron sai kace yaron da Zulaihar Baba ta haifa? Kinsan lokacin da ni aka je Sokoto suna, amma a ƙagare na yi sati ɗayan ni da na je da zimmar zaman jego." Ita ma Hajiyar fiddo ido ta yi tace "Yaya dama ƙanwata da nafi so kalar abinda ta haifa kenan shine baku sanar mun ba? Kin san fa lokacin Alhaji yana ciwon ajali shiyasa ban je ba. Amma kuka ce mana yaron kyakkyawa ne kuma yana ƙalau?" Shiru yaya Habi ta yi kamar ba ita aka tambaya ba. Nisawa ta yi ta ce "Allah sarki ƙanwata mai yawan sona, kin mun rana, kin zame mun lema a lokacin da rayuwata ta shiga wani yanayin ƙunci. Ina ma ace a lokacin da kika mutu na san wannan, da duk tsanata da Musakai sai na riƙi wannan yaron naki hannu biyu na masa gata, da ban wulaƙanta ko da mai irin siffarsa ba..." Ta faɗa tana hawaye. "Allah ya jikanki da Rahama ƙanwata. Na miki alƙawarin zan je har Sokoto don karɓo yaronki daga hannun dangin ubansa, ba wanda zan bari ya wulakanta jinina. Ko waye kuwa ya yi kuskuren aikatawa sai na yi Shari'a da shi." Haka ta yi ta sambatu har sai da yaya Habi ta dakatar da ita da faɗar "Ya isa haka, haƙuri zaki yi, ki ci gaba da masu addu'a." @@@@@@@@@@@@@@ Bayan kamar watanni bakwai da wannan maganar Hajiya ta shirya zuwa Sokoto don karɓo yaronta. A da taso ta bari har ta ji damar ƙafa, amma da taga ba alamun haka, ta ce "Ina amfanin baɗi ba rai?" Gwanda ta je tun lokacin da take da abun yi. A ranar wata Assabar Hajiya tare da wani kawunsu (dake zaune a nan Kaduna) suka yiwa Birnin shehu dirar mikiya..... To fah! Readers Hajiya na neman yaronta, wanda ta wulakanta fa waye? Ya zasu kwashe tsakaninta da a halin Alh Munir dama Hajiya Hasina? Ya rayuwa Abdul zata ci gaba da wakana?. Ku biyo alƙalamin Ummu inteesar don ji ya zata kaya. More comment more typing Ummu inteesar ce.❤️😍
    February 15, 2021