Featured Create an Ad

Mambobi

 • Jidda Washa Aslm barkanku da safiya yan'uwa maza da mata, Allah ya bamu albarkar wannan rana, ya sa da mu da alkhairinsa a ko da yaushe.
  Oct 14

 • Nafi'u adamu Salaam friends barkammu dashanruwa
  May 12

 • Abubakar Sulaiman II Yakamata Yan Arewa Mudaina Yaudarar Kanmu.Ni Banga Wata Tsiya Da Buhari Yakeson Yayiwa Arewa Ba Wanda Har Zaisa Ace Yan Kudu Suna Bakin Ciki Wanda Shine Yasanya Suke Wannan Zanga-zanga Domin Kawo Karshen Mulkin Buhari Ba. Talauchi me kawai yayiwa mutane katutu a ko ina. Angama Lockdown din Jahilci.Anzo Anwayi gari babu kudi a hannun mutane babu Sana'a Ga Tsadar Rayuwa Yaya Baza ayi Tashin Hankali Ba.
  Wed at 8:59 PM

 • Rufaida Umar NADAMAR FURUCI Rufaida Umar. "Hoo! Ka ji kunya! Wallahi ka ji kunya! Tirr! Da miji irinka!" Wata siririyar mace ce ta ci ?amara a daidai majalisar wasu dattawa tana sababi. Wanda ake dominsa, ya sunkuyar da kai yana jin wani ra?a?i a ?asan ransa. Ga yara da manya an taru ana kallonsu. Wani tsamurmurin dattijo dake gefensa ya dubi matar yana nuna ta da yatsan shi manuniya. "Wallahi Asabe ki ji tsoron Allah, ki tuba tun kafin lokaci ya ?ure miki! Wane irin wulakanci ne za ki biyo mijinki bainar jama'a ki ci mutuncinsa? ?arin aure a kansa aka fara ne?" Jin haka ya sa ta yi kan Dattijon nan da sababi. "Kai Amadu! Wallahi ka yi gaggawar fita daga idanuna na runtse! Dama ai ko ba ka nuna hali ba na san ku ne munafukan da ke hure mishi kunne! Wato ga annoba, yana kawo muku karya da gaskiya a kaina kuna ha?uwa ku zage ni tas! Hakan ka?ai bai yi muku ba sai da kuka ga zai auro min sa'ar ?iyata. Kai ai da ace ma na samu ciki da wuri da tuni na aurar da Yaha. Amma tsabar wula?anci, a rasa wa za a ha?a ni kishi da ita sai yarinya ?ar bana-bakwai! To wallahi karr nake kallo ku! Aure ne dai ina raye Murtala bai isa ya yi shi ba. Idan kuwa yana ja da ni to mu zuba mu gani! Ya dai ji kunya wallahi, an girma ba a san an girma ba!" Ran dattijan ya ?aci, Sule wanda ya fi su harzu?a ya mi?e tsaye jiki yana rawa. "Mutuniyar banza da wofi! Yau kin ?ara tabbatar da ko ke wace ce! Na yi tirr da shawarar da na ba Murtala na aurenki, da ace na san za ki zame mishi bala'i da masifa da ban soma ba! Kuma Asabe mutuwa ce sai dai ki yi, aure dai babu fashi! ?an'uwanmu ba zai mutu da annoba irinki ba! Shashasha kawai!" Wata irin shewa ta sanya gami da sakin gu?a tana rausaya kai kamar ta?a??iya. "Ayyiriri nanaye! Yaro bai san wuta ba sai ya taka wallahi! Mu zuba mu gani Sule, gobe dai za a daura aure ko? To, ni Asabe na ce mu zuba, na ga uban da ya isa ya ?aurawa Murtala aure. Zan kashe mutum na kashe banza wallahi! Duk abin da ya biyo baya ka yi kuka da kanka!" Daga haka ta bar wajen tana sababi da kururuwa da cika-baki. Murtala har lokacin bai ?ago ba sai zubar da hawaye, sai da Amadu ya kori dukkan jama'ar da suka taru kafin ya soma yi wa Murtala magana cikin fa?a-fa?a. "Me ya sa ba za ka iya sakin wannan matar ba? Ha?uri na me kake yi da ita har haka Murtala? Cin mutumcin da take maka ya yi yawa kai kuwa kamar ma ba gani kake ba! Akan wane dalili? Idan yara ne Allah Ya raya maka su. Amman wannan cin mutumcin da me ya yi kama?" Sule ya yi ?wafa. "Ka ?yale shi! Tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka ai, na ce ka rabu da shi kawai Amadu! Kunnen Murtala ba ya jin laifin Asabe, idanuwansa ban ce suna gani ba. Amman na rantse da Allah ba macen da ta isa na zauna ta ci mutumcina irin haka! Ka zama namiji, kuka aikin banza ne! Wannan ba matar rufin asiri ba ce." Shi dai Murtala ba baka sai kunne, ya gama sauraronsu, da ?yar ya saki ransa bayan sun ?arashe da yi mishi nasiha mai kwantar da zuciya kafin daga bisani su hau zolayarsa akan amaryar da zai yi. Nan ya ?an sake amman labarin zuciya a tambayi fuska. *** Washegari da misalin ?arfe takwas, Asabe ce tsaye ?i?am a ?ofar ?akin Murtala tana dakon fitowarsa duk kuwa da ta sanya sakata ta rufe ?akin gam tun daren jiya da ya dawo gida. Bugun duniya ya yi bata bu?e ba, abinci ma cewa ta yi wanda su Amadu suka ba shi a majalisa ya ishe shi. Da Asuba ma bata bu?e ba shi ma bai ?wan?wasa ba. Wannan ya sa tana tashi, ta kasa, ta tsare a bakin ?ofar. Yaranta sai safa da marwa suke yi suna masu jin takaicin halin uwarsu, yayin da masu goya mata baya na yi. Atika wacce ta fi kowannensu tausayin baban nasu ta dube ta. "Haba Umma, don Allah mene ne haka kike yi? Kin hana Baba fita alhalin kin san yau..." "Atika zan ci ubanki! Zan ci ubanki wallahi muddin ba ki fita a hanyata ba. Shegiyar yarinya marar kishin uwa. Ku wuce ku tafi makaranta tun ban karya ?afafunku ba." Atika ta goge hawayenta, ta ja hannun ?annenta su biyar suka fice daga gidan. Suna fita ta ci karo da Amadu da Sule sai wani Kawun babansa Murtala a waje. Ta gaishe su. "Kira mana Babanku mana, lokaci na ?urewa." A sanyaye ta labarta musu abin da ke faruwa. Wannan ya sanya suka shiga gidan da sallama, musamman ma Sule wanda ya fi su sha?a. Asabe na zaune saman kujera tana girgiza ?afa tana cin ?osai mai zafi, ba ta ko jin zafinsa saboda yanda ranta ke suya. Kallon tara saura ta yi musu kafin ta kau da kai tana ?wafa. "Asabe wace irin mata ce ke? Me ya sa ba kya jin bari?!" Kawu ke wannan maganar cikin tausasan lafazi don a tunaninsa zai sa ta tausaya. Ta mi?e tsaye gami da furzar da ?osan bakinta, harara ta watsa musu da jajayen idanunta wa?anda kishi ya rinar. "Lamido kake ko Rilwan? To wallahi ba ka isa ka aurar da mijina ga kowace shegiya ba, ba zan yarda ba! Mutu ka raba ni da Murtala! Ba wanda ya isa ya..." Ai bata kai ?arshe ba, Sule ya dauke ta da kyakkyawan mari yana huci. Wani irin hantsilawa ta yi, ta daka tsalle ta mi?e ta yi kansa tana kantara ashariya. "Ni! Ni za ka mara har gidan aurena Su.." Bata kai ga ?arasawa ba ya ?ara dauketa da wani marin, ya angiza ta gefe. "An mare ki asararriya! Na ce an mara ?in! Banza da bata san darajar aure ba! Kuma wallahi kika yi wani yun?urin hana mu fid da Murtala daga gidan nan sai na zage na ci ubanki!" Ya dubi Amadu. "Amadu bu?e min ?ofar nan!" Amadu ba musu ya ?arasa ya zare sakata, shi kuwa Sule suna fa?i in fa?a da Asabe wadda ta koma tamkar zararriya. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Furucin Amadu ya maido da su hayyacinsu. Gaba?aya suka dube shi. Kawu ya ?arasa ?akin da sauri. Ganin haka duk suka shiga ciki. Abin da suka gani ya yi matu?ar gigita su. Murtala ne kwance, jini na fita ta kunne da hancinsa. Iyakar ru?ewa sun shiga. Wata irin azabbabiyar ?ara Asabe ta saki. Ta juya da zummar fita daga ?akin sai dai cikin zafin nama Amadu ya tare ?ofar. "Annamimiya! Ina za ki?! Ina za ki je bayan kin kashe shi?!! Babu inda za ki fita!!" Asabe ta fashe da kuka. "Wallahi na rantse da girman Allah ban kashe Murtala ba! Wallahi ban kashe shi ba!" Kawu wanda ke fid da hawaye jikinsa har rawa yake ya dubi Sule. "Sulaimanu, kira ?ansanda." Jin haka gaba?aya Asabe ta ?ara rikicewa tana ha?a su da Allah su rufa mata asiri, rantsuwa sosai ta shiga yi akan ba ita ta kashe Murtala ba, amman ina! Babu mai sauraronta. Atika na cin karo da gawar Babanta ta fasa ?ara ta fa?i anan ta sume. Hayaniyar ta jawo hankalin makwabta, sai ga shi an soma cika gidan. Babu jimawa Sule ya dawo tare da ?ansanda, Asabe na ta rantsuwar ba ta kashe mijinta ba sai dai babu wanda ya saurareta. Kowa ma ya bu?e baki cewa ya ke yi za ta aikata duba da irin furucin da ta dinga yi na kashe rai. Har tana ikrarin MU ZUBA MU GANI. Da wannan aka tafi da Asabe ofishin 'yansanda. Iyakar binciken ma'aikata ba su gano ta?aimaiman abinda ya kashe Murtala ba. Haka aka ci gaba da tsare Asabe kafin a kammala shari'a. Iyakar gaskiyarta ta fa?a akan ba ta kashe Murtala ba, sai dai babu wanda ya saurareta ballantana ya yarda duba da munanan kalamanta wa?anda da su lauyan dake kare ha??in Murtala ya ci galabar da Al?ali ya sa a tsare ta. Kwananta uku a gidan yari, tana zaune zugum tana tunanin munanan halayenta, aka aiko tafiya da ita ta yi ba?o. Bata ta6a zaton akwai wanda zai duba maraicinta ya ziyarce ta ba, haka nan Atika tun a harabar kotu ta ce babu ita ba ita saboda ta kashe ubanta. Bayan an kai ta ?akin ganawa da ba?i, ta saki baki ganin ba kowa ba ne sai Sule. Wani irin murmushi yake yi mata na mugunta har ta samu wuri ta zauna. Bayan idanu sun ?auke a kansu ya soma magana. "Asabe kenan, sannu kin ji? Ai dama wanda ya riga ka kwana to zai riga ka tashi. Har kina zaton Ni zan mance irin tsantsar yaudarar da kika yi min a zamanin samartaka? Wannan ka?an kika gani, sai na sa an kashe ki kamar yanda na ba da Murtala ga Dodon tsafi." Ya dan yi waige-waigensa kafin ya dube ta yana murmushi cikin ra?a ya ce. "Ni ne silar mutuwar mijinki, kuma ni zan zama silar taki mutuwar. Ko a haka na bar ki na kashe ki Asabe! Wannan somin ta6i ne daga ni Sule." Cikin rawar murya ta nuna shi da yatsa. "Kai.. kai...ne..su..?" Dariya ya saki a hankali. "?warai kuwa, ni ne nan silar mutuwarsa domin a duniya babu abin da nake so ban da shahara da dukiya. Ko ta wane hali sai na samu." Wata razananniyar ?ara ta saki, ta cakume shi da hannayenta tana kuka. "Sule ?an'uwansa?! ?an'uwansa?! Allah Ya isa tsakanina da kai!" Ganin tana neman tona asirinsu ya yi saurin fincikewa, gandiroba ta yi saurin zuwa ta rirri?eta. Tana zage-zage da tsinuwa sai dai ba wanda ya kula da sambatunta. Sun ga fin haka a gidan yari, Sule na murmushin mugunta har aka shige da ita ciki sannan ya juya ya fice daga wurin zuciyarsa tas ya bar Asabe cikin NADAMAR FURUCI. *KARSHE*
  October 23, 2019

 • Abdullahi Yusuf Assalamu alaikum, INA maku fatan alheri tare da fatan Allah ya zaunar mana da kasarmu lafiya
  Oct 11

 • Zaharadden Nasir *HAUSA AUTHORS FORUM* (H.A.F) Na farin cikin sanar da daukacin marubuta, makaranta, manazarta, mawaka. Da ma dukkan masu sha'awar harkar adabi cewa; Kungiyar ta shirya tsaf don dawowa ci gaba da gabatar da tarukanta na wata-wata da ta saba yi, bayan hutu na tsawon lokaci da ta dauka a sakamakon annobar Corona. Kungiyar zata ci gaba da gabatar da tarukanta a bisa bin tsarin shawarar hukumar kare cututtuka masu yad'uwa wato NCDC. Za a dawo yin tarukan ne a; RANAR: Lahadi 25 ga watan Oktoba, 2020 WURI: Kurna Primary, Katsina road, kusa da Akija Motors. LOKACI: 11😸0am. Allah Ya bada ikon zuwa. _*Sanarwa*_ _zaharadden nasir_ *P.R.O 1* A madadin shugabanni.
  Thu at 9:22 PM