Mambobi

 • Maishaq Muhammad Wai Mai Yasa Al’ummah Duk Da Irin Kiranye Kiranyen Da Malamai Keyi Akan Gyaran Zuciya Basaji Ba Sa Kuma Yi Sai Watan Ramadhana Yazo, Anan Ne Zakaga Jin Tsoron Ubangiji Amma Da Zarar Watan Ya Gabata Sai Kuma Akoma Tamtar Ba’ataba Jin Tsoron Ubangiji Ba?!
  Mar 31

 • Kamala Minna ME YA SA...? Na kasa fahimtar cukumurɗar nan, lamarin yana raunata min lissafi sosai. Akwai mazaje da yawa da suke yiwa mace kallo wata maras tunani da lissafi a cikin rayuwarta. Bata da iko ko alfarma a fannin a yi shawara da ita,ko a zauna da ita cikin wani zance ko lamari da ya jirkice ake neman mafita. Sai kaji ana cewa bata da lissafi ko shawarar da za ta bayar har anyi amfani dashi, domin bata san kanta ba, shiririta kawai zata yiwa mutane. Ba abin takaici da ciwon rai, sai Mazaje da suke yiwa matansu kalar fahimtar nan, sai ka ji namiji na cewa ba zai nemi shawara da matarsa ba, mace ce ita kanta bata san kanta ba shiririta za ta yi masa. Na kasa fahimtar tunanin mazajen nan. Shin mace ita ba mutum bane ko kuwa bata da zuciya da kwanyar da za ta yi tunani da ita ce?. Shin namiji ne kawai mai hangen nesa da sanin ya kamata ko ya ya? Na kasa fahimtar gangan ɗin nan. Lissafin mace da namiji na sani ba ɗaya bane na amshi Farillar nan. Amma mai yasa ba za ake yi musu adalci ba wajan ba su dama a cikin neman mafita? wannan tauye haƙƙi ne da mai da mace ta ji a ranta ita ba wata bace hakan kuma damuwa ce da ke sanya ciwuka masu girma a zuciyar mace. Don Allah ake adalci Kamar yadda ake ganin mace bata cancanta da lissafin neman mafita ba, to haka shima namiji. Akwai mazajen da tunaninsu in aka sanya shi a sikile wallahi Allah ko an amshe shi a matsayi mafita faɗuwa za ayi warwas macen da aka raina sai ka ga ita nata da aka mai kallon hadarin kaji ya yi amfani. Kalmar Wasu Mazan da wasu matan ya kamata ace ana ado dashi wajan yanke hukunci ba wai ayi jam'u wanjan faɗin MATA ba hakan rashin adalci ne. Matarka fa sirrin kace duk yadda za kayi saɓa-ta juya-ta sunanta ba zai taɓa canzawa a sirrinka ba. Ya kamata ake adalci. An san ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, don haka ake saka kalmar 'Wasu' a duk abinda za ayi in har ana son adalci. Zama kayi nazari da tunanin wani duhu da ka shiga tare da iyalinka ba karamar shakuwa da girmamawa da sanya zukatan iyalan naka alfahari hakan ke yi ba, don Allah ake duba ana saran bakin gatari. Ɗiya mace daraja ce da ita, girma ne da ita, in ka kira mace duk mara lissafi kana da uwa fa ita a wani mataki zaka ajje ta?🤔 Allah ya kyauta. KamalaMinna.
  November 3, 2020

 • Saifullah Ibrahim TSAKIYAR RANA (Gajeren labari) Na Saifullah Ibrahim. Ɗan acaba ne ya yi gamo da ƴan sanda. Kamar dai sauran masu abubuwan hawa duk ya ji ya tsargu. Shi in ma ba ƙaddara ba, ba son bin wannan hanyar ya ke yi ba. ko da kuwa fasinjansa kusa da wurin za a sauke shi, ya fi gwammace ya kurɗa ta kwanonin da zai kaucewa haduwa da jami’an hanya koda kuwa zai fi ƙona fetur ɗinsa. Fitilar bada hannu na nuna saura sakan 55 su tafi. A tsallaken titi Madu ya cire hular inifom ɗinsa. Rana ta yi walkiya a kan molonsa. Yasa hankaci ya goge zufan da ya taru a kansa da fuskarsa. Ya hango ɗan acaɓa ya ƙage tsakanin motoci. Da ɗan acaban nan ya ga dan sandan nan ya nufo shi sai ya dubi hanya. Saura sakan 15. Ya duba ya ga ko da sararin da zai iya kutsawa; Motoci sun yi masa qawanya ta kowane haugi. Ɗan sanda da zuwanka ka dubi talotalon da ɗan acaɓan ya dauko da kyau sai ka tsinkawa dan acaɓan nan mari. Fiyau. “Barawon banza da wofi” Marin a bazata ya zowa ɗan acaɓan nan. Zullumin yiyuwar faruwar irin wannan zaluncin da faruwar zaluncin a lokaci ɗaya ya gigita ɗan acaɓan. Fitilar bada hannu ta nuna kore. Kamar dai kore na nufin a ruga, Kowa ya saki tayoyin abun hawansa ya arce. Ɗan acaɓa ba dama ya tafi. Domin kuwa Madu ya sa hannu ya zare makullin mashin ɗinsa. Shi yanzu wannan cin mutuncin ne ya fi damunsa. Ga mari ga ƙazafin sata. Duk sa’adda ya tuna wannan cin mutuncin sai ya ji takaicin kansa, da bai sa hannu ya rama ba nan take. Da hankalinsa ya komo, ya ga har jama’a sun taru. Cikinsu da yan uwansa ƴan acaɓa. Ya daga hannayensa zuwa sama daidai haƙarƙarinsa, sauran yatsunsa a dunƙule, mununai a tsaye. Ya ce, “wallahi ni ba ɓarawo bane.” Ya duba ya ga koda wanda ya yarda da abunda ya faɗa. Fuskar kowa da waswasi. Ɗan acaɓan bai san abinda ya sato ba. Amma duk da haka ƙarfin gwiwarsa ya karye. Ga zafin rana mai sa mutum ya kiɗime. Haka mutum yake ji idan aka tuhume shi da sata, kuma ba wanda zai bada shaidarsa a kusa. Ya dubi jama’a, ya ƙara rantsewa, “wallahi ni ba barawo ba ne.” Ɗan sandan yace, “jiya da daddare ya tsallaka gidana ya sace mini talotalo”—ya nuna talotalon dake ɗaure akan mashin, ya na huci ya na ƙarawa—“yau sai ka yaba aya zaƙinta. Ba za ka sake tsallakawa gidan ɗan sanda kayi sata ba” Daga jin haka ƴan acaɓar dake wurin suka yi Allah wadai suka watse. Ba su tafi ba sai da wani dattijo ya yi jawabi zuwaga ɗaukacin jama’ar da suka taru a wurin. Ya ce, “wannan sune ɓata gari masu zubar da mutuncin sana'ar Acaɓa. Kowa ya san mu da jajircewa wurin neman na kai. Amma kullum sai an samu ɓata gari masu shafa mana baƙin jini ba mu ji ba, ba mu gani ba. wannan shi ke ɓata mana suna a cikin al’umma. Amma Allah ya isa tsakanin mu da irin waɗannan mutane.” Wannan jawabin ya yi wa ɗan acaɓan ciwo sosai. Wato har an ware shi daga ƴan uwansa, an sanya shi cikin wasu waisu ɓata gari. Da wucewarsu shikenan ya rasa waɗanda suka tsaya masa. Saura yan sanda da yara, mafi yawansu Almajirai ne da masu tallar fiyawata, masu kallon yadda za ta kaya tsakanin ɓarawo da ƴansanda. Da ya duba ya ga hakan, sai duk wani sauran kwarin gwiwarsa ya sulale, bai san sadda hawaye suka gangaro daga cikin idanunsa ba. A na nan za a wuce dashi tashar yan sanda, sai wani dattijo mai saida kayan marmari da lemuka daga gefen titi ya taso. A wurinsa ƴansandan nan ke karɓar bashi suna biya a ƙarshen wata. Dama ya ga tunda aka fara wannan al’amarin ƴansandan nan ba abinda suke ma ɗan acaɓan nan sai hantara da shuri. Ƴan sanda baka yi musu komai ba ma ya ka ƙare dasu, ballantana ma kayi musu sata? Sai ya zo ya sa baki domin a sasanta ba sai an je can ba. amma shi kam ɗan acaɓa ina? Yace shi wallahi ba zai yadda a tafi da talotalonsa ba, bayan duk cin mutuncinsa da akayi masa. Duk inda za’a tafi, sai a tafi. Ɗan sandan ya ce, “ka gani ko, shi banda sata ma, harda ƙarfin hali gare shi” Sai dai dattijon nan bai yarda ƙarfin hali bane. Sai ya tambayi ɗan acaɓan koda wanda zai bada shaida a kan haka? Matarsa kawai ce shaidarsa. Ita ta yi kiwon talotalon tun yana ɗan tsaki. Yanzu ma dalilin siyo mata magani ne zai siyarda Talo-talon amma ya san ba lalle tazo ta ba da shaida ba. ****** Kafin a kira matar ɗan acaɓan tana kwance jikinta ya yi tsami saboda dukan da ta sha jiya. Yanzu dai bayan ƙawarta ta ta zo ta sami fuskarta a kumbure, ta taimaka mata wurin yanke shawarar komawa gida. “E na san yana ƙoƙari wurin ciyar da ke da baki duk abinda bai fi ƙarfinsa ba. Amma ai ba shi ne hujjar da zai maida ke jaka ba. dukan yau daban na gobe daban?” ƙawar tata ta ce, da ta zauna bakin gado. “E, na sani. Amma kin san makauniyar zuciya ce da shi. Sai ya yi sai ya dawo da na sani. Yau ma ba ki ga yadda ya ba ni haƙuri ba da safe” “to sai ki zauna yana dukanki yana ba ki haƙuri ki na tashi. Haka za a cigaba har ranar da ya hallakaki?” “toh yanzu idan aurena ya mutu mai mutane za ku ce?” “hmmm,” ba tasan yadda za ta amsa mata wannan tambayar ba. amma tasan rashin amsar wannan tambayar shi ya ajiye mata da yawa acikin kangi. "Sai ki zauna idan ya kashe ki, mutanen za su zo ta'aziyya" Ta tafi ta barta a cikin raɗaɗin ciwo. Ko da kiran ya shiga wayarta ta riga ta yanke shawara. Ba za ta zaunaba, duk abunda mutane zasu ce, sun daɗe ba su ce ba. Idan ta tsaya ya hallaka ta, mutanen da kansu zasu zo tambayar me ya sa ta tsaya. Mutane ba a yi musu dai-dai. Da ta ɗaga wayar taji baƙuwar murya ance, “Hello.” Har zata ce “wrong number” sai taji ance, “Yan sanda ne daga Tudun wada roundabout kizo ana nemanki. Gabanta ya ce ras. “me na yi?” “in kin zo za ki ji” “toh a gaskiya ni sai na tambayi izinin miji na, kuma yanzu ya fita” “to ai mijin na ki ne muka kama da laifin satar talotalo” Kira ya yanke Tace “Alhaki kwikwiyo.” Ta fahimci talotalon da ake magana akai. Kuma ta tabbata ita ta yi kiwonshi tun yana ɗan tsaki. Amma ita yadda take ji a lokacin ko kulle mijinta za a yi sai a kulle shi. Idan ma ta tafi ba amfanarsa za ta yi ba, don kuwa shaidar ƙarya za ta bada. ***** Ɗan acaɓan baiyi tsammanin zuwan matarsa ba. don haka da ya ga ta zo, fuska a murtuƙe, sai hankalinsa ya tashi. Shin dama haka ya kumburar mata da fuska? Ko shi ne wani ya doka ba zai taba zuwa ya taimake shi ba. ya san yadda ya ke jin ya na son ramuwa akan dan sandan nan da ya tsinka ma sa mari haka ta ke ji game dashi. Ya ce a ransa, amma ai ita ta jawo. Ni ba zan zauna mace ta raina ni ba. Amma bai san miye a cikin zuciyarta ba. Da ta zo sai ta ɗaga fikafikin talotalon nan ta kwance wani zobe da ta ɗaura a ƙarƙashin fikafikin. Ɗaurin ya jima har ya yi sawu a wurin. Sai kuma ta jawo irin zoben daga cikin Jakarta ta nuna. Ta yi wannan ne daman sabida irin wannan ranar. Duk wannan rigimar da a ke yi ba wanda ya damu da daidaita adalci tsakanin mai zargi da wanda a ke zargi. daga yin iƙirarin, sai kowa ya yarda cewa dan acaban nan ɓarawo ne. amma bayan wannan matar ta nuna hujja, sai hankalin kowa ya koma kan ɗan sandan nan. Shi ma da ya ga haka sai ya ɗauki waya ya kira matarsa ya sa handsfree don kowa ya tabbata lalle an yi masa sata, koda kuwa ba wannan talotalon bane. Matar ɗan sandan na ɗaukar wayar sai tace; “Ai yanzu na ke da niyyar kiranka. Talotalon nan ya dawo. Ina tunanin dai da assuba ya fita. Fitar ka ke nan sai ga shi ya dawo gida” A nan komai ya kai ƙarshe amma a wurin ɗan acaɓa da matarsa akwai sauran husuma. da ya bata kuɗi wai ta hau adaidaita zai biyo bayan ta, tsaki kawai ta yi ta ce zuciyarta, kai da wa? Ai zama na a gidan ka ya ƙare. Ta hau napep zuwa tasha daga nan za ta koma garinsu. Ɗan acaɓan nan kuma ya laɓe a wani wuri inda ya ke hango ɗan sandan da kyau. Bayan ɗan sandan ya tashi daga aiki, ya bishi ta baya har zuwa gidansa. Ya ce, “zamu hadu wani karon” (Ƙarshe) Ni sabon hannu ne a rubutun Hausa kuma baƙo a wannan zauren. Dan Allah a taimaka a yi mini sharhi ko ɗan guntu ne. Nagode.
  October 26, 2020

 • Muhammad Abu Muhammad Mdadina DA iyalaina muna mika sakon ta'aziyy ga fulani bingel DA yan'uwan ta bisa rashin mahaifinsu. Allah gafarta mishi ya sa aljannah ce makomarshi
  Mar 29

 • Abdulwahab *ALLAH YANA DUBI GA ZUƘATA NE.* - "Kada ka taɓa yin tunanin cewa Allah yana kallon gangar jikinka ne domin yi maka hisabi akai, a'a yana yin dubi izuwa ga zuciyarka sannan sai yayi maka hisabi akai" - "Dukkanin wani aikin da ka aikata, to lallai shi Allah babu ruwansa da wannan aikin komai yawansa, shi dai zai duba zuciyarka ne yaga niyyarka da kuma ƙudrinka na zuci" - "Manzon Allah ﷺ, yace: haƙiƙa lallai Allah baya yin kallo izuwa ga gangar jikinku, ko ƙirar ku, (ko fuskokin ku), saidai kaɗai yana yin kallo ne izuwa ga zuƙatan ku" Sahih Muslim (2564) - "Lallai Allah baya yin dubi izuwa ga surar jikinku, ko dukiyoyinku, saidai kaɗai yana yin dubi ne izuwa ga zuƙatan ku da kuma aiyukan ku" barkanmu da ranaaa Abdulwahab hamisu ishaq DAMBOODEEN
  Mar 19

 • Zainab Alhamdulillah Ina Yuma kowa fatan alkhairi. Alhamdulillah alhamdulillah alhamdulillah.
  Feb 5

 • Malam Dogo Barka da yamma daga turai. Ina fata kuna lafiya. Akwai wannan virus daga ?asar Sin a ?asashen Hausawa?
  February 26, 2020

 • Umar Isah *A RAYUWA KATAIMAKI WANDA YAKE NEMAN TAIMAKO INDAI KANA DA HALIN YIN HAKAN* *BARKA DA SAFIYAR JUMA'AT MUBARAQ RAMDHAN MUBARAKH*???????????????????????????????? Labaran Safiyar Jumma'a 08/05/2020CE - 15/9/1441AH. Cikakkun labaran An samu karuwar mutane 381 masu dauke da cutar Covid-19 a Najeriya, jimilla 3,526. Gwamnatin tarayya ta ce har yanzu 'yan Najeriya na wasa da cutar Coronavirus. Hukumar INEC ta agaza wa Jihar Sokoto a yaki da cutar Covid-19 a jihar. Shugaba Buhari ya amince a sayo kayan aikin lafiya daga kasashen waje. Gwamna El-Rufa'i na jihar Kaduna ya ce Gwamnonin Arewa sun shirya hana almajiranci a jihohinsu. 'Yan bindiga sun kashe mutane 11 a kauyukan Faskari da Batsari a jihar Katsina. Coronavirus: Ministan lafiya ya ce Najeriya za ta yi amfani da magungunan gargajiya don magance cutar. Mutane 55 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan sama a Ruwanda. Iskar gas mai guba ta yi ajalin mutane da dama a Indiya. Hamshakin dan kasuwa a Rasha, Dmitriy Bosov ya kashe kansa. Bayern Munich ta nada Miroslav Klose a matsayin mataimakin koci kan kwantiragin kaka daya. *wanne labari ne yaja hankalinka/ki*?
  May 8, 2020

 • Danladi Haruna *SAKAMAKON MUHAWARA* *RANAR MAGAJI DANBATTA (19/01/2021)* *KARAWA TA 55 FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION:- MAKI= 77 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION:- MAKI =76 *KARAWA TA 56 KARAMCI WRITERS ASSC.:- MAKI= 81 MARUBUTA KARE HAKKIN AL'UMMA WRITERS ASSOCIATION:- MAKI= 80 #MuhawararBakandamiya2020
  Jan 20

 • Nura Ahmad Ina amsawa. Nima ina fatan hakan. Allah Yasa mu dace.
  October 13, 2016