Featured Create an Ad

Mambobi

 • Maryamerh Abdul Abubuwan da suke faruwa a Arewacin Najeriya abun takaici ne abun Allah wadai. Babu ranan da zaka tashi baka ji sabon abunda ya daga maka hankali ba. Wai mu yaushe Gwamnati zata dubamu ne mu talakawanta? Haba
  Jul 14

 • Hauwa Shehu " SAKACI NA..... ***GODIYA *** Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin talikai, Allah kayi dadin tsira ga shugaban mu Annabi Muhammad ( S.A.W) da ahalinsa da sahabbansa baki daya. **** GABATARWA**** "Sakaci na ... Takaitaccen labari ne da yake magana akan yadda wasu mazan kan guji kananan sana'o'i da ayyukan karfi, da yadda suke jefa Kansu da iyalan su cikin kunci kuma su dora alhakin hakan ga shugabanni, da yadda wasu masu kudin kan amfani da dukiyar su wajen cin zarafin yara 'kanana. *** TSOKACI. *** wannan labarin kirkirarre ne ba ayishi don cin zarafin wani ko wata ba. **** **** **** **** "Malam don Allah dan annabi ka taimaka kaje ka samo wani abu kar zinatu ta mutu" Sabuwa CE ta take magana cikin tashin hankali, hawaye wani nabin wani, yayin da zinatu yarinya yar kimanin shekara biyar ke kwance a kan cinyar ta tana ta murkususu gami da yunkurin amai kamar zata amayo hanjin cikinta, duk yunkurin da takeyi babu wani abu da ke fitowa daga bakin nata sai wani koren miyau mai yauki ne kawai ke iya fitowa saboda babu sauran wani abinci a cikin nata. Malam Ayuba dake tsaye bakin kofar dakin hannun shi na dama tokare akan habarshi, na hagun kuma ya dafe bangon dakin dashi. "Hhmm... ! Ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya. "Duk inda nake tunanin zan samu wani taimako sabuwa Naje ban samuba, har gidan Alhaji mato na gangare naje amma abun yaci tura, ko ganin shi ma ban samu nayi ba, sunce wai baya gari Alhalin kuma naga motarshi a kofar gidan." Cikin rashin kwarin gwuiwa malan Ayuba ke yiwa matar shi bayani. Wani kukan ta sake fashewa dashi mai sauti sannan tace " yanzu muna ji muna gani zamu bari yunwa ta kashe zinatu ? Don Allah kayi wani abu akai mana malan. "Da ina da yadda zanyi da nayi tuntuni, Sabuwa na fiki jin ciwon rashin aikin nan, to amma ya zamuyi kasar tamuce ta koma haka, taken ta ya dade da canzawa ya koma " ( Daga 'kwauri sai gwuiwa). Idan ba wani hamshakin maikudi ko mai mulki ka saniba to bazaka taba samun wani abun arziki ba, ya'yansu kawai suka sani da yan' uwansu, bayan kuma muma yan kasa ne muna da hakkin mu mori arzikin kasar tamu. Wallahi baza mu yafe musu ba akan wannan kuncin rayuwar da suka jefamu. Share hawayenta tayi, ta kalleshi cikin takaici tace " Kullum zancen naka d'aya ne, yiwa masu kudi da masu mulki Allah ya isa, bayan kai a karan kanka baka wani yunkuri na sauyawa kanka rayuwa, kana kwance a gida arzikin zaizo ya same ka? Duk Wanda fa ka ganshi da arziki to ka tambayeshi irin gwagwarmayar da yasha, har yakai matsayin da yake." "Assalamu alaikum" da sallamarsa ya shigo fuskarshi Fal da annuri. Ya na zuwa dai - dai kofar dakin yayi saurin Jefar da karamar robar o'k din da ke hannunshi mai dauke da buhu a ciki. Ya fada dakin yana tambayar "Umma meya samu zinatu? " Bashari ai ba sabon abu bane Yunwa CE kawai Ke dawainiya da ita gashi har tana kokarin haddasa mata wata cutar, kasan tun kokon jiya da safe ba abun da muka sake sawa a cikin mu sai ruwa. Sabuwa ta bawa d'an nata bashari Mai kimanin shakara sha biyu amsa tana nazarin yanayin shi. Lokaci guda bashari yasa hannunshi Cikin aljihun wandon makarantar dake jikinsa ya ciro kudi yan biyar-biyar da goma-goma dayawa ya soma hadawa, saida ya hada sannan Ya kirga, dari biyu da naira goma sha biyar cif. Ya mikawa umman tashi, cikin mamaki Ta kar'ba fuskarta da alamun tuhumar ina Ya samo su, ita dai a iya sanin ta makaranta ta aike su shida dan uwansa. "Sai kiyi maza ki lissafa masa abun da zai Siyo miki tun kafin muma mu shiga wani Hali. Muryar Malam Ayuba CE ta katse mata tunani Wanda ita ta manta ma dashi tsaye tun shigowar basharin. Sake mikawa basharin kudin tayi gami da Yi masa lissafi, tsakin masara gwangwani Uku 90 gishir 10, gawayin30, man ja 20 alayyahu 15. Hamsin din da tarage kuma ka karbowa zinatu soyayyiyar doya A wajen isa mai doya da kwai, ta samu taci kafin a gama Faten tsakin. " Haba sabuwa wacce irin doya kuma? Baki ganin cikin ya dan lafa mata, ai sai ta kara Hakuri mintin nawa ne an ruda faten, kowa sai ya shashshar'ba. Ita kuma hamsin din ba sai a ajiye taba ko koko ne a siya da safe." Ba Wanda ya ce masa komai cikin su. Bashari ya mike ya nufi hanyar fita domin yin siyayyar da aka Aike shi. "Kai..! Bani naira hamsin nan. Malam Ayuba ya umarci dan nashi fuska a tsamke. Ba musu ya ya lissafa hamsin ya bashi. " Haba malam kana ganin yadda yarinyar nan Ta galabaita bata iya ko kwakwkwaran motsi saboda yunwa, amma kace wai har sai an gama girkin da ko daurawa ba'ayiba. " Kowa da kika gani fa a wannan zamanin hakuri yake sabuwa, domin Yunwa, fatara da talauci duk sunbi sun dabaibaye al'umma, masu kudin Kuma basa son taimako, gwamnati kuma bata da niyar tallafawa talawanta Kullum sai kareraye suke yiwa Al'umma babu wani cigaba. Malan Ayuba ne ke magana alokacin da yake kokarin jawo wata kujera yar' tsugunne dake tsakar gidan ya zauna. Ya sake dai- dai ta zaman sa, yayin da ita kuma sabuwa ke kokarin kwantar da Zinatu wacce tuni baccin wahala ya dauke ta sai faman ajiyar zuciya take, a kan tabarmar da ke cikin dakin. Bayan ta kwantar da ita kai tsaye tsakar gida ta fito ta jawo kurfotin ta ( murhun gawayi) ta zazzage tokar da take ciki gami da gyara wayar kai don gawayin yayi mata auki. Neman waje tayi ta zaunan itama tana jiran dawowar bashari zuciyarta cike fal da tunani kala- kala. "Nikuwa malam nace ba, da wannan zaman da muke a haka mai zai hana ka dinga bin Bala direba kana tayashi lodin kayan lambu daga kwari kuna kaiwa kasuwar yan kaba, tunda naji ance yaron da yake binshi ya samu aikin a kamfanin robobi, kaga kafin a samu wani sai inyi maza in sanar da larai matar shi tamai magana nasan bazai kiba. A haka sai asirin mu ya rufu tunda kullum za'a sallame ka koda abun da za'a baka ba yawa ai yafi wannan yawon maular da kake yi kullum.... Tunda ta fara magana idon shi a lumshe yake ya jingina kanshi a bango baice da ita kalaba amma yanajin ta ambaci maula yayi zunbur ya bude ido gami da gyara zaman kujerar. Cikin dacin rai yace... " Wato lalacewar tawa har takai ki kirani da mai yawon maula ? Mai yasa mata kuke da saurin manta alkhairi ne ? Yanzu har kin manta lokacin da nake aiki a gidan mai menene bana wada ta ki da shi na abinci gwargwadon karfina, kuma tunda Allah yayiwa alhaji mai gidan man mu rasuwa aka saida gidan man wani irin kokari ne bana yi don ganin na samu wani aikin amma abun yaci tura, kuma... "Bance baka kokari ba amma karawa zakayi akan Wanda kake yi saboda ita rayuwar nan sai ka dage ka jajirce sannan ka hada da kuma addu'a zaka samu rufin asiri, kuma ni banga aibuba don kabi malan Bala tunda ba wani aikin karfi bane sosai nasan zaka iya." Ta katseshi ba tare da ya kammala fadin abun da yake son fadi ba. Wata uwar harara ya zuba mata gami da cewa " Baza a bishi ba din, ke a tunaninki wani abun arziki ake samu a dakon su Alayyahu da salak ? To ki daina ma tunanin haka, gobe da sassafe in Allah ya kaimu zan shirya in bi abokina da muka rasa aiki tare wajen aikin su, yace inje zai hanadi da uban gidansa ko Allah zaisa a dace. Tabe baki tayi gami da cewa "Allah yasa adace din." " Amin. ya amsa a takaice. Sannan ya mike yayi hanyar kofar gida don karta kara zunguro masa wani zancen, don ya gama fuskantarta bata gajiya da soki burutsu da sunan wai tana bashi shawara. Itama bata ce komai ba, ta bishi da ido tana mamakin hali irin na mijin nata. kwata- kwata bayason motsa jikinshi duk wani aiki indai na karfi ne bazaiyi ba, sannan ya raina duk wata karamar sa'a koda kuwa akwai rufin asiri aciki ,ya gwammace yayi tabin gidajen masu kudi ya na yawon maula da Neman gindin zama, wannan wacce irin mutuwar zuciyace da rashin sanin ciwon kai yake damu wasu mazan na wannan zamani, ita kanta a matsayinta na mace babu irin sana'ar cikin gida da bata gwada ba amma sun cinye jarin sai ma uban bashi da har yanzu larai ke binta cikon kudin waken suya da ta amsa lokacin tana sana'ar awara. Tana zaune nan bashari ya dawo da cefanen,amsa tayi ta fara kokarin hada wutar. ''Meya hanaka zuwa makaranta bashari? Kuma a ina ka samo wadannan kudin? Ta watso masa tambayoyin ba tare da ta kalli Inda yake ba. "Umma da na fita da safe na hadu da sabi'u abokina zashi talla "pure water" shine nayi tunanin in bishi ko sawu daya ne inyi don mu samu na kashe wa. Bashar yabawa mahaifiyar tashi amsa cikin ladabi. "Shi dan uwan naka fa ina ka barshi ? Kuma waya baka kudin da ka sarin fiyawatan? Ta sake jefo masa wasu tambayoyin. "Umar ya tafi makaranta, kudin kuma umman su sabi'u ce ta bani naira dari da zummar in nayi ko sawu biyu ne sai in cire ribar an kai mata darin ta, to duka kudin ma shine akayi wannan cefanen dashi. Umma ta gyada kai cikin gamsuwa don tasan mahaifiyar sabi'un sosai mutuniyar kirki ce, itama tunda mijinta ya rasu yaran suka daina zuwa makaranta suka shiga fadi tashin rayuwa don babu wani mai taimaka musu duk da kasancewar su marayu. Ana kiran sallar azahar umar ya shigo yana tangadi game da hada hanya, sharaf ya zube a kofar dakin nasu duk da cewa rana ta riski wajen amma hakan bai dame shiba saboda tsabar gajiya da kuma yunwa dake tare dashi. Daga inda take tana wanke alayyahun dazata zuba a ruden tsakin tace " yi hakuri ka tashi a rana Babana, saura kadan in karasa." Ba tare da ya amsaba yaja jikinshi a wahale zuwa cikin dakin. Da ido kawai ta bishi cikin tsananin tsausayi, ita kanta dauriya kawai take yi ballantana yaran nata da ba wasu shekaru ne dasu ba, Tabbas tasan in rayuwar su zata cigaba a haka to wata rana baza su iya jurewa ba, domin yunwa babu abun da bazata iya sa mutum ya aikataba. Jiki ba kwari ta sauke faten, tana cikin rabawa Malan Ayuba ya shigo. Bai tsaya jiran ace ga nasa ba ya dauki wanda ta gama zubawa ya ja gefe. Ido kawai ta bishi da shi domin inda sabo ta saba da wannan halin nasa. Daukar nasu tayi ita da yaran tayi dakin. Turawa su bashari nasu tayi gaban su, sannan ta ajiye nata gefe ta kalli inda zinatu ke kwance haryanzu tana bacci. "Zinatu..zinatu tashi maza kici abinci kinjin." Sabuwa ce ke kokarin tashin ya'rta ta daga bacci. A hankali zinatu ta bude ido gami da yunkurin ta shi amma ta kasa, sabo da kwata-kwata jikinta ba 'kwari. Dasauri sabuwa ta tallafota ta jingina ta da jikinta, sannan ta jawo kwanon ta fara bata a baki. Balaifi taci sosai sanna sabuwa ta bata ruwa tasha gami da gyara ta tana kokarin zaunar da ita, lokaci guda zinatu ta ri'ke cikinta tana bude baki da zummar yin magana sai amai. Cikin kankanin lokaci ta wanke jikin mahaifiyar tata da amai, hankali tashe duk suka tsaya da cin abincin suna mata sannu harda malam Ayuba da ya baro inda yake zaune ya shigo dakin don ganin abun dake faruwa. "Anya malam baza mu tafi da yarinyar nan asibiti ba kuwa? Naga jikin nata ya matsa. " ki kwantar da hankalin ki zata samu sauki basai anje wani asibiti ba, kawai tayiwa Faten cin yunwa ne, kuma bata Bari ya fad'a mataba take kokarin, kwanciya,kinga wannan ai aikin garaje ne ita kuma masara ba'a mata garaje. Malan Ayuba ya bata amsa cikin halin ko in kula. "Wallahi Baba zinatu bata da lafiya sosai , kalli yadda take wani irin abufa. Umar ne ke magana cikin sarkewar murya. Wani mugun kallo Malan Ayuba ya zabgawa umar sannan yace... "To suda uban surutu, wanene ya tambaye ka? Ko ni bana gani? Koda yake ba laifin ka bane tunda ka koshi ai sai zance harda fadi ba a tambaye ka ba. Ita dai sabuwa bata kara cewa komai ba kawai kokari take ta gyara jikinta dana Zinatu. Tana gamawa ta dauki zinatu wacce numfashinta ke fita da kyar' ta goya a bayan. Sannan ta kalli ya'yan nata maza tace "Kada kuje ko ina yanzu zan dawo bazan Dade ba insha Allah. " Allah ya dawo dake lfy . duk suka amsa a sanyaye. Ta gefanshi ta raba zata wuce ba tare da tace masa uffan ba. "Ina kuma zaki, ba tare da kin tambayi izini ba ? "Asibiti zan kaita, kuma bana bukatar sahalewar ka, domin ko ka amince ko baka amince ba dole in kaina don bazan iya jurar ganinta a wannan halin ba. Bata tsaya jin abinda zai sake cewa ba tayi ficewarta. Shi ma bai yi kokarin sake cewa komai ba, don yasan tabbas zinatu na bukatar ganin likita, kawai abunda yasa bai goyi bayan zuwa asibitin ba shine rashin kudi, ko kudin motar da zai kaisu asibitin ma babu balle a zo kan na magani. Kai tsaye gidan su sabi'u ta nufa, ta samu mahaifiyar sabi'u a tsakar gida tana kokarin tace gasarar kunun zaki da takeyi na siyarwa. " Lale maraba da sabuwa,yau kece a gidan namu? Inno ta tarbeta cikin fara'a. Mushiga daga ciki mana. Dasauri sabuwa tace "A'a nan ma ya isa, ai sauri ma nakeyi. Kinga zinatu ce bata da lfy, shine nazo ki taimakamin da rancen ko dubu daya ne zan kaita asibiti. Cikin tausayi inno ta kalle ta ita da yarinyar da ke goye a bayanta, tace " Wallahi sabuwa babu kudi a hannu na kindai san yadda rayuwar nan tayi tsanani yanzu, sai dai kawai mu neni sauki a wajen Allah. Dama ace yara sun dawo daga talla ne, to da sai a gagganda aga me za'a samu. "Babu komai inno bari mutafi nagode. Da sauri inno ta kwance gefen zanin ta, ta Ciro wata tsohuwar Dari biyu ta mikawa sabuwa. "Ki karbi wannan ko motane Ku hau, Allah ya bata. "Amin. Sabuwa ta amsa gami da sa hannu ta karbi kudin a sanyaye. Jiki ba kwari ta tunkari gidan larai dukka cewa tasan ko tana da shi ba lallai ta bata ba, don larai bata wasa da kudi. A kofar gidan ta tarradda MalamBala ya dawo daga aiki yaka kokarin yin parking din motarshi yar kur'kura. Cikin girmamawa suka gaisa, tana kokarin shigewa gidan taji yace... " Lafiya aka goya wannan amaryar tawa a baya? A hankali ta juyo tace "Wallahi bata da lafiya. "Shine kuma Baku kaita asibitiba sabuwa? Ina shi Ayuban yake? Kwallace ta cika mata ido, lokaci guda kuma ta fara gangarowa kan fustarta ba tare da Ta tsammaci zubowar tasu ba. Yanayin ta da ya ganina yasa shi fuskantar damuwar ta don dama yasan malan Ayuba bashi da wata Sana'a yanzu. "Kinga ba kuka zakiyi ba Sabuwa, zaki iya shiga wanna motar mu tafi? Da sauri ta daga masa kai alamar "Eh. Da kanshi ya bude mata gidan gaba ta shiga lokacin zinatu na ta wani irin shakuwa, shi ma cikin hanzari ya shiga motar suka nufi asibitin. Lokacin da suka iso asibitin zinatu tuni ta daina shakuwar, idon ta lumshe da alama ta samu bacci. Kallo daya Malam bala yayi mata ya kauda kai, cikin sanyin murya yace " ki hanzarta ki shiga da ita, ni zan jira anan idan ana bukatar wani abu sai kiyi min magana. " Toh. Ta amsa gami da wuce, wa wasu ma'aikatan jinya biyu taga sun fito daga wani daki da sauri ta tunkare su tana kokarin yi musu bayani. Daya daga cikin nurses din ta sa hannu ta karbi zinatu. Tsam nurse din ta tsaya tana kallon ta, ita kanta sabuwa saida gabanta ya fadi ganin yadda komai na jikin zinatu ya saki. " Biyoni ciki. Nurse din ta umarci sabuwa yayin da take kokarin shiga wani daki. Ba musu ta bita har bakin wani gado da ake kwanta da marasa lfy, a kai taga an kwarta da zinatu. "Ki zauna nan kusa da ita Ki jirani ina zuwa. Minti kadan da fitar nurse din sai gata sun dawo ita da wani likita yana gaba tana biye masa a baya. " dan jiramu a waje. Yaba sabuwa umarni. Bai tsaya wani bata lokaci ba kan zinatu ya nufa, hannun shi yakai dai -dai saitin hancinta , sannan ya dan bude mata idonta guda daya lokaci guda kuma ya sa mata wani abu a kirjinta sannan ya kara kunnen sa kunne sa. Duk abun da akeyi sabuwa na kallonsu ta window, haka kurum taji zuciyarta ta mata nauyi kamar wacce aka daura wa wani katon dutse, kwata - kwata ta rasa meke damunta. Nurse ce ta leko tayi mata alamar tazo da hannu. Tana shiga dakin likitan yace "Hajiya sai dai muyi hakuri, Allah ne ya baki ita kuma yayi ikon sa Akanta. Yana kaiwa nan ya fice daga dakin. A hankali ta karasa gaban gadon da zinatu ke kwance ta dauke ta ta goyata. Kwata- kwata ta nemi kuka ta rasa, sai wani suya da radadi da zuciyarta keyi. Tabbas ta san cewa mutuwa dole ce kuma kowa zaman jiranta yake yi, amma duk da haka gani take zinatu ta rasune sakamakon SAKACi irin nasu, a matsayin su na iyayenta sun kasa bata kulawar da ta dace, sun kasa sauke hakkin ta da Allah ya daura musu. Kaico da wannan rayuwa. " Sabuwa lfy? Ya jikin nata? Muryar malam Bala ce ta katse mata tunanin da takeyi, sai alokacin ma ta fuskanci har takai bakin gate inda yake tsaye yana jiranta. " Allah ya karbi Abarsa. Abun da ta iya cewa kenan. "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un. Shi malam bala yayi ta maimaitawa har suka shiga motar. A kofar gida suka taradda Malan Ayuba ya dawo daga sallar la'asar yana kokarin shiga gida. Yana hango sabuwa a motor Malam Bala yayi saurin shigewa cikin gidan yana mita. " Mata sai taurin kan tsiya, na gaya mata bazan yi wannan aikin ba shine har da wani zuwa ta jaji'boshi, to sai mu gani ai in ana dole. Umar da Bashari ne dake tsakar gidan suka bishi da kallo don basu san musabbabin fadan nashi ba. Ko kallon inda yake batayi ba ta nemi kan tabarma ta kwantar da zinatu. Da sauri ya'yan nata suka yo kanta "umma ya jikin nata ? Ta samu sauki ko? Duk suka jero mata tambayar a tare. Sai dai muyi mata addu'a zinatu ta fita daga cikin wanna kuntatacciyar rayuwa, Allah yaji kanki zinatu. Ta fada alokacin wasu hawaye masu dumi suka gangaro fuskarta. Kuka mai tsanani yaran keyi musamman Bashari kasan cewar yafi umar wayo, ganin yadda suke kuka ya dad'a k'aryar mata da zuciya ta rungume su suka ci gaba da wani irin kuka mai tsuma zuciya. Malam Ayuba yana tsaye ya rasa bakin lallashi, shi kanshi hawaye yake yi, tabbas mutuwar ta buge shi, ko da wasa bai taba kawowa zinatu mutuwa, ashe ba mai tsahon rai bace. Nan da nan makota suka shirshigo kasan cewa Malan Bala ya Sanar musu. Ba'a dauki wani lokaci ba akayi mata sutura aka kaita ma kwancinta. Bayan anyi sadakar bakwai. Da sassafe ya shirya ya fito yana gyara hula lokacin sabuwa na share tsakar gida. " Mun tafi sai Allah ya dawo damu. " Ina kuma zaka je Malan? Au na manta ban gaya miki ba munyi magana da Malan Bala akan shawarar da kika bani, na amince zan dunga binshi, kinga yau zamu fara fita. Har cikin ranta taji dadin hakan don haka da farar'ar ta race " Madallah, Allah ya bada sa'a ya kawo rabo mai amfani. "Amin. Sannan yasa kai ya fita. Cikin kwana biyun nan da Ayuba ke fita babu laifi rayuwar su ta dan canza, kullum basa rasa abun da zasu ci , Bashari ya ci gaba da zuwa makaranta kasancewar shi dan JSS 1 umar kuma Primary 5. Yau har Karfe takwas na safe taga yana kwance bashi da niyar tashi, tasan kuma in dai zasu fita aiki baya kaiwa karfe bakwai ma balle takwas. " Malam ni kuwa yau lfy naga Baka shirin fita? "Lafiya lau. Ya bata amsa ba tare da ya kalli inda take ba. " Allah yasa dai ba wani abune ya shiga tsakaninka da Malam Balan ba. "Babu abun da ya shiga tsakanina da shi kawai na gaji da wannan wahalar ne, kina gani fa Dari uku Dari hudu ake bani kullum randa yaga dama ne zai ban Dari biyar. Ko ta yaya mutum zaiyi arziki da yan wannan kudin da basu isa cin abinci ba ma." Galala....Ta saki baki tana kallon shi, ta ma rasa mai za ta CE masa don tsabar takaici. "Uhmmm bari kiga in tashi in nufi wajen abokin nan nawa da yayi min alkawarin hadani da uban gidan sa. Lokaci guda ya mike ya zari buta ya soma kwaskwarima. Kai tsaye gidan lawal ya nufa, lokacin tara da rabi har ta wuce. Ya taki sa'a don kuwa ya sameshi yana shirin fita. Hannu ya mika masa sukayi musabaha. Kana Ayuba yace " Mutumi na ka samu duniya irin wannan buga shadda haka ? Kai da gani kasan naira ta zauna. Hahahha.... Dariya lawal ya bushe da ita gami da dukan kafadar Ayuba. "Har yanzu kananan da abun dariyar ka Ayuba, ina wata naira ta zauna anan? Ana dai malejin rayuwa kawai. Da sauri Ayuba yace shiyasa ni ma nazo ka dan jonani a inda kake malejin ko nima na samu rayuwata ta canza. Lawal ne ya danyi Jim yana nazarin wani abu," karka damu duk aikin da ka sani wlh zanyi indai ba faskare bane ko dako. Malam Ayuba ne ya katse masa tunani. To ai yanzu matsalar shine, ogan nawa da nace zan hadaka dashi bana tunanin yanzu yana bukatar ma'aikata masu yawan shekaru irin naka, shiyasa kaga na danyi shiru ina nazarin abinyi. Cikin mamaki malam Ayuba yace Yanzu har nayi tsufan da bazan moru ba? Murmushi Lawal yayi sannan yace ba ina nufin ka tsufa bane, sai dai nasan halin Alhajine sarai, ba lallai yayi na'am da kai ba. Amma bari in kirashi in sanar dashi idan ya aminci yanzu sai mu tafi dakai dama can nayi nima. Waya ya zaro daga Aljihun shi ya lalubo Nambar Alhaji bugu daya tashiga saidai kiran yayi kamar zai tsinke sannan aka dauka. "Ya akayi najika shiru har yanzu ? Daga bangaren Alhaji. " Ranka ya dade yanzu nake shirin tahowa. "Kayan sun samu? Alhaji ya kara tambaya. A'a wadan da mukayi order sai zuwa yamma zasu iso, yanzu haka ina tare da wani tsohon abokina yana neman aiki shine nace bari in tuntubeka, in ka amince sai muzo dashi ka ganshi kayi masa interview. Lawal ya ba Alhaji Amsa. "Kai ma kasan ban cika son harka da manya ba amma babu damuwa zaka iya zuwa dashi in har ka tabbatar zai iya. Da sauri Ayuba ya daga kai alamar zai iya, dake wayar a handsfree take yana jin duk tattaunawar da suke yi. Kai tsaye cikin motar da Ayuba ya gani a kofar gidan suka shiga,Civic ce karama mai ruwan toka. A cikin motar Ayuba ke ta faman mamakin yadda Lawal ya samu ci gaba a rayuwarshi. "Wannan ba komai bane matukar zakayiwa Alhaji abinda yake so cikin kankanin lokaci kaima zaka mallaki duk wannan.cewar Lawal, haka suka ci gaba da tafiya har suka iso wata Unguwa, shi dai Ayuba bai san ko ina bane, amma yanayin gidajen Alfarma dake yankin ya nuna cewa unguwar ta masu hannu da shuni ce. Wani makeken gida suka nufa, Lawal yayi horn da sauri mai gadi ya bude kofar don ya san Lawal din kuma yana daga cikin manyan yaran ubangidan nasa. tunda suka shiga gidan yake da kalle- kalle, shi a isa tsahon rayuwarsa bai taba shiga gida na alfarma irin wannan ba, ji yake inama shine mamallakin wannan gidan da ya gama morewa a duniya, koda suka shiga falon ma dad'a susucewa yayi,tuni ya yankewa kanshi shawarar koma wani irin aiki aka sashi a gidan nan dole yayi don shima ya dangwali arziki. Wata matattakala da zata sadasu da babban falon sama yaga lawal yabi don haka bai tsaya wata- wata ba shima ya mara masa baya. Ido ya fara saukewa kan wani kakkauran mutum kwance akan duguwar kujera daga shi sai singlet da boxer, idon shi a lumshi da alama yana jin dadin yanayin, wani matashi ne zaune a gefen kujerar yana mammatsamasa kafa. "Barka da hutawa Alhaji. Lawal ya gaida Mutumin cikin rissinawa. " Yauwa ya amsa a takaice gami da daga wa matashin da ke kusa da shi hannu alamar ya dakata da abun da yakeyi, ya dai-dai ta zamanshi sannan ya kalli inda Ayuba yake. Kallo daya yayi masa ya kauda dakai, shi kuma Ayuba gani haka ya sashi saurin durkusawa har kasa domin ya kwashi gaisuwa. Ba tare da Alhaji ya amsa ba ya cewa Lawal " Kai da nake sa ran gani yara danyu sharaf yan sha biyar sha shida masu jini a jika shine zaka kawo min wannan gwala-gwajin. Da hanzari Ayuba yace "Yallabai dan sha biyu zaiyi? Ina da yaro mai kwazo na tabbata aikin da dan sha biyar zai yi bashari zai iya. Alhaji ne ya tattaro da hankalinshi gareshi, iya kallon da yayi masa ya fuskanci Ayuba mutum ne kyakykyawa bashi da munin halitta kwata kwata, babu ce kawai ta kodar dashi, yabi ya jejjeme haka, tabbas idan za'a samu dan nashi harkar zatayi kyau. Murmushi yayi ya kalli lawal "Ka masa bayanin irin aikin da nake bukata? " A'a nazo da shi ne tukunna inji yadda zakuyi, idan yayi maka sai ayi masa bayani. Yanzu tunda yaron sa zai kawo ya kamata ya san irin aikin da dansa zaiyi. Ya juya da kallon shi ga Ayuba Wanda ya riga ya gama bazan kunne don jin irin aikin. " Ba wani aiki ne mai wahala ba, duk lokacin da Alhaji ke gari yana bukatar masu debe masa kewa, da kuma kokarin sauke masa gajiyarsa, kamar yadda ka shigo ka taradda wannan matashin nayi. Lawal ya koro masa jawabi. Bakaramin daure masa kai abun yayi ba, debe kewa, sauke gajiya wannan wani irin surkulle ne, shidai ya san namiji yace zai kawo ba mace ba ballantana yayi tunanin ko Alhaji na son hutawa da itane, hankalinshi ne yakai kan matashi da ya shigo ya tarar yana yiwa Alhajin tausa, nan da nan tunanin shi ya hasaso masa abun da suke nufi. "Wato dai in na fahimta za'a dinga yiwa Alhaji tausa ne duk lokacin da yake gari. Cewar Ayuba. "Yauwa dan gari aikin kenan. Lawal ya fada yana dariya. Lokacin ne kuma Alhaji ya jefowa Ayuba bandir din kudi yan Dari biyar -biyar sababbi fil kan cinyar shi, "idan ka yanke shawara ka sanar da shi Alhaji ya fada yayin da ya mike yana kokarin shigewa wani daki. "Ai bawata shawara Alhaji, na amince kawai, wannan ai ba abun da za'aki ba ne, na amince wlh, yaushe zai fara zuwa aikin? Ayuba ya fada yana ta faman jujjuya kudin a hannunsa. Wani murmushi Alhaji ya saki gami da cewa zuwa yamma za'a iya kawo shi, kai kuma Lawal idan ka dawo da yamman zamu hadu. Bai jira jin wani abu daga gare suba ya shige dakin. Acikin mota Ayuba ya kalli Lawal yace " Allah yasa dai ba kudin kan d'ana na amsa ba, don gaskiya a tsorace nake, irin wannan kudi haka kuma ba wani aikin kirki ba. "Kar ka damu mutumina ba abin da kake tunani bane, kuma dubun su na nan tafe in har danka yayi biyayya. Tana zaune ta zabga uban tagumi tana ta faman sake-sake, kamar daga sama taga ya shigo da buhun shinkafa sannan ya koma ya dawo da jarkar mai karama da katan din taliya, wata leda mai sanda-sanda ya mika mata. Kar'ba tayi tana binshi da kallon mamakin daga ina kayan suka fito. Malam duk wadan nan kaya daga ina haka? Waya bamu zakka? Hohoho...! Sabuwa meyasa kike haka ? Mutum bai kawo ba kice bai kawo ba, ya kawo kuma mai makwacin Ki karba da godiya a'a kin tsaya tuhuma da bin ba'asi. "To ai gani nayi baka da karfin da zaka iya wannan siyayyar shiyasa na tambaya. "Kuma shikenan Allah bazai kawomin budi ba. Allah ya baka hakuri ta fada jiki ba kwari. Har ya kama hanya zai fita ya juyo yace "yauwa ina yaran nan ? Basu dawo daga makaranta ba tukunna. "Idan sun dawo zuwa banya la'asar Ki sa bashari ya shirya, kayan sallar shi na bara nake son ya saka zamuje wani waje dashi. " To ta amsa yayin da take zazzage ledar da ya miko mata, kayan miya ne harda kaza a ciki.lallai yau duniya ta samu nan da nan ta shiga sarrafawa. Kowa a gidan malam Ayuba yasan yau canji ya samu don sunci kun koshi harda naman kaza wadan baxa su ma iya tuna rabonsu da cin kaza ba. La'asar sakaliya Lawal yazo har gidan malam Ayuba ya tafi da Bashari. Kwarai dagaske Alhaji ya yaba da yaron, tunda ya ganshi ya kwadaitu da shi. "Matsonan mana abokina. Alhaji ya umarci Bashari daya dan matso kusa dashi. A dan tsorace Bashari ya karasa kusa da Alhaji. "Ka saki jikin ka, babu abun da zai faru kaji ko? Cewar lawal. Gyada kai Bashari yayi alamar gamsuwa. "Ina ganin ya kamata ka fara nuna masa abun da ya dace, da yadda ya kamata yayi kasancewarshi yaro karami kuma sabon hannu. Alhaji ne ke magana, yayin da ya kishingida akan kujera. Lawal da kanshi ya tashi ya zagaya ta bayan Alhaji, ya daura hannuwanshi a kan kafadunshi ya yana mammatsawa, haka ya dinga yi yana mammatsawa Alhaji sassan jikinshi a hankali. Shi kuma Alhajin sai faman wani lumlumshe ido yake yi. Shidai Bashari ya na zaune awajen yana kallon su, mamaki duk ya cikashi kuma ya gaza fahimtar ainahin abun da suke aika tawa. Muryar lawal ya tsinkayo yana umartarshi da ya matso kusa. Ba musu ya karasa daf dasu. Lawal ne ya dinga nuna masa yadda zaiwa Alhaji tausa, sun dan dauki tsahon lokaci suna cikin yanayin sannan daga bisani Alhaji ya umarci Lawal da su shiga cikin daki. "Ka jira mu anan yanzu zan fito mu tafi. Cewar lawal daga kai kawai Bashari yayi don shi dama ya k'osa da su tafi. Ba haka Alhaji yaso ba, amma dole yayi hakuri na dan wani lokaci saboda bai kamata ayiwa yaron garaje ba. Basu wani dade ba ya fito suka tafi, a hanya ne Lawal ya dinga karfafawa Bashari gwuiwa Akan ya saki jikinshi, kafin ya kaishi gida sai da suka biya yasai masa ice cream da dambum nama. A kofar gidan Malam Ayuba ya taresu dama tuntuni su yake jira.Bayan sunyi sallama da malam Lawal ya kama kunne Bashari yace " kar inji ko dawasa ka sanar da mahaifiyarka irin aikin da zaka rinka yiwa Alhaji, duk randa ka bude baki ka gaya mata kuwa ka tabbatar zamu koma gidan jiya, yunwa ce zata kashe mu kamar yadda ta kashe zinatu, daga nan kuma tarihin mu zai shafe a duniyar nan, su kuma masu kudi su ci gaba da jin dadinsu. Cikin sanyi jiki Bashari yace "Bazan fada ba Baba. Ko a cikin gida da Sabuwa ta tambayi Bashari irin aikin da mahaifinshi ya Samar masa sai yace aikin bawa fulawa ruwa da yanke ciyayi ne a gidan wani Alhaji. Ya fadi hakane bisa umarnin mahaifinshi. " Ni a ganina Malam wannan aikin yafi dacewa dakai ba Bashari ba, kaga Bashari yaro ne karami, kamata yayi mu maida hankali wajen ilimin shi bawai mu kaishi aikatau gidan masu kudi ba. " Kai....! Sabuwa kin cika korafi wallahi, sau nawa zan fada miki sunce basason Wanda ya manyanta, sai masu kananan shekaru, ko so kike yi muyi asarar wannan damar? " Ai... "Ai me? Kinga ni zancen ya ishe ni haka. Ya katseta ba tare da ta fadi abin da take son fada ba, dole tayi shiru badon ranta ya so ba. Tsahon kwanakin nan kullum sai an kai Bashari gidan Alhaji an masa training, kuma duk randa yaje sai ya dawo da abun arziki, Malam Ayuba ke tare shi a kofar gida ya amshe yan kudaden, ya barshi da kayan ciye- ciyen. Yau Asabar ba makaranta boko don haka Alhaji ya umarci da akawo bashari da wuri. Yau ba kamar kullum ba akan gado suka taradda Alhaji ya mimmike daga shi sai gajeran wando yana jiran zuwansu, " Cire kayanka ka hau gadon. Lawal ya umarci Bashari. Ido ya zaro lokaci guda kuma tsoro ya bayyana a fuskarsa, jikin shi na rawa ya soma ja da baya. "Kada kaji tsoro babu wani abu aciki, Baka ganin duk mazane yan uwanka, babu banbanci a tsakanin mu ai. Lawal ya fada yana murmushi gami da kokarin jawoshi jikinnshi. Da sauri bashari ya sake ja baya yana girgiza kai " gas...kiya ni kunya nake ji ya fada murya na rawa. Sai lokacin Alhaji ya yi murmushi yace " karkaji kunya, mu iyayayenka ne kaji, ya fada yana shafa al'aurarshi. "Girgiza kai yayi alamun bai amince ba, ran Alhaji ne ya soma baci, yace da Lawal bafa zanyi asarar kudin da na kashe akan yaron nan ba, don gobe nake sa ran yin tafiya, ya kamata kasan abiyi. Cikin zafin nama Lawal ya cafko bashari, ya soma rabashi da kayan jikin shi, bashari nata kokarin turjewa, saukar wani wawan mari yaji a kuncinsa, hakan ya sashi nutsuwa ba tare da ya shirya ba, sai da ya raba shi da kayan jikinshi tsaf sannan ya jefashi kan gadon. Nan da nan Alhaji ya kankame shi yana ta shashshafashi, shi kuma yaron kuka yake sosai yana neman taimako. Kan mudubi Lawal ya nufa ya dauko Vaseline ya mikawa Alhaji sannan ya fita daga dakin gami da cewa zanje in dawo. Da karfin Alhaji ya kifa Bashari zuwa rufda ciki, yasa hannu daya ya danne hannayen shi, dayan kuma ya soma shafa masa Vaseline a duburarshi, yana kokarin danna al'aurarshi ciki amma ya gagara shiga, ganin yana kokarin jiwa yaron ciwone yasa shi tunanin dauko lubricant ya kara koya samu ta shiga cikin sauki. Tashi yayi na nufi jikin wardrobe din dake manne a bangon daki ya soma duba lubricants din, anankali Bashari ya kai hannunsa kan wata dim light dake gefen gadon, Alhaji na juyowa da zummar hawowa kan gadon cikin zafin nama Bashari ya kwala masa dim light din a gabansa, da sauri ya saki kwalin lubricants din ya dafe wajen gami da sakin wata yar' kara. Ganin haka yasa Bashari tashi cikin hanzari ya kwashi kayanshi ya fita a guje. Ya ci sa'a kuwa ba kowa a falon, ko a bakin gate ma mai gadi bai hanashi fita ba don ya dade da zargin ubangidan nashi cikin mummunar harka duba da yadda ake yawan kawo masa yara matasa. Gudu sosai yayi kafin ya dangana da babban titi, haka ya dinga tafiya ba tare da sanin inda ya dosa ba, tafiya ta kusan kimanin awa guda yayi sannan ya gane inda yake, waje ya nema ya zauna yana ta maida numfashi. Yana zaune nan ya hangin wani mai tallan pure water ya roke shi da ya bashi daya yasha. Bayan yasha ne ya mike a kasale ya nufi unguwarsu, duk da yasan da nisa amma ba shi da zabi dole ya miki hanya. Kamar an wurgo shi ya shigo gidan wujiga wujiga ,Malam Ayuba na zaune a gidin makwarara yana alwala, ita kuma sabuwa fitowarta kenan bandaki, bata san lokacin da ta yar da butar dake hannunta ta nufo Bashari tana tambayarshi meya sameshi. Fadawa yayi jikinta ya fashe da kuka. "Don ubanka bazaka yi Magana ba, kanaji ana tambayarka kayi shiru. Malam Ayuba ya taso kamar zai dake shi. Muryarshi na rawa cikin kuka ya soma labarta musu abun da yafaru, jiki na rawa sabuwa ta jawoshi ta cire masa wando ta fara dudduba shi, sai da ta tabbatas ba wani gagarimin abu da ya faru sannan ta jashi zuwa daki. Malam Ayuba tsaye yayi tsit kamar ruwa ya cinye shi ya rasa abinyi,bai taba tunanin al'amarin su lawal ya kai ga Neman maza ba, in banda sharrin zamani da sharrin shaidan me namiji zai ji a jikin dan uwanshi namiji,musamman ma karamin yaro kamar Bashari da bai ma balaga ba ballantana yasan wani jin dadi. Tabbas yayi nadamar aminta dasu, kuma ya san kwadayi da mutuwar zuciya ce ta jawo masa, da bai sakawa kanshi dogon buriba ya jajirce yayi ri'ko da karamar sana'arshi tabbas da bai jefa ilayanshi a wannan halin ba. Fitowa tayi hannun ta rike da na ya'yanta Umar kuma rike da jakar ka yansu. Da sauri ya sha gabansu. " Sabuwa don Allah Ki saurare ni, wlh ban yi tunanin haka zata faruwa. " Bazan iya zama da mutum mara zuciya Mara imani irinka ba Ayuba, tunda har zaka iya daukar danka na cikin ka ka kai ayi luwadi dashi don ka samu kudi to ina ganin tarayyata dakai ta 'kare, don na san wata rana nima zaka iya kaini ayi zina dani don ka samu kudi. " Wa' iyazubillahi, subhanallahi, wlh wannan ma kuskure ne da SAKACI NA amma bawai da niya na kaishi ba, sabuwa na roke Ki da Allah Ki yafe min Wlh nayi nadama. " Nadamarka ta banza, tunda bazaka iya ciyar da iyalinka da guminka na halas ba. Kaga ni ban guri in wuce kauyen mu zan tafi na gaji da wannan rayuwar. "Wallahi ko dako ne zanyi, ke ko faskare ne zanyi wallahi, don Allah Ki zauna karki tafi kece rufin asiri na ya fada hawaye na zuba daga idonshi. Da sauri taja hannun yaranta zasu wuce, umar ne ya rike mata hannu yace " Umma baba yace kiyi hakuri bazai sake ba, ba kiga yana kuka ba don Allah kar mu tafi mu barshi. Tsayawa tayi cikin sanyin jiki, " umar mahaifinku baya sonku, baya kishin ku kwata- kwata, zama tare dashi bazai amfane mu da komai ba gara mu tafi kawai. "Sabuwa na tuba wlh don Allah karki tafi, ya juya ga yaran, Bashari ka yafemin don Allah Ku zauna tare dani. ita kanta ba son tafiyar take yiba don ko taje kauyen wata wahalarce kasancewarta marainiya. Haka ya rinka lallashinta da yi mata alk'awarin zai canza rayuwarshi har ya samu ta hakura. Ko takan su lawal bai bi ba, sums kuma basu naimeshi ba. Da kanshi yaje ya samu malam Bala ya roke shi akan zai ci gaba da binshi. Cikin kankanin lokaci Ayuba ya canza tsarin rayuwar shi da kanshi, ya daina bin gidajen masu kudi ya daina zaman jiran gwamnati ta kawo masa sauyi. idan sun dawo daga kasuwa shi da Malam Bala da yamma ya Fita suyar kifi a bakin gada, dama ita ce tsohuwar sana'ar shi. Allah kuma ya sanyawa Sana'ar Albarka yanzu ba abin da yake gagarar su, yaransa kuma suna zuwa makaranta. Bayan wani lokaci Ayuba na zaune a wajen sana'ar shi, Lawal ya zo tabbas badan ya dade da sanin lawal ba to da bazai gane shi ba saboda yadda ya rame. Anan ya roki Ayuba gafara, kuma yake shaida masa cewa ya dade da da dena harkar luwadi yanzu bashi da wani abinyi, abincin da zai cima gagarar shi yake yi, Alhaji ma yanzu ya na can bashi da lfy, tsutsace kawai ke fita ta duburarshi. Sosai Ayuba ya jinjina al'amarin, yace dama ai SAKACIN mu ne da watsi da kananan sana'o'i kan jefa mu ga Halaka. Alhamdulilah. Ubangiji Allah ya sa mu fadaka da wannan takaitaccen labarin, Allah kuma ya yafe mana kura-kuran mu. Amin. Hauwa Shehu. 31/10/2019
  October 31, 2019

 • Aishatu ibrahim Oriflame kamfani ne daga kasar Sweden. Office dinsu a Nigeria yana garin Lagos. In kikayi register da su zaki sayi kaya akan farashin sari direct daga company su kawo miki har gida kuma. In kika fara kasuwanci da kamfanin Oriflame zaki rika samun kudi ta hanya 4. 1👉ta hanyar ribar da zaki rika samu in kika sayar sa kayanki 2👉ta hanyar biyanki albashi duk wata bayan an kirga yawan points din sayayyar/cinikin da kike yi. 3👉ta hanyar yi ma wasu register a karkashinki. Za a kirga points din sayayyar da sukeyi a hada miki da naki points din sayayyar da kikeyi a rika biyanki duk wata. 4👉 ta hanyar samun kyautar kudi a hannu (cash award) in kin samu sabon matsayi daga director zuwa president. Kyautar tana farawa daga dubu 250k zuwa million 150, ya danganta da kokarinki wurin yin sayayya da kuma samo wasu suyi register a karkashinki. Tuntubeni ta wannan hanyar don jin karin bayanin yadda akeyi. 07032698888 WhatsApp........... Name Address Email (active) State Phone Date of birth 🏄🏻‍♀🏄🏻‍♀🏄🏻‍♀🏄🏻‍♀🏄🏻‍♀🏄🏻‍♀ karku bari a baku lbr sai naji ku🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Oriflame look great have fun make a lot of money💵💵💵💃🏻💃🏻💃🏻🤸🏻‍♀
  Jul 6

 • hibbatou ali Salamu alaikum, mata iyayen gida, Suna na Hibbatou ali ... ko kin san cewa yin sana’a da samun kudin shiga alkhairi ne a gare ki? Idan kina matar aure ko dalibar makaranta ina baki shawara da ki kama sana’a ko mi kankantar sa, ni dai sana’a ta Oriflame ce kuma Alhamdulillah, ina samun rufin asiri. Don haka idan kin dade kina tunanin sana’ar da zakiyi, ki tuntube ni a whatsapp ta wannan number, +22790954662 zan koya maki irin business dina sannan in ci gaba da rike hannun ki har sai kin fahimci komai ta yadda zaki iya yin komai da kan ki...amma fa ba na masu kiwuya bane, na mata ne masu kokari da jajircewa. Ga number ta zan maimaita +22790954662
  Jul 20

 • Rukayya Ibrahim Lawal Har kullum idan kana so ka ci nasara a rayuwa , kafara wanke zuciyarka kafin jikinka ka wanke harshenka kafin hannunka ka kyautata zato ga mutane. A kullum a rayuwa ka kasance mai kyakkyawar zuciya da iklasi, kada ka bayyanawa duniya aibun wani don mayar da kanka tsarkakakke, kada ka Kushe wani don samun yabo kada ka sayi farin jini ta hanyar daurawa wani bakin jini. Barkanmu da wadannan lukuta masu albarka ayawaita yiwa annabi s a w, salati ,,,daga shareef kabiru sidi fari
  Jul 25