Mambobi

  • pheedy Esmaa'eel Welkam to bakandamiya my buhda
    June 18, 2020

  • Rahma kabir *SO SARTSE* © *Rahma Kabir Mrs MG* *Wattpad😗@rahmakabir *_Page 13._* Bukar ko da yaji labarin haihuwar Kaltume bai zo ba, sai ya kuma dulmiya cikin Maiduguri ya cigaba da rayuwar da ya ɗaukarwa kansa. Tun abin yana damun Mamman harya zo ya yakice shi a ransa ya cigaba da rayuwarsa tamkar bai da wani ɗan uwa a duniya. Kaltume na gama wankar arbain ƙanwar Kaala ta tafi gida, suka cigaba da rayuwar su gwanin sha'awa. Ɓangaren Alh. Zanna, asalinsa ya fito daga yankin ƙauyen Marte, kanuri ne ciki da bai, yana da mata Falmata da yaronsu guda Hafiz wanda yake da shekara huɗu a duniya, Zanna ya kasance manomi yana shuka kayan lanbu, a wani lokaci Allah ya jeho masa iftila'i gonarsa ya ƙone gaba ɗaya bai cire komai ba, tun daga lokacin ya shiga halin talauci sosai, hakan yasa wata rana ya shirya ya bar ƙauyensu ya shigo cikin birnin Maiduguri domin ya samawa kansa wani sana'a. Zuwansa da kwana uku ya samu aiki a gurin wanke motoci, da kyar suka ɗauke shi sai da ya haɗa da roko da magiya kafin suka amince. A washe gari ne Mamman ya kai motarsa gurin dan a wanke masa, aka yi sa'a Zanna shi ne ya wanke motar, Mamman ya kalleta shi cikin kulawa. "Ɗan uwa amma dai yau ne ka fara aiki a nan ko?" "Eh jiya na fara aiki" "Allah sarki, hala kai baƙo ne?" "Eh baƙo ne ni daga yankin Marte" "Amma meya baka sha'awa a wannan aikin? baka gudun sanyi ya kamaka saboda yawan amfani da ruwa" Idon Zanna ya kawo kwalla ya duba Mamman da kyau, kwata-kwata ba zai wuce sa'ansa ba, sai dai kuma daga ganin Mamman yana cikin rufin asirin Allah, saɓanin shi da an ganshi za a hango tsantsar talauci da ya yi masa katutu. "Kayi shuru" Cewar Mamman ya katse masa tunaninsa, Zanna ya nisa ya ce. "To na dai fara da wannan ɗin, kafin in samu wani aikin" "Kana da iyali?" "Eh ina da suka na baro su a kauye, yanzu a masallaci nake kwana kafin na samu matsuguni" "Allah sarki" Mamman ya ce sai ya ciro kuɗi ya miƙa masa. "Gobe in Allah ya kaimu da safe ka hau abin hawa ka ce ya kai ka Mamman Plaza, in ya sauke ka sai ka ce kana so a nuna naka office ɗin Mamman, za a kawo ka gurina sai mu yi magana" Cike da murna Zanna ya amsa kuɗin yana masa Nagode da Addu'a. Mamman ya yi murmushi ya shiga mota ya wuce gida. Washe gari kamar yadda suka yi magana haka Zanna ya tafi wurin Mamman, ya samu kyakkyawar tarba a gunsa, dan kafin su fara magana da Mamman, sai da ya sanya aka kawo masa abin karin kumallo ya ci ya ƙoshi kana Mamman ya yi masa bayani. "Sunana Mamman Bakura, wannan wurin mallakina ne, in ba damuwa zan ɗauke ka aiki a matsayin driver in ka iya tuƙi, sannan zaka riƙa zama a nan ofice ɗina kana taya ni wasu ayyuka da kuma kula da customers. Sannan kuma zan baka masauki a gidana, nan da mako guda ka je garinku ka ɗauka iyalinka" Nan take Zanna ya fashe da kukan murna ya rasa dame zai godewa Mamman, sai da ya yi mai isarsa kana ya sassauta kukansa ya shiga jero masa Addu'a da godiya. Mamman ya nuna masa babu komai, haka nan yaji ya taimaka masa saboda Allah, shi dai burinsa ya riƙe masa amana. A wannan rana haka suka yini a nan plaza, zuwa yamma Mamman ya ɗauki Zanna ya wuce da shi gurin wanke mota ya ɗauki kayansa ya yiwa masu gurin sallama, suka wuce gidan Mamman ya ba shi masauki a BQ. Wannan shi ne farkon haɗuwar Mamman da Zanna, a hankali suka shaƙu sosai, bayan mako guda Zanna yaje Marte ya ɗauko iylinsa, Falmata ba ƙaramin Murna ta yi ba suka yi sallama da dangi suka taho. Falmata ta shaƙu Kaltume kullun tana ɓangarenta tana taya ta aiki da renon Beena, cikin watanni shida sun shaƙu sosai kamar ƴan uwa. A wannan lokacin Zanna yasan wasu sirrika na Mamman saboda baya ɓoye masa komai dan ya ɗauke shi tamkar ɗan uwansa na jini, hatta labarin Bukar ya sani wanda a lokacin zuwansa biyu kuma duk suna haɗuwa, in ya zo bai wuce ya karɓi kuɗi wurin Mamman ya ƙara gaba, duk kansu sai dai su bi shi da addu'an shiriya. Mamman shi ne ya sanya Hafiz a makarantar boko da islamiya, yana jin yaron kamar ɗan cikinsa saboda tsantsar amanar da Zanna ya riƙe masa, yana jinsu tamkar ahali guda suka fito. Lokacin aikin hajji ta ya zo, haka Mamman ya biyawa kansa da Kaltume, a wurin Zanna ya bar duk kadarorinsa ya ba shi yaja ragamar kasuwancinsa har ya dawo saboda ya yaba da riƙon amanarsa, sannan Kaltume ta barwa Falmata riƙon Mubeena, lokacin tafiya ya yi, gaba ɗaya suka shiga mota suka tafi filin jirgi, haka suka yi ban kwana suna kuka kamar karsu rabu, bayan sun shiga jirgi ne su Zanna suka dawo gida. Tunda Bukar ya ji labarin tafiyar Yayansa Mamman Makka, sai ya shiga zuwa gidansa akai-akai, yana yiwa su Zanna iskanci kala-kala kuma sai ya ce dole sai ya ba shi kuɗi, haka dai Zanna yake haƙuri da shi kamar yadda yaga Mamman yana yi, sai ya ɗauki kuɗin ya ba shi dan a zauna lafiya, har Allah ya dawo dasu Mamman. Su Kaltume sun yi aiki hajji lafiya sun dawo gida cikin aminci, suka raba tsaraba ga mutane, kusan yawan tsarabansu daga na Mubeena sai na Hafiz, Kaltume kuwa duk tsarabarta na Mubeena ce, ta siya mata ɗan kunne na zinari ya kai kala uku, banda kayan sawa wanda har ta soma tafiya duk zata saka su. Danginsu duk suka zo yi musu barka da zuwa suka amsa nasu tsarabar suka tafi. Mamman ya ji shuru-shuru bai ga Bukar ba, sai hankalinsa ya tashi duk da yana da labarin zuwansa wurin Zanna lokacin basa nan, hakan yasa ya shiga cigiyarsa amma shuru ba labari, ƙarshe dole ya hukura ya cigaba da hidimominsa. Bayan dawowarsu Makka da wata uku ne, wata rana ƴan sanda suka zo gidan da safe suka yi sallama da Mamman, ko da ya fito suka gaisa, ɗaya daga cikin ƴan sandan ya shaida masa labarin cewar "An kama Bukar cikin ƴan fashi sun je gidan wani Alhaji sun kwashe masa kuɗi, sauƙin lamarin basu yi kisa ba, har an yanke musu hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara biyar, to ana ɗan bibiyar lamarin nasu a kotu, shi ne ya bada labarinka ya ce mu zo mu gaya maka" Idon Mamman ya yi ja saboda tashin hankali. "Yanzu ni meye zan yi masa? tunda rayuwar daya zaɓarwa kansa kenan ni babu ruwana, dan haka zaku iya tafiya" "Haba Alhaji ka yi haƙuri mana, hannunka bai ruɓewa ka yar" Cewar ɗaya daga cikin ƴan sanda. "To me zan yi masa?" Cewar Mamman cike da takaici. "Taimakawa za ka yi, domin Allah da Annabi ya ke roƙon mu akan mu zo gunka ka ceci rayuwarsa, dan ya ce ya tuba ba zai sake ba. A yanzu dai an yanke belinsa miliyan uku kafin a fidda shi" "Tafdi jam, wallahi ba zan yi asarar kuɗina ba, ku ce masa zan taya shi da addu'a har Allah ya fito da shi" Daga haka bai kuma magana ba ya koma cikin gida cike da damuwa sosai. Haka ya labartawa su Zanna lamarin, Zanna ya sanya baki akan ya yi haƙuri ya bada kuɗin ya fidda shi, ƙila sanadin shiryuwansa ne ya zo. Mamman yaƙi sauraren maganar Zanna, a cewarsa in yaji wuya zai natsu ya gyara rayuwarsa, amma ba zai yi asarar kuɗinsa ba. ******* Kwanci tashi Mubeena ta shekara guda a duniya, ta yi wayo sosai tafiyarta ta yi kwari, ta yi mugun sabo da Falmata tamkar ita ce ta haifeta, saboda a lokacin Kaltume ta ƙara ɗaukar wani cikin hakan yasa ta yaye Mubeena, sai renonta ya zama yana gun Falmata. Wata rana Mamman ya shirya musu tafiya dan kai ziyara ƙauyensu, Kaltume ce a baya ita da Mubeena sai Mamman a gaba gefen Zanna yana tuƙasu. Haka suka je ƙauyensu suka sada zumunci, sai da suka yi tsawon kwana biyu kana suka kamo harya dawowa. Sun kusa shigowa gari mota ta kwacewa Zanna ya aukawa wata babban mota ta wuntsilasu gefen hanya, kafin zuwan Mutane Zanna ya fito da kyar yana jan jiki, kukan Mubeena ce yake ratsa dodon kunansa, cikin tashin hankali ya yi azama ya buɗe ƙofar baya, da kyar ya ciro ta ya aje ta a ƙasa nesa da motar, ya dawo ya jawo Alh. Mamman wanda jini ya wanke masa fuska yana fidda nishi da kya ya aje shi gefe, ya koma wurin Kaltume ya jawota ita ma ya ajeta gefen Mamman, a hankali Kaltume ta motsa hannunta ta kama na mijinta da ƙarfi, sai ta shiga yin nishi kamar mai naƙuda, jini ya fara fita ta kasanta nan take ya malale ƙasan wurin. Zanna ya matso gunta yana mata sannu, Kaltume tana son yin magana amma ta kasa, sai kawai ta nuna masa Mubeena da hannu, da gudu yaje ya ɗauketa ya kawota kusa da ita, sai ta kama hannun Mubeena. "Amana..." Kawai ta iya furtawa sai muryanta ya sarƙe hawaye masu ɗumi suna bin gefen fuskarta, Zanna ya fashe da kuka ya fara karanto mata kalmar Shahada, Kaltume ta soma amsawa a hankali, a haka motan road safety ta zo gurin suka kwashesu suka sanya a mota, Zanna yana rungume da Mubeena suka shiga motar, ya zauna gefen Mamman da bai san inda kansa yake ba, Kaltume kuwa tana ta jero kalmar Shahada, kafin su ƙarasa asibiti Allah ya yi mata cikawa. Wani irin kuka Zanna yake yi yana ambaton sunan Allah, hankali sa ya yi matuƙar tashi. A haka suka isa Babban asibitin Maiduguri, su duka aka shiga dasu emergency room, dai-dai lokacin ana kiran sallar Azahar. Likitoci sunata ƙoƙarin ceto ransu. Daya ɗaga cikin likitocin ne ya fito yana mai share gumi ya kamo hannun Zanna ya ce "Ka yi haƙuri, Matar tun a hanya ta rasu, shi kuka mai gidan mun samu nasarar dawowar numfashinsa. Allah ya jikanta da Rahma, zaka iya shiga ciki ga gansu" Yana faɗar haka ya wuce, Zanna ya ɗauki Mubeena da tun ɗazu take barci ya sabata a kafaɗa, ya shiga ɗakin a tsorace yana kuka ya hango Kaltume an rufe mata fuska, ga Mamman kwance magashiyyan yana fidda numfashi da kyar, ya isa bakin gadon Kaltume ya shiga jero mata addu'a yana tofa mata, ya ɗauki kimanin minti talatin a gunta. Daga bisani ya isa wurin gadon Mamman, a lokacin ya samu ya buɗe ido har yana ƙirƙiro wa Zanna murmushi, ya buɗe murya a wahalce ya soma magana. "Zanna kaga yadda lamarin Ubangiji ya kasance damu, ka yi haƙuri da nauyin da zai hau kanka. Ni Muhammad na danƙa maka amanar ƴata Mubeena ka zame mata ubu, uwa da dangi, don Allah karka barta ta yi kukan maraici, nasan kai mutum ne mai amana ina so ka ƙara akan na da dana sanka, kar ka yarda riƙon Mubeena ya koma wurin danginmu, kar ka yarda riƙon Mubeena ya koma hannun Bukar ko yasan in da kuke, ka nisanta kanku ga danginmu har sai Mubeena ta mallaki hankalinta, sai ka sanar da ita labarinmu ka kaita wurin ahalinmu. Don Allah ka bar in da muke ka gina sabuwar rayuwa ku kaɗai ba tare da sanin kowa ba, saboda ina son Mubeena ta yi rayuwar farin ciki da soyayyar iyaye, ka saida duk kadarorina ka gida sabuwar ruyuwa, ina so ka kasa dukiyata kashi huɗu ka ɗauki kashi ɗaya na baka halak malak, kashi uku kuma ka juyawa Mubeena har sai ta mallaki hankalinta sai ka danƙa mata dukiyarta. Nagode sosai Allah ya baka ikon riƙe amanarta" Sai ya juya kansa yana kallon Kaltume. "Allah ya jiƙanki Matata ya saka miki da gidan Aljanna Firdausi" Nan take muryarsa ya sarƙe, Zanna ya shiga karanta masa Kalmar shahada har Allah ya karɓi abinsa. A wannan lokacin kuka ya ɗaukewa Zanna, ya fita yaje ya dankawa wata nurse Mubeena ya kira likita ya zo ya duba Mamman, shima ya tabbatar masa daya ciki. Zanna ya fita ya tari abin hawa ya isa babban masallacin unguwarsu ya shaidawa limaminsu abin da ya faru, nan take aka tura mota zuwa asibiti aka ɗauki gawarsu Mamman zuwa gida. Falmata saboda firgici har suma ta yi, koda ta farfaɗo ta amsa Mubeena ta ƙanƙame ta a jikinta tana kuka kamar mahaukaciya, Hafiz duk da bayi da wayo yasan cewar babban abune ya faru a gidan nasu, kuka yake har muryansa yana dishewa. Kafin a ce kabo unguwar ya cika da al'umman annabi har cikin gidan, kafin sallar magrib aka yi musi sutura aka sadasu da gidansu na gaskiya. _Kullu nafsin za ikatul maut, Allah ka jikan duk wa'inda suka rigamu zuwa gidan gaskiya, kasa mu cika da Imani, Ameen._ Zuwa safiya danginsu duk sun hallara, sun ci kuka sosai. Har zuwa ranar bakwai Zanna bai fidda kwalla ba zuciyarsa ta bushe sai yawan ajiyar zuciya da yake yi, shi ne yake ta amsar gaisuwa, anyi addu'an bakwai an watse lafiya, wasu daga cikin danginsu suka zauna har sai anyi addu'an arba'in. A wannan zaman ne wasu daga cikin ƴan uwansu suka nuna maitarsu a fili cewar suna son su riƴe Mubeena da dukiyarta, har hakan ya kawo rikici tsakanin dangin Mamman dana Kaltume, Zanna shi dai na shi ido bai kuma yi masu musun ba zai bamu ba, face ma haƙuri daya basu da lallama akan su jira shi ya tattara dukiyarta gaba ɗaya ya basu, da wannan shawarar suka amince suka zauna lafiya. Bukar ya yi kuka kamar ransa zai fita lokacin daya ji labarin mutuwar ɗan uwansa da matarsa, duk yadda yaso ya fito an hana shi ƙarshe dole ya haƙura. Tun daga wannan lokacin ne ya watsar da duk shiriritarsa ya ƙuduri aniyar zai zama mutumin kirki in ya fito, zai yi aure ya riƙe Mubeena amana da dukiyarta. Abin da danginsu Mamman basu sani ba, Zanna ya tattara duniyar Mubeena duka ya buɗe sabon account ya kaimu banki, ya saida Mamman plazan da gidansa da suke ciki da motar da yake hawa, duk a haɗa kuɗin a asusun banki. Banki suka yiwa Zanna lissafin kuɗin gaba ɗaya, suka raba kashi huɗu, ya ɗauki kashi ɗaya na shi ya bar kashi uku a banki. Yaje can wata sabuwar unguwa kamar za a fita garin, ya siya gida a nan da kuɗinsa ɗaki ciki ɗai-ɗai har uku, sai bayi da kicin sai filin tsakar gida, ya yi komai cikin sirri, ya siya musu kayan ɗaki masu sauƙin kuɗi ya zuba, hatta abinci ya siya ya aje, dawowa kawai ya rage musu. Bayan anyi sadakar arbain, har lokacin danginsu Kaltume da Mamman sunƙi tafiya, suna jiran Zanna ya haɗo kuɗin gadon Mubeena. Cikin ikon Allah kuwa Mubeena bata yarda da kowa a cikinsu sai Falmata, hakan ya bawa Zanna damar ɗaukar yaran cikin dare ya fita dasu Falmata na biye da shi a baya, ko kayan su basu ɗauka ba sai na jikinsu, sai kuma akwatin da ya zuba gwala-gwalan Kaltume da hotunansu da kuma takardun banki da duk abin da ya shafi gadon Mubeena, shi kawai suka ɗauka suka bar gidan cikin dare misalin ƙarfe tara. Sai da suka yi safiya kusan na awa guda suka bar unguwar da kewayenta gaba ɗaya, kana suka tari mai taxi suka hau ya wuce dasu sabuwar unguwa, sai da suka yi tafiya na kusan hawa ɗaya da minti biyar kafin suka isa sabuwar unguwar, mai taxi ya sauke su bakin hanya suka ƙarasa da ƙafa, sai ƙarfe sha ɗaya da mintuna suka kai gidan, ko da suka isa kwanciya suka yi domin sun kwaso gajiya. Can cikin gari kuwa, ko da dangin suka wayi gari basu ga su Falmata ba sai basu nuna damuwarsu ba ganin akwai kayansu a gidan, hankalinsu bai tashi ba sai da aka kwana aka yini, basu ba labarinsu, zuwa yamma wanda ya siya gidan ya basu takardar notice, hankalinsu ya tashi suka bazama niman Zanna. Kwanan su biyu suna gantali daga ƙarshe suka gane cewar ya saida komai ya gudu ne, gaskiya yasha zagi a gunsu sosai wasu harda kukan bakin ciki suka yi suna tsinewa Zanna da Falmata. Haka suka ƙara kwanaki ganin ba sarki sai Allah, daga ƙarshe sai suka rabe kayan gidan harda nasu Falmata, kowa ya ja nasa suka bar gidan suka koma ƙauyensu. Haka lamarin ya ishe Bukar kamar labarin Hikaya, ya shiga tashin hankali sosai yana tunanin ko Zanna ya yi haka ne domin ya danne duniyar Mubeena. Hakan ne yasa ya ɗauki alwashin in ya fito sai ya nimo shi duk inda ya shiga, kuma sai ya raba shi da dukiyar ya dawo hannunsa ya kwace Mubeena. Ta mangaren Zanna sun kafa sabuwar rayuwa mai cike da aminci, Falmata ta riƙe Mubeena tamkar ita ce tahaifeta. Zanna ya buɗe shago a jikin gidansa yana saida kayan provision, hankalinsu ya kwanta Mubeena ta manta da wasu Iyayenta domin a yanzu ba tada Iyayen da suka wuce su Zanna. Haka rayuwa ya yi ta tafiya har tsawon shekaru uku, komai ya lafa an manta da rayuwarsu Mubeena, Zanna hatta garinsu yaƙi zuwa, dan yana ganin kamar ko danginsu Mamman zasu je can. A wannan lokacin Falmata ta ƙara haihuwar Hafsat harta she kara ɗaya a duniya, sun sanya Mubeena a makaranta mai tsada zuna zuwa da Hafiz, Falmata ke ɗawainiyar kaisu da ɗauko su, har zuwa lokacin Zanna bai taɓa dukiyar Mubeena ba. Ana haka ne ya haɗu da wani mutum a unguwarsu yana fita ƙasashen afrika yana saro atamfofi a can, da haka Zanna ya soma binsa suka ƙulla abota mai tsafta, Alhaji Umaru ya koyar da Zanna yadda ake kasuwanci, ganin haka yasa Zanna ya sanar da shi cewar yana da kadarorinsa na gado a ƙauye, yana so ya saida ya buɗe katon guri don bunƙasa kasuwancinsa, Zanna ya ɓoye gaskiyar labarin dan har yanzu bai yarda da wani ba da har zai gaya masa gaskiyar dukiyar na Mubeena ce. Alh. Umaru ya ba shi shawara da ya samu fili ya gida shaguna ya zuba haya, sauran sai ya sanya kayansa a ciki yana bada sari, da wannan sharawan Zanna ya ɗibo kaso biyu a dukiyar Mubeena ya siya fili a bakin hanya ya gina shaguna bakwai, ya riƙe biyu yaba zuba atamfofi da kayan pan senigal yana saidasu akan sari, duk bisa jagorancin Alh. Umaru. *******   ***    ******* *Bayan shekara biyu* Bukar ya kammala zaman gidan yari na shekara biyar cif, ko da ya fito ƙauyensu ya nufa ya samu labarin duk abin da ya faru, kwanan sa biyu ya dawo cikin birni cike sa baƙin ciki, a wannan lokacin ya ɗau aniyar zama mutumin kirki dan cika ƙudurin Mamman, sai kawai ya yake shawarar ya tafi garin Kano. Zuwansa da wata guda Allah ya haɗa shi da wani Alh. Aminu, ya ɗauke shi aiki a kamfaninsa na haɗa yoghurt, cikin ƙanƙanin lokaci Bukar ya samu karɓuwa sosai a gurin, ya tsaya tayin dana ya koya aiki mai kyau ana biyansa duk wata yana tara kuɗinsa. *****       ****** *Bayan shekara biyu* Bukar ya kware sosai ya iya aiki kuma kuɗinsa sun taru da yawa, a nan ya sanar da Alh. Umaru zai koma garinsu ya kafa nashi gurin, Alhajin bai ji daɗi ba amma ba zai tauye shi ba tunda ya koya aikin, burinsa duk yaransa da suka yi aiki ƙarƙashinsa su kafa nasu gurin, hakan yasa ya ɗauki kuɗi masu tsoka ya ba Bukar kyauta, ya yi murna sosai da godiya ya kama kansa bayan ya yi sallama da duk mutanen kamfanin. Bukar kafin ya bar Kano sai da ya siya duk injinan da suke amfani dasu wajen haɗa yoghurt ɗin, da duk kayan aiki ya barsu a nan, kafin ya tattara ya koma Maiduguri ya samu wani ƙaramin gida ya kama hayansa, sai ya koma Kano ya kwaso kayansa da ya siya ya zo ya kafa su a gidan, ya samu yara matasa ya karantar dasu komai ya fara yin yoghurt na shi na kansa, a hankali ya amsu a wurin mutane, da kaɗan-kaɗan ya bunƙasa sosai. ******   ***   ******* *Bayan shekara uku* Zanna ya zama babban Alhaji duk sun sauya kamar ba su taɓa shan wata wahala ba a duniya, a wannan lokacin ne Zanna ya buɗe katafaren kamfani wanda ya sanya masa M&B cosmetics & perfumes Nigeria limited. Ma'anar M&B shi ne Mamman Bakura, hakanan yaji sha'awar sanya sunan Mahaifin Mubeena. Wannan kamfanin ya karɓu sosai domin har daga garuruwa suna zuwa suna sarar kaya, suna yin duk kayan kwalliyar kama daga power kala-kala, jan baki, gazal, mascara, da sauran kayan kwalliya, duk kuma suna ɗauke da tambarin M&B jikin ko wani kaya. Ɓangaren turaruka ma haka, kama daga na jiki, kaya, hatta su humra da turaren tsinke dana wuta duk suna saida nasu na kamfanin, sai kuma wasu turaruka da suke kawosu daga ƙasashen waje, sai dai sunfi kawo irin na ƙasar Makka da ƙasar Sudan. Duk wani turare da kake nima in dai ka zo kamfanin M&B zaka samu. A wannan lokacin Baba Zanna ya sauya musu gida zuwa new GRA, ya siya motar hawa da kuma motar su Mami wanda za a riƙa kai su Mubeena makaranta. *********     ********* *Bayan shekaru da yawa* Ɓangaren Bukar ya gina kamfaninsa na yoghurt mai suna AB yoghurt. Yana bayar da sari ga ƴan kasuwa birni dana ƙauye. Duk wannan buɗi daya samu yana nan yana bincike akan inda Zanna na ɓoye, kuma har zuwa lokacin bai samu bayanin komai a kansu ba. Har malaman tsubbu yasa suka yi masa bincike, sun ba shi tabbacin zasu haɗu amma lokaci bai yi ba. A wannan lokacin Bukar ya yi aure harya haifi yara biyu, Nabeela da Anwar har sun tasa suna primary school. Sai kuma halin da ya ɗauka na niman mata, tun Matar bata sani ba har ya fito fili, haka dai ta cigaba da zama da shi tana haƙuri. ****** Mubeena da Fanna sun kammala secondary har zasu shiga university, kawancensu ya samo asali tun primary da aka sanya Fanna suka shaƙu sosai, duk inda Beena take Fanna tana wurin har zuwa girmansu suna tare, wanda suka yi alwashin yin karatu tare komai ɗaya. Sun samu admission a nan university of Maiduguri, duk iyayensu suka yi musu register suka fara zuwa, kwas ɗinsu ɗaya Mass com. Mubeena ta tashi cikin gata wanda bata taɓa sanin cewa basu Baba bane suka haifeta ba, su kuma su Baba sun cigaba da riƙe maganar har zuwa lokacin da zai aurar da Mubeena kafin zai faɗa mata gaskiyar asalinta.             ***** Su Beena suna 200level, wata rana ruwa ya tare Fanna a makaranta lokacin Yaya Hafiz ya ɗauki Beena sun wuce gida, da ruwan ya ɗauke Fanna ta fito ya fara takawa a hanya kafin ta samu a abin hawa, Alh. Bukar ya biyo ta hanyar Allah ya haɗa shi da Fanna yana ganinta ransa ya biya, sai ya tsaya dan ya latsa yaji ko ƴar hannu ce, suka gaisa ya nima zai rage mata hanya ba musu ta amince dama ta soma gajiya da tafiyar sai ta shiga motar, Alh. Bukar ya shiga janta da hira, cikin dabara ya shigar da bayanin yana sonta, Fanna ba jan aji ta amince a cewarta ta samu saurayin siyan kati, dan ita dama mace ce mai san ƙarya da harkan wayewa, sai dai duk samarin da take dasu ba wasu basu kuɗi bane shiyasa take haƙuri dasu a haka. Tun daga wannan lokacin Alhaji ya shiga kashe mata kuɗi ya siya mata babbar waya, nan da nan Fanna ta yi clean ta faso gari, lokacin da take bawa Mubeena labarin Alh. Bukar da irin hidimar da yake mata, Mubeena faɗa ta yi mata da nasiha akan tabi duniya a hankali, tun daga lokacin Fanna ta daina gaya nata komai, ko zata bata labari sama-sama take faɗa mata. A haka ne Alhaji Bukar ya buɗe wa Fanna ido, shi ne mutum na farko daya fara keta mata haddi, a ranar Fanna tasha kuka, Alh. Bukar ya ce mata ba wani abu bane ya nuna mata tabbacin zai aureta, hakan yasa ta saki jiki suka cigaba da rayuwar shashanci yana kashe mata kuɗi. Wata rana ya zo ɗaukar Fanna a makaranta lokacin ita kuma Beena ba a zo ɗaukarta ba, a nan Fanna ta jata zuwa wurin Alh. Bukar dan su gaisa, yana ganin Mubeena gabansa ya faɗi domin ya hango tsantsar kamarta da ɗan uwansa Mamman sai dai ita tanada haske, bakinsa har yana rawa wurin tambayar Fanna sunanta, ba wani ja ta gaya masa sunanta Mubeena Zanna. Gaban Bukar ya faɗi ras, ya lashe lebensa na ƙasa ya saki wani shu'umin murmushi, abin da ya daɗe yana nima shekara da shekara yau ya yi katari da shi. 'Wato Zanna ka riƙe Mubeena da dukiyarta tamkar kaine ka haifeta ko? baka sanar da ita labarin iyayenta ba, ka sanya tana amfani da sunanka' Duk zancen zuci ya yi, a fili kuma ya kalli Mubeena suka gaisa, a haka ne Hafiz ya zo ɗaukarta Mubeena ta yi musu sallama ta wuce. Fanna ta shiga motar suka wuce, a hanya ne Bukar ya yi ta tambayar Fanna labarin Mubeena cikin dabara, ita kuma ta ba shi labarin duk abin da ta sani nata. Tun daga wannan lokacin ya fara binciken Zanna da duk abin da yake ciki ba tare da ya sani ba, a wannan lokacin baya buƙatar Mubeena ta san labarinta ya fi ƙaunar dukiyarta fiye da ita, shiyasa ya ɗauki alwashin ya kasheta daga baya sai ya tunkari Zanna, ya san zuwa lokacin dole ya danƙa masa dukiyar Mubeena tunda ta riga ta mutu, shi sai ya ci gadon. Da wannan gurɓatacciyar shawarar ya soma haɗa plan yadda zai kashe Mubeena, ya ɓoye komai a ransa, hatta Fanna bai nuna mata ya san Mubeena ba suka cigaba da harkansu. Ɓangaren Alh. Zanna kuwa, hankalinsa kwance yake gudanar da rayuwarsa, ya ɗauki son duniya ya aza akan Mubeena, ƙiri-ƙiri yake nuna banbaci a kan yaransa kuma Mubeena yarinya ce mai biyayya, domin sunyi wa yaran tarbiyya mai kyau, zuwa girmansu ne Mami ta saki komai a cewarta sun mallaki hankalinsu ba zasu lalace ba. Yadda Baba yake nuna mugun so ga Beena shi ne ya hura wutar ƙiyayyar Mubeena a zuciyar Hafsat, har wata ran Mami take shigar mata tana jin zafin bambancin da Baba ke nunawa, sai dai takan yi ƙoƙarin danne zuciyarta gudun kar ranta ya ɓaci a gurinsa, dan duk lokacin data kawo masa ƙorafin haka, kaca-kaca yake mata ya tunatar da ita asalinsu da kum matsayinsu, sannan arzikin Mubeena suke ci. _Wannan shi ne asalin tushen labarin, wanda son da Mubeena take yiwa Mansoor ya yi sanadin tono asirin da ke ɓoye_ _Cigaban Labarin..._ *Rahma ce*
    Mar 1