Sabon shirinmu na 'Rayuwa da Zamantakewa' a yau ya yi hira ne da Hajiya Bilkisu Zailani (Queen Shiba) game da illolin fyade ga yara mata da kuma hanyoyin magance su. Mai gabatarwarmu Hadiza Balarabe ce ta tattauna da ita.
Ku saurari kasidar Hassan Adnan na yabon Annabi (SAW) mai taken 'Sannu Farin Duba'.
A sabon shirinmu na 'Rayuwa da Zamantakewa', mai gabatarwarmu Hadiza Balarabe ta tattauna ne tare da Hajiya Maryam Ibrahim (First Lady), founder na Masshu's Save Life Initiative, game da matsalolin dake tattare da yawon maula da kuma yadda matasa, musamman mata za su dogara da kansu.
A lakca da ya gabatar a ABU Zaria, Dr Jamilu Zarewa yayi bayanin abubuwan da ya kamata mutum mai neman ilimi ya bi a tsari na Musulunci da kuma irin falalar da bin hakan kan kawo.
A wannan shiri na 'Rayuwa da Zamantakewa', mai gabatarwarmu Hadiza Balarabe ta tattauna tare da Hajiya Maryam Alhassan Dan iya, marubuciyar littattafan Hausa, game da dalilan da ke kawo mata su shiga yawon bariki da kuma matsalolin da hakan ke janyowa har da ma yadda za a shawo kan matsalar.