Game da Mu

Bakandamiya taska ce da aka ƙirƙireta don ba wa jama'a kowa da kowa damar musayar basira, sada zumunci da harkokin kasuwanci ta hanyar amfani da na'urorin zamani kuma cikin harshen Hausa.

 

Kowa na iya yin rajista ya buɗe shafi a taskar don mambobi su ƙaru da shi, kana shi ma ya ƙaru da su. Duk mamban da ya yi rajista (har ma da wanda bai yi rajista ba) yana iya amfana ko mu’amala da Bakandamiya ta muhimman ɓangarorinta guda 10 kamar haka:

 

1. Activity feeds

 

Activity feeds shine bangon nan na farko, wato member status page, wanda mutum zai fara gani da zarar ya yi log in. Idan mutum bai yi log in ba ba zai iya ganin activity feeds ba.

 

A activity feeds mutum na iya ganin duk sababbin abubuwa da mambobi suka sanya, kamar su rubutu, bidiyoyi, sautuka, hotuna da makamantansu. Kana mutum zai iya yin comment, ko like ko sake sharing don wasu su kara gani.

 

Idan mutum na so yake ganin abubuwan da wani ke posting koda yaushe to ya yi following wannan mutumin. Idan aka je shafinsa (profile) za a ga alamun 'follow' sai a latsa.

 

2. Rubutu

 

Sashen rubutu na daga cikin muhimman sashe na Bakandamiya. A nan ne mambobi ke buga rubuce-rubuce masu ilmantarwa da suka shafi fannoni daban-daban, kamar su kimiyya da fasaha, kiwon lafiya, zamantakewa, tarihi da al’adu, ƙagaggun labarai da makamantarsu.

 

Kuna iya latsa nan don ziyartar sashen rubutu.

 

3. Bidiyoyi

 

Bakandamiya na da sashen bidiyoyi inda mambobi za su iya sanya bidiyoyi kala-kala, kuma kowa na iya kallo. Shi ma fannin bidiyoyi an kasa shi zuwa kashi daban-daban, kama daga kwalliya da sutura, wa’azi da tambayoyin addini, koyon sana’o’i, da abubuwan al’ajabi, da ma sauran bidiyo kala-kala. In dai mutum ya san Youtube, to tamkar haka ya ke.

 

4. Sautuka

 

Wannan muhimmin ɓangare ne da Bakandamiya ke kawo muku abubuwa daban-daban cikin sauti, kama daga wa’azi da karatun littattafan addini, zuwa karatun littattafan Hausa na da da na yanzu, da waƙoƙi da hira da masana akan abubuwan da suka shafi rayuwa da dai makamantarsu.

 

Yanzu haka sashen sautuka na ɗauke da karatun littafin Magana Jari Ce na ɗaya da na biyu da na uku, kana da karatun littafin Ahlari da Iziyyah, da Risala wanda marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya karantar lokacin rayuwarsa.

 

Ku latsa nan don sauraren abubuwan da sashen ya ƙunsa. Sannan idan kun yi rajista kuna iya sanya sautukanku da abin da kuke so ku sanya don amfanin al’umma.

 

5. Hotuna

 

Wannan ɓangare ne da zai bai wa mambobi dama su ƙirƙiro albam na hotuna daban-daban don tarihi da makamancin haka, misali, akwai sashen hotunan tarihi da al’adu, da shahararrun mutane da dai sauransu. Har ila yau, mutum na iya kirkirar albam na wani kayan kasuwanci da yake sayarwa.

 

Abin da ya bambanta sashen hotunan Bakandamiya da na sauran kafafen yanar gizo shi ne, a Bakandamiya, kowane hoto da sunansa (sunan wanda ko abin da ke hoton) da kuma taƙaitaccen bayani game da hoton. Saboda haka, sashe ne na hotuna da ke ɗauke ta ɗimbin bayanai masu muhimmanci.

 

6. Zauruka

 

Ana amfani da zauruka ne kamar yadda ake amfani da ‘group’ a kafafen sada zumunta. Kowane mamba na iya ƙirƙirar zaure gwargwadon abin da yake so ya yi da shi, kama daga zauren abokai, zuwa na haɗin kai da kai, da na kasuwanci, da na karatu da makamantarsu. A halin yanzu muna da zauruka daban-daban da mambobi da dama suka ƙirƙiro. Ku latsa nan don ganin su.

 

7. Tambayoyi

 

Wannan sashe ne na tambayoyi da amsoshi wanda kowa zai iya amfana da shi. Wanda ya yi rajista yana iya tambaya kuma ya ba da amsar tambayar da wani ya yi. Idan kuma mutum bai yi rajista ba, to yana iya karanta komai amma ba zai iya rubuta tambaya ko amsa ba har sai ya yi rajista.

 

An kasa sashen ‘Tambaya’ kashi-kashi, kama daga tambayoyi a kan abin da ya shafi addini – tsarki, alwala, sallah, azumi, zakka, hajji – zuwa abin da ya shafi, kimiyya da fasaha, noma da kiwo, zamantakewa, girke-girke, koyon Turanci, na’ura mai ƙwaƙwalwa, tarihi da al’adu, da ma sauran tambayoyi daban-daban da za a ƙaru da su.  Ku latsa nan don ziyartar sashen tambayoyi.

 

Idan kuma kuna da tambaya game da yadda za ku yi amfani da taskar Bakandamyar ce, misali kuna fuskantar wata matsala na rajista ko sanya hoto, ko makamantarsu, to kuna iya latsa nan don ziyartar Zauren Bakandamiya ku yi tambaya, ko kuma ku latsa nan don zuwa 'Support Center' namu don samun cikakken bayani game da amfani da taskar.

 

8. Sanarwa

 

Sanarwa sashe ne da kowane mamba zai iya ɗora wata sanarwa ta shi don kaiwa ga mutanen da yake buƙata. Misali, za ku iya ɗora sanarwar taruka, ɗaurin aure, bukukuwan al’adu da na siyasa da dai sauransu. Ku latsa nan don ganin yadda wannan sashe ya ke, kuma ku dora sanarwarku.

 

9. Ra’ayoyi

 

Wannan muhimmin sashe ne da mambobi za su iya amfani da shi don sanin ra’ayoyin mutane dangane da wani abu da suke son sani, misali, suna son sanin ko wace cuta ce ta fi yi wa yara ƙanana illa a wani yanki, ko kuwa wane ɗan takarar siyasa ne zai iya yin rinjaye a zaɓe mai zuwa, da makamantarsu.

 

Mamba na iya ƙirƙirar tambaya tare da zaɓi guda biyu ko uku ko ma fiye da haka don mai zaɓar ra’ayin ya zaɓa. Da zarar an kammala zaɓe, zai ba ka cikakkun alƙaluma na yawan mutane da suka bayyana ra’ayinsu da kuma adadin ra’ayoyin na su.

 

10. Sana'o'i

 

Kamar yadda muka faɗa a taken Bakandamiya a baya cewa, dandali ne na musayar basira, da sada zumunci da kuma kasuwanci. Yana daga cikin babban hadafin Bakandamiya, ya samar da wani tsari na zamani don al’umma da ke birane da ƙauyuka su amfana daga damar da na’urorin zamani suka bayar a yanzu don yin kasuwanci.

 

Kowane mamba na iya ɗora sana'arsa ko hajarsa, da hoton hajar, da lambar waya da adireshin inda mai saye zai samu hajar. Duk hajar da aka ɗora a wannan sashe mutane na iya cin karo da shi idan suka yi browsing Google don sayen wani abu. Ku latsa nan don shiga ku sanya hajojinku. 

 

Idan kuma tallar hajojinku ku ke son bayarwa kai tsaye ta hanyar ɗora banner, to sai ku latsa nan don karanta cikakken bayani game da abin da ya shafi hakan, kama daga inda za a sanya maku banner din, da yawan kwanaki da zai yi, da kuma kuɗin da za ku biya da yadda za ku biya.

 

Baya ga waɗannan muhimman sashe guda 10, har ila yau, kowane mamba na iya aikawa da saƙo, wato text message, ga wani mamba matuƙar akwai abota tsakaninsu. Har wa yau, waɗanda suka ƙirƙiro zauruka na iya aikawa da saƙonni ga mambobin zaurukan na su. Da zarar mamba ya yi rajista ya kuma shiga shafinsa, to zai ga inda ake latsawa a aika da saƙonni.

 

Kada ku manta kuna iya aikawa da duk wata tambaya game da abin da ya shige maku duhu game da amfani da taskar a “Zauren Bakandamiya”, wanda za ku same shi a cikin jerin sauran zauruka.

 

Har ila yau, kuna iya binciko duk abinda ku ke so ta hanyar rubuta sunan abin a 'search bar', wato akwatin bincike, da ke saman shafin farko da zarar kun yi sign in a taskar.

 

A taƙaice waɗannan su ne suka tattara suka gina Bakandamiya, kuma kowane mamba na iya amfani da kusan kowane sashe kyauta. Idan akwai sashen da kuka bukaci amfani da shi sannan bai yiwu ba to ku latsa nan don tuntubar mu.

 

Muna rokon dun mai amfani da taskar Bakandamiya da ya guji yada jita-jita da karerayi ko batanci ga wani ko wata. Mu yi amfani da taskar don karuwar mu da karuwar abokanmu. Duk wanda ya kasance yana yin akasin hakan, tabbas Bakandamiya zata dakatar da shi daga amfani da taskar.

 

Kuna iya ziyartar shafinmu na 'Terms of Service' da kuma na 'Privacy Policy' don sumun cikakkun bayanai game da ƙa'idoji da suka shafi amfani da taskar Bakandamiya.

 

Mun gode.