Tsarin sanya talla na zamani na daga cikin sabon salo da Bakandamiya ta zo da shi wanda ya banbanta ta da sauran taskokin yanar gizo. Don haka, kuna iya tallata hajojinku na kasuwanci ko wani harkoki naku a Bakandamiya wanda zai baku damar kaiwa ga abokan kasuwancinku kai tsaye babu shamaki.
Wadanda za su ga tallarku
Idan ku ka sanya talla a taskar Bakandamiya, duk wanda ya shigo taskar yana iya ganin tallar a shafuka daban-daban. Sannan kuna iya sanya tallarku ta kai ga wasu mutane na musamman, misali kwastomominku da ke zaune a wata jiha ko karamar kukuma, ko gari, maza ko mata, da makamantan haka.
Farashin sanya talla
Ga farashin sanya talla a Bakandamiya kamar haka:
Bayan kun zabi irin tsawon lokaci da ku ke so, sai ku biya kudi a account namu kamar haka:
Bayan kun biya kudin sai ku aiko mana da shaidan biya (payment receipt) ta email ko WhatsApp namu dake kasa:
Email: admin@bakandamiya.com
WhatsApp: +234 (0) 907 230 4548
Har ila yau, za ku aiko da banner wanda za a sanya muku a tallarku, misali hoton irin kayan da kuke sayarwa ko kuma wasu bayanai da ku ke so a nunawa kwastomominku.
Wadanda ke zaune a kasashen wajen Nageria ko kuma suke so su biya da US Dollars sai su tuntube mu.
Muna kara tabbatar muku da cewa ta hanyar amfani da tsarin tallar taskarmu za ku iya aikawa da sakonninku da hajojinku zuwa ga wadanda ku ke so kai tsaye da kuma dubban mutane a ko’ina a duniya.
Sai fa an gwada a kan san na kwarai.
Mun gode.