TALLACE-TALLACE

Tsarin sanya tallace-tallace na zamani na daga cikin sabon salo da Bakandamiya ta zo da shi wanda ya banbanta ta da sauran taskokin yanar gizo. Don haka, kuna iya tallata hajojinku na kasuwanci ko wani harkoki naku a Bakandamiya wanda zai baku damar kaiwa ga abokan kasuwancinku kai tsaye babu shamaki.

 

Wadanda za su ga tallarku

 

Idan ku ka sanya talla a taskar Bakandamiya, duk wanda ya shigo taskar yana iya ganin tallar a shafuka daban-daban, wadanda za ku ga hotunansu a nan gaba.

 

Na biyu, kuna iya sanya tallarku ta kai ga wasu mutane na musamman, misali kwastomominku da ke zaune a wata jiha ko karamar kukuma, maza ko mata, da makamantan haka.

 

Farashin sanya talla

 

Farashin sanya talla a Bakandamiya ya kasu kashi uku.

 

 1. Bisa yawan kallon tallanku da aka yi (based on views). Kowane kallo: N1.00
 2. Bisa yawan latsa tallarku da aka yi (based on clicks). Kowane latsawa: N3.00
 3. Bisa tsawon kwanaki kamar haka:
  • Tsawon sati daya: N5,000.00
  • Tsawon sati biyu: N8,000.00
  • Tsawon wata daya: N15,000.00
  • Tsawon wata uku: N40,000.00
  • Idan kuna bukatar lokaci fiye da haka sai ku tuntube mu

 

Bayan kun zabi irin tsawon lokaci da ku ke so, sai ku biya kudi a account namu kamar haka:

 

 • Bank: Guaranty Trust Bank Plc
 • Account Name: Bakandamiya Global Concept Ltd
 • Account No.: 0227180030 (NAIRA)

 

Bayan kun biya kudin sai ku aiko mana da shaidan biya (payment receipt) ta email ko WhatsApp namu dake kasa:

 

Email: admin@bakandamiya.com

WhatsApp: +234 (0) 907 230 4548

 

Har ila yau, za ku aiko da banner wanda za a sanya muku a tallarku, misali hoton irin kayan da kuke sayarwa ko kuma wasu bayanai da k uke so a nunawa kwastomominku.

 

Wadanda ke zaune a kasashen wajen Nageria ko kuma suke so su biya da US Dollars sai su tuntube mu.

 

Kuna iya kallon misalan hotuna yadda tallarku za su fito a taskar.

 

Misalin talla a mobile appa

 

Misalin talla a mobile web view

 

Targeted ads on a computer activity feeds view

Misalin talla a computer activity feeds

 

Muna kara tabbatar muku da cewa ta hanyar amfani da tsarin tallace-tallacen taskarmu, za ku iya aikawa da sakonninku da hajojinku zuwa ga wadanda ku ke so kai tsaye da kuma dubban mutane a ko’ina a duniya.

 

Sai fa an gwada a kan san na kwarai.

 

Mun gode.